29

3.3K 303 0
                                    

2⃣9⃣

Gaba d'aya su john sungama tada hankalinsu wajen Neman su Aysha, harda ya Naufal amasu Neman, duk inda ake tunanin zasuje anje, amma babu koda labarinsu, hargisansu Ariana k'awar su Aysha, itama saida taji babu dad'i, dantana k'aunar Aysha sosai, amma tabbas tasan wata rana zasu had'u.
       Ranarda aka sanarmai jirgi zaije Nigeria tunda wuri yaje yatare a filin jirgin, duk wani shigi da ficin fasinjoji a idonsa akayi, har aka gama komai jirgin yatashi baiga komai kama dasu Aysha ba.
   Wannanma yak'ara tada hankalinsu sosai.

+++++++
      Su Aysha kam suna Canada hankalinsu kwance, komai suka buk'ata suna samunshi, babu tsangwama bare k'yara, basu 6oye komaiba kuma alabarinsu, sun fad'ama Dady komai, yakumayi alk'awarin taimaka musu.
    Sannan yace, "zai madasu makaranta, Dan iliminsu shine zaizama makamin daxasu kar6o 'yancinsu harma da sauran yaran dasuke cikin irin halin da aka sakasu.
    Su Aysha sunyi matuk'ar farinci da hakan, sun d'auki Dady tamkar mahaifinsu, kuma suna k'ok'arin gyara tafiyar addinin yaran gidan, dansuga sunada k'arancin kulawa anan 6angaren.
      Sosai Dady yaji dad'i, Dan dama Naufal ne mai k'ok'arin hakan, tokuma aiiki yamasa yawa ayanzu.

_____________________________
      Bikinsu Sultan da Mujahedeen nata gaba towa, yayinda cikin mama keta k'ara girma, amma tanata k'umshe kayanta bataso asani.
   Batasan tuni Ammah tafargaba, Dan haka taketa bata kulawa, sosai lamarin yarink'a bama mama kunya, danta lurama kamar kowa yasan tanada cikin agidan.
      Dan sosai hajia babba ke nuna mata k'arin k'iyayya da tsana.
    Ko kad'an bata kulata, ita kanta hajia babba tsoron mama takeyi sosai tundacan barema yanzun, duk dai sanda suka had'u sai hajia babba tayima mama habaici, wai abin kunya tsofai-tsofai mama tayi ciki.
       Tun abin nadamun mama harya koma bata dariyama.

Koda aka shiga hifimar bikinsu ya Sultan mama itace akan komai, babu laifima umme Amarya nad'an saka baki awasu al'amuran.
     Komai anyishi Na girma da arzik'i, ansha bidiri sosai da bired'e.
    Tundaga randa aka d'aura auren ya khaleel yabar gidan, Dan bayason adameshi da surutun k'annensa sun rigasa aure, duk da dama shican bai bama dangi fuskar wasa dashiba.
     To bikidai yatashi lfy, ankawo amare anan cikin gidan, dagacan baya baffah yasayi k'aton fili da dad'ewa ya ajiye domin 'ya'yansa, duk Wanda yatashi aure saidai yad'iba nasa yagina, Dan anraba musu tuni, akwai katanga tsakaninsu dasu ainahin cikin gidan, sai akayi k'ofar dazata sadaka danan cikin gidan baffah, yayinda gate d'in gidan yake a can baya, saiya kasance layinsu daban-daban.
    
Bayan biki babu dad'ewa baffah yad'auke mama suka lula k'asar Turkia.
    Bazasu dawoba saita haihu.

+++++++++++++
           A UK kam su john harsun fara sanyi daneman su Aysha, wannan yasaka ya Naufal tattara inasa-inasa yamusu sallama yadawo Canada.
     Alokacin su Aysha harsun fara University hankalinsu kwance, kasancewar Dady lecturer ne a makarantar.
    Sosai su Aysha suka dage, Dan Canada suna amfani da yare biyu ne, English & French.
      Sosai sukayi murna da dawowar ya Naufal kusafasu, yakwashe komai yabasu labari bayan barinsu islands UK, sunsha dariya sosai, wani gurin kuma su John sukansha tsinuwa.

