3⃣8⃣
Biris yayi da wayar yacigaba da kallonsa, harta yanke aka kuma kira Na 2, kiran daya kuma shigowane yahasala zuciyarsa, wani uban tsaki yasaki, tareda kwala kiran mufeedah!!.
Dama tana la6e, jin kiran daya kwala mata yasaka 'yan hanjinta wuntsilawa, afili tace shikenan namutu yau, wlhy ya khaleel kasheni zaiyi kawai.
Wai dan ubanki bakiranki nakeyibane.
Jikinta narawa tafito, sai mutstsuka ido takeyi alamar abarci tataso, yawatsa mata wata harara da mayun idanun nan nasa, jitayi tamkar tasaki fitsari awajen.
'Dauka wayarki kibarnan kafin namiki dukan mutuwa.
Aibama tabari yak'arsa fad'a tafisgi wayar dasauri ta runtuma da gudu tana mai godema ALLAH daya tserar da ita.
Tana shiga d'aki aka sake kira, d'agawa tayi dasauri, har taune le6enta nak'asa takeyi wajen saurin yin magana, haba babie tunda kaga kayi kiran farko ban d'agaba aikasan akwai matsala, yanzu dakaja ya khaleel yad'auki wayar yaduba wlhy da daga ni har kai mungama yawo.
Wai kina nufin wayar tana hannunsa?.
A'a tana kusadashine.........tabashi labari..
Ajiyar zuciya yasauke, kai my mufeey ALLAH ya taimakemu, wlhy karkiji wasa tsoron yayan nan naki nakeji, bashida mutunci idan kafad'a tarkonsa, ga wani abokina nan agidan yari zai k'are rayuwarsa ta dalilin yayanki.
Kai kajimin, ainasan laifi yayi yakamashi, Dan ya khaleel akan aikinsane kawai hakan kefaruwa tsakaninsa da mutane, saikuma mu k'annensa dayakeyi Dan kulada tarbiyyarmu.
Hakane, yanzu yaza'ayi kenan?.
Tab ai wlhy yau saidai mud'auki Na Annabawa, Dan yana falonmu zaunema yana kallo, nibanma San yadawo k'asarba.
To shikenan saida safe.
Baijira cewartaba ya yanke wayar yana mitar saidai ke, amma wlhy nikam sainaje Na more, ga 'yan mata nan buhu-buhu a birnin Abuja.Bai bar falonba saida film d'in yak'are, sanda yafitama mufeedah tagaji da la6e-la6enta tayi barci.
*_Washe gari_*
Har 8:30am Aysha bata tashiba, tuni su Affan sunbar d'akin, ita kad'ai taketa juye-juyenta a gado.
Kowa ya hallara a dining har baffah kasancewar weekend ne, Ammah ce kawai babu tana Jigawa abinta.
Anty Mamie takalli dukkan yaran babu Aysha da ya khaleel, har mufeedah dasu hasnah suna nan, Dan dolene suzo tunda harda baffah, gakuma zakin gidan yana nan, Momy dama saita gadama take cin abinci dasu, babu kuma ya Sultan da ya mujahedeen, sunacan 6angarensu da matansu.
Muslim tashi kakira babana, kekuma maleeka kira Aysha.
Da to suka amsa.
Babu dad'ewa saiga ya khaleel sunfito shida musleem, har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nasa, k'annensa suka gaisheshi.
Yaja kujerar ya zauna, saida mama takuma aika tasleem sannan su Aysha suka fito, da alama saida maleeka tasha dagama wajen tashin Aysha, dan kayan barcinema ajikinta sai hijjab data d'ora iya kugu a saman kayan barcin, daka kalli idonta kasan yanzu tatashi a barci, saboda akwai ja acikinsu, gasukama sun k'ara zama manya, durk'usawa tayi tagaida baffah, ya amsa cikin fara'a, harda dafa kanta yana mata lale marhabun dadawowarta kasarta, (dan mama tayi masa bayanin komai dangane da dawowar Aysha kasar dakuma zuwansu itada fadeelah, shikam yace Aysha tazo kenan, dan bazata koma kanoba, tunda yaso adawo da Ummulkhairi nan amma kawu bilyamin yabashi hak'uri saboda tana hannun uncle Ahmad ne, to yanzu kam shima tashi d'iyar tadawo gareshi acewarsa, mama dai dariya kawai tayi, amma ak'asan ranta tafiso Aysha tayi aure, dan tasan mijin nata akwai son karatu, harma tambayarta matakin karatun ayshar yayi, tace, "wlhy bata saniba, saidai ya tambayrta".)
Ta gaida Anty Mamie da umme Amarya, sannan tagaida sauran samarin gidan da 'yan mata, babu Wanda yaganeta, amma dai musleem ya kafeta da idanu.
Baffah yace tashi kizauna d'iyata yanuna mata kujera d'aya data rage wadda take kusada ya khaleel.
Jitayi tamkar tafasa ihu, amma babu damar hakan, dan baffah kallon mahaifi take masa ba mijin uwa ba.
Haka ta zauna duk atakure, bayan mama tagama had'ama baffah abincinsa ta zubama Anty Mamie da umme Amarya, tazubama kanta, Aysha dake kusada ya khaleel tace tatashi ta had'a masa shima, bak'aramar kid'ima zancen Maman yasakataba, dukda wani sashe Na zuciyarta yana farinciki.
Babu yanda zatayi tahad'a masa komai, yanata danna waya abinsa tamkar baisan mi'akeyi a dining d'inba, tana gamawa tazagaya tazubama ya Zunnurain da ya Ramadan, ta iso kan Musleem daketa kallonta tun d'azun, magana yay mata k'asa-k'asa batareda kowa yajishiba, _Ammafa kin had'u wlhy_, Aysha tayi murmushi, itama tace kaima haka ya musleem.
Tsayawa yayi cak daga danna wayarsa, yad'ago fararen idanunsa yakafe Aysha da musleem da idanu, Muhsen ne yalura da kallon da ya khaleel yakeyi, ya zunguri musleem, kai Malam ka kulafa, babban Yaya yana harararka.
Da sauri musleem yad'ago suka kuwa had'a ido da shi, ya watsa masa uwar harara, kasa dakai musleem yayi damamakin hararar, babu yanda za'ayi yace yaji maganar dayakeyi da yarinyar. Amma irin sannan uwar harara haka.
Ita Aysha ma tuni tayi gaba, harta zubama Hafiz, tana kaiwa kan mufeedah ta ajiye bowl d'in hannunta tadawo wajen zamanta.
Wani tuk'in bak'in ciki yatokare makoshin mufeedah, wai agola tazo tana nuna musu Isa, wadda in auren wuri tayi saita kusa haihuwar kamarta.
Aysha kam ko'a kwalar rigarta, dan ita duk abinda yashafi hajia babba ta tsaneshi, ya khaleel ne kawai yafita zakka acikinsu.
Kowa yagama zuba abincin baffah yay bismillah, kowa yayi aka fara break, Aysha dukata takura, sai juya cokalin takeyi, shikam wandama takeyi da shi ko'a kwalar rigarsa, abincinsa yakeci hankali kwance, duk sanda zata d'ago saisun had'a ido da Musleem da Zunnurain, saita kuma zama atakure, tarasa wannan kallon kurullah dasuke jifanta da shi, hakadai aka kammala cin abincin kowa yafara kama gabansa Aysha bata wani ci abin kirkiba.
Itace ta biyard'in mik'ewa.
Hartaja kujerarta baya tamike tajiyo muryarsa yana fad'in dawo ki zaune.
Kowa saida yad'ago ya kalleshi, Aysha datasan da ita yake tayi kamar bata ganeba tafara tafiya, da d'an k'arfi yace Aee'sha dake nake.
Yanda yakira sunan saida tsigar jikin Aysha yatashi, kowa kuma kallonsu kawai yakeyi, babu Wanda yasaka baki.
Dawowa ayshar tayi ta zauna, yad'ago suka had'a ido, tayi saurin janye nata, filet d'in abincinta da cup d'in shayi yanuna mata, wakika barma wanna🍵🍝?.
Kwal-kwal tayi da idanu, cikin turo baki tace nifa Na k'oshi.
Shiru yayi yacigaba dashan tea d'insa.
Mama ta dakama Aysha harara, wakike turama wannan shegen bakin? Koshi sa'ankine?.
No barni da'ita mama, tