~~~~
BAYAN WATA BIYU.
"Nadiya..."
Muryar Abdallah ta kira ta cikin wayar dake kare a kunnen Nadiyan, a lokacin tana zaune ne akan bedside drawer ɗakin Safina bayan ta baro ɗakin mahaifiyarta, Fulani.
"...Yaushe zan zo in ɗauke ku?" Ya tambaya.
Wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskarta ba shiri.
"Au ka fasa turo securityn su tafi damu? Ko ka manta ne kira na ƙarshe da kayi abinda kace kenan?"
"Lokacin raina a hasale yake, for god's sake ta yaya zaki tsallake kasar nan har ki tafi U.S ban sani ba? Munzo kusan mu bakwai da freinds ɗina yi muku gaisuwa amma akace min wai ba kya nan, and I tried your line God knows how many times ban same ki ba, so yaya kike so reaction ɗina ya zama a lokacin dana same ki?"
Nadiya ta cije leɓɓenta, gaya mata yake yi yazo gaisuwar mahaifinta da iya abokansa su bakwai kawai, babu ƴanuwansa ko ɗaya balle kuma uwa-uba iyayensa, kuma har dan bai same ta ba zai iya buɗe baki yayi ƙorafi bayan sai da akayi arba'in ɗin mutuwar sannan suka bar ƙasar, kuma bayan ɗan guntun text ɗin sa da ta gani a cikin wayarta bai ƙara waiwayar tata sai bayan arba'in ɗin, a idonta ta hango ƴanuwan mijin Aisha yadda suka dinga sauka mota-mota har sai da aka share makoki, shi kansa mijin nata kwanansa biyu a garin.
Ta sani cewa yin ƙorafinta a wannan lokacin bashi da wani amfani, don ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba yayi abubuwa makamancin waɗannan ɗin kuma maganarta bata canja komai ba, balle a yanzu da take jin zuciyarta na tsoron sake jangwalo wani abun da zai sa abubuwa suka ƙara ɓaci a tsakaninsu.
A yanzu ta fara gajiya da wannan zaman da take yi, wata biyu an share makoki kowa ya tafi ya barta, Aisha ta koma gidanta tuni sannan Safina kuma ta koma makaranta, an gama dukkan wata hatsaniyar sarauta kuma duk yadda aka kai ruwa rana, duk wata fafutuka da Saifudeen ƙannen Mai martaba suka yi, sarauta ta kuɓuce daga gidansu.
Saifudeen bai samu sarautar ba, cin hanci da siyasa sunyi kaka-gida sunyi baƙe-bake ta kowanne ɓangaren masu zaɓen Sarkin, anyi amfani da karfin naira da kuma na siyasa an danƙa sarautar garin Kiyari ga zuri'ar gidan Auwalu Rumfa, babban jikan gidan mai suna Yakubu shi ya maye wajen zaman mai martaba, wani mutum mai ƙarancin addini da kuma son zuciya, don haka alhini ya ƙaru a zuciyoyin mutane ta yadda har bayan an share makokin arba'in jama'a basu bar jimami ba.
Kuma bayan an share makokin ne Saifudeen ya haɗa ta da wani cousin ɗinsu da yake waba wajenta mai suna Ashraf suka je har U.S kai Fulani asibiti, kuma har sun dawo anyi mata aikin gashi ta fara jin sauki ma don tun kafin su taho tana fahimtar dukkan wani abu da ake gaya mata har ma ta kanyi tambaya kan wasu abubuwa da suka faru a baya duk da maganarta bata fita sosai.
Satinsu uku acan yanzu kuma satinsu ɗaya da dawowa, amma har ta fara gajiya don duk da akwai mahidimta a ɓangaren ammad ba abinda take yi tunda suka dawo ɗin sai kula da Fulanin, don har yanzu ko hannunta bata iya ɗagawa, matsalar da aka magance a U.S ta ƙwaƙwalwarta ce kadai amma shanyewar jikinta na nan ba abinda ya canja duk kuwa da gashin ƙashin da ake mata safe da yamma.
Don haka a hankalinta san cewa wannan zaman ba shine mafi alkhairi a wajenta ba, sannan kuma ta lissafa taga cewa in har ta dage kan rabuwa da Abdallah a yanzu to ba ƙaramin kuskure zata yi ba don da kyar ne idan zata sake samun wani kamarsa saboda dame zata yi taƙama a yanzu? Uban da ya mutu? Sarautar da ba tasu ba? Ko Uwar da baza ta taba iya tsaya mata a komai na harkar rayuwa ba? Dama bayan muƙamin mahaifinsu, da Fulani suke takama wajen cewa itace ƙafarsu a ga duk wasu duk manya-manyan mutane na ƙasar nan, amma a yanzu da ita da babu banbanci kadan ne fon haka dame zata bugi ƙirji tace zata samu miji wanda yafi Abdallah? Yaro, kuma mai kuɗi da tashe irinsa? idan tayi sa'a wataƙila sai dai irin manyan alhazawan nan da suka tara ɗan kuɗinsu ta shiga a ta uku koma ta huɗu.
VOUS LISEZ
Zanen Dutse Complete✓
Fiction générale#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...