DAYA.

10.1K 677 22
                                    

~~~

Ka bud'e zuciyarka ga wanda ba zai tab'a sawa kaji cewa 'rayuwa tana da wahala' ba.

🎶'Zani naje gidan ibada...

Ni da masoyi zamu zauna...

Ga wasu zasu kaini d'akin aurena!'🎶

Duk da girma irin na gidan sarautar KIYARI, babu lungu da sak'on da zaka kurd'a sautin wak'ar da ake gudanarwa daga can wajen kamun bikin bai shiga kunnenka ba, sannan ga mutane nan birjik! Tun daga bayi na cikin masarautar har zuwa tarin jama'ar gari da suke d'id'ikowa don gane wa idonsu shahararren bikin da aka fara gudanarwa a yau.

Biki na gimbiya kuma 'ya mace ta biyu a gurin mai martaba 'Ahmad Uba Kamsusi', Haka nan kuma biki na farko da aka fara gudanarwa a gidan sarautar tun bayan zamanin da mai martaba ya gaji mahaifinsa.

Duk inda zaka duba ko ka kalla ado ne na k'awa anyi shi birjik cikin nau'i kala-kala don burge al'umma da kuma dangin ango wanda suma suka kasance jinin sarauta daga garin Sakkwato. Ba wai barin mutane ake su k'arasa can inda ake gudanar da
Kamun ba, amma duk da haka saboda wadata abubuwa kai ba zaka ce ba ko'ina ake bikin ba, don kalolin abinci yawo kawai suke tsakanin mutane kowa na zab'ar ra'ayinsa yaci ya cika cikinsa harda guzurin na gida ma, sannan kuma kid'an daya karad'e ilahirin masarautar ma ya k'ara zirga-zirga da kuma hada-hadar mutane.

A cikin wannan hayaniyar Maijidda na can tsaye ita da Suraj daga bayan hanyar da zata kai ka shamaki inda babu wulgawar mutane sosai. Hannunta rik'e yake da wani kwando mai cike da wasu k'anana abubuwa masu kyalli sai juya shi take cikin yatsunta.

"Dan Allah ki gaya min mana, me Baddon tace da kika gaya mata?"

Muryarsa ta tambayeta a hankali amma cike da zumud'i. Ta d'an cije lebb'enta kad'an tana kallonsa sannan tace.

"Me kake tunanin zata ce?"

"Wallahi ban sani ba tunda kinga ai ba saninta nayi ai sosai ba, kawai ki yanke dogon zancen ki fad'a min ko zuciyata ta nutsu..."

Girarta biyu ta had'e alamun rashin fahimtarsa.

"To meye duk ka wani tashi hankalinka ka san dai ai ba zaginka zata yi ba ko?"

Maganar tasa shi dariyar da bai shirya ba a lokaci guda.

"Zagi kuma Jidda? Wa yake zancensa anan? Kawai fatana Allah yasa ta amince dani ne."

Jin haka yasa ta juya ga barin kallonsa sannan ta d'anyi murmushi kad'an tace.

"Ai kaima ka san da tace wani abu da ba zan tsaya anan ina sake maka magana ba."

"Allah da gaske kike? Bata ce miki komai akaina ba?"

Wannan rashin fahimtar ya sake dawowa kan fuskarta, ta juyo ta kalle shi.

"Me kake tunani zata ce? ni fa kawai tace min ne ta san Babanka ya tab'a aiki a b'angaren Fulani kafin ya koma wajen mai martaba, bayan haka bata ce komai ba."

"Haka ne..." Ya fad'a yana gyada kai.

"... zata sanshi, Baddo ai ta dad'e a masarautar nan, ina jin tun farkon zamanin Sarki Uba take ko?"

Ta d'aga kanta a hankali.

"Na san dai tun mai martaba na yanzu bai yi aure ba suka zo ita da mamanta."

Ya sake gyad'a kansa sannan yayi shiru kuma, zuciyar Jidda ta d'an matse kad'an, ta zata a lokacin ko zaiyi mata zancen turo iyayensa ko kuma wata maganar auren da zata kaisu ga mataki na gaba kamar yadda ta dad'e tana sak'awa a zuciyarta amma kuma baice komai ba.

Zanen Dutse Complete✓Donde viven las historias. Descúbrelo ahora