____________________________

      Rayuwa tashud'a sosai, abubuwa nata gudun fanfalak'e, tuni mama ta haihuwa 'yan uku duk maza, bak'aramin farinciki wannan familie suka shigaba, idan kacire hajia babba datakeji kamar ta 6atar da mama da 'yayanta, wad'anda sukaci sunan baffa, da Baban mama da Baban baffan.
     *_Rufa'ee (khalefa), Dawud (Affan), Abdallah (Adeel)_*.
      Yara harsun fara wayo abinsu, kowa sansu yakeyi agidan, kasancewar sune k'anan.
      Amma banda 'yan 6angaren hajia babba.
   Ya khaleel ne kawai babu ruwansa, shidama baya raba d'ayan biyu. Kowa nasane agidan, yana bama su mama girmansu, yana k'yautatama k'annensa da iyayensa, yana nan har yanzu baya d'aukar raini.

####
    Suma dai su Aysha karatu natafiya musu yanda yakamata Alhamllah kam, Aysha ank'ara girma sosai, tazama big girl abinta, yanzu tana shekara ta 16, takusa shiga 17. Amma idan kaganta saika d'aukama takai 18 saboda jindad'i da kwanciyar hankalinsu data samu, takanyi tunanin gida, wani lokacin takansha kukanta saboda kewar su mama da 'yan uwanta, meerah da ifteehal sukan lallasheta danuna mata ladan mai hak'uri, aganinsu aii komai yazo k'arshe, tunda Dady yace dasun kammala karatunsu nanda shekara 1½ dakansa zai maidasu Nigeria, wannan yasama Aysha tak'ara maida hankalinta sosai ga karatun.
      Bata kula kowa, Dan it's ko aboki namiji batashi a school, inhar baka ganta tareda ifteehal ba to zaka ganta tana karatu ko latsa waya, Maheer ne kawai Aysha take sakewa dashi bayan Naufal data d'auka amatsayin babban wa.
      Son ya khaleel kam yana nan mak'ale a zuciyarta, kullum k'ara girma yakeyi dasakin rassa, amma ta danne kayanta bats amince kowa yasaniba.

Meerah da ya Naufal kam soyayya mai k'arfi tashiga, 100% iyayensa sun amince masa ya auri meerah.
     Acewar Dady aii zaiyi jihadi ne, kuma meerah ba it's tasaka kanta a wannan halinba.
      Kiwa yayi farinciki da wannan had'i, karfa Sholy da ifteee da maheer suji labari, sosai suke arinciki.

*_bayan shekara 1_*

          Aysha sanye cikin bak'in dogon wando, ta d'ora jar riga wadda takai mata har guywa, hakama rigar sanyinta ja mai k'yalli, tayane siririn bak'in gyale akanta, sosai tayi k'yau, danta k'ara girma da cikar hallita, komai nata Na babbar mace yagama bayyana.
    Ya Naufal daya fito daga d'akinsa yace oya lil sholy ina iftee kuzo Na saukeku inada wajen zuwa.
      Kai ya Naufal, nikam tunda bikinku yamatso kaida Anty meerah duk kunwani rud'ar da kanku, idan sauri kakeyi kabamu key d'in kawai mutafi.
    No kumuje Na ajiyeku kawai, idan kuma zaku jira maheer ne to nawuce abina, dadyma yau bazaije aikiba.
       Tab broth munada exams fa yau, inamu inajiran sarkin barcin can. Iftee dake fitowa saga d'aki tafad'a.
      Gaba ya Naufal yayi abinsa, tofa zanwuce abina.
     Da Saudi sukabi bayansa.

Tunda suka shigo makarantar yau gaban Aysha keta fad'uwa, ga girarta ta dama sai harbawa takeyi, addu'oi taitayi azuciyarta.
      Kasanceaar itada ifteehal kiwa da abinda yake karanta yasa basa tare ayanzu.
        Gama exams d'insu kenan Aysha tafito amatuk'ar gajiye, tafiya take kamar zata fad'i, ga yunwa, class d'in su ifteehal tanufa Dan bata iya cin abinci saida ita, tunda tazo school d'in batada k'awa sai ifteehal, sauran duk k'awayen hello hii ne, garama wata 'Yar Nigeria mai suna Khursum, itama bawani sakin jiki ayshan tayi da itaba, saboda tsaro, Dan haka kawai halayen Khursum d'in basa birge Aysha, kullum kuma Anty meerah tana nuna mata tayi taka tsantsan da mutane, saboda tasan su John bawai sun daina Neman su baneba.
      Kan Aysha ak'asa tana danna waya domin kiran ifteehal saitaji kawai tayi karo da Abu.
    Da sauri tad'ago tana kallonsa, fad'uwar gaba, tsinkewar zuciya, daskarewar jini duk suka riski Aysha alokaci d'aya.
       Cikin mamaki take kallonsa, ko'a mafarki bata ta6a tunanin ganin mai kama dashibama awannan lokacin........... ✍🏿

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now