ASHIRIN.

4.5K 652 206
                                    

~~~~

A gefen babban titi, expressway wanda ke ɓullewa zuwa mabanbantan garuruwa, wata ƴar ƙaramar rumfa ce irin ta kara da reshunan itace a ƙasan inuwar wata bishiya, irin dai rumfunan da motoci ke waucewa cikin matsanancin gudun da zaka yi mamakin a yaushe suke ciniki, a cikin rumfar tebur ne mai ɗauke da manya da ƙananun kwanduna masu ɗauke da albasa da dankalin turawa, an kasa su manya-manya gwanin ban sha'awa.

Isah mai rumfar ya kalli abokinsa dake zaune yana cinikin dafaffiyar masara akan wata budurwa data tsallako daga cikin ƙauyen nasu ta kawo musu.

"Ke wai ba ƴar gidansu Habu mai kayan miya bace?"

Abokin nasa, Jamilu ya tambaya.

"A gidan nake mana amma ai kowa da shashinsa."

Yarinyar ta amsa tana ɗan haɗe rai, alamun ba za'ayi mata wayo ba.

"To ko ba komai ai ɗanuwanki ne, ni kuma abokina ne, don haka ai kya siyar mun hudu hamsin ɗin nan." Cewar Jamilun yana washe baki.

Yarinyar ta sake hade rai.

"To ai wadda ta ɗoran tallan bata ce in siyar haka ba, in zaka ban saba'in na siyar, in ba haka ba ka zube min kayana in koma."

"Saba'in?..." Cewar Jamilun.

Isah ya juyo daga wanke dankalin da yake a cikin wata ƙatuwar roba yace.

"Haba wai ya kake haka ne? In baza ka bata saba'in ɗin ba ka ajiye daya mana ka karbi uku hamsin, amma ka zaunar da yarinya tun ɗazu sai maimaita abu ɗaya kuke? Ko girman masarar ka kalla ai taci saba'in."

"Ni fa kaga shi yasa bana son ciniki a rumfarka, don kana siyarwa da masu kuɗi kayanka gani kake kowa ma kuɗin ne dashi?..."

Sai ya sake juyawa wajen yarinyar.

"... Ke kin siyar sittin? In ba haka alqur'an na fasa, don ni uku ba zata ishe ni ba."

Yarinyar ta haɗe rai alamun ba haka taso ba, baƙar jagirar data lafta a fuskarta ta kanannaɗe cikin tattarewar goshin nata kafin tace.

"Kawo."

"Yawwa ko ke fa, yanzu ake ciniki, wallahi in muka saba ma har gida zan dinga biyo ki ina siya." Cewar Jamilun yana dariyar shakiyanci, Isah ya sake juyowa ya kalle shi, har zai yi magana sai lokacin yayi daidai da tsayuwar wata farar mota a ɗan gaba dasu kadan, don haka ya saki wankinsa ya ɗauki kwanon albasa ɗaya na dankali ɗaya ya ruga da gudu zuwa wajen motar.

"Alhaji barka da zuwa."

Ya faɗa daidai lokacin da gilashin motar ke zugewa, wani magidanci ne da matarsa da kuma yara biyu maza a gidan baya, sai dai mijin amsa waya yake bai ko kalle shi ba don haka matar ce ta amsa.

"Nawa ne kwanon dankalin?"

"Duba daya da naira ɗari ne Hajiya."

"Na albasar kuma fa?"

"Dari takwas."

Sai ta juya ta kalli mijin nata, bai ji me ta faɗa ba don a hankali tayi maganar, cikin wata siga da in ba wanda aka saba yiwa ba, ba zaka ji komai ba, mijin ya juyo ya kalli kwandunan dake hannun Isah na wasu ƴan sakanni sannan ya gyaɗa kansa kafin ya juya ya cigaba da wayar.

"A zuba min kowanne kwando biyar."

"An gama Hajiya!" Cewar Isah da azamarsa zai koma wajen rumfar, sai dai yana yin taku na farko, kafin ƙafarsa ta sauka akan kwaltar da taku na biyu wani irin abu tamkar almara ya faru, daga cikin dajin dake gefensu can bayan rumfar Isan, wata irin ƙara kamar ta fashewar wani abu mai girma ta cika iska, tayi amsa amo wanda ya taho kuma tare da girgizawar da tayi karaikin ruguginta.

Zanen Dutse Complete✓Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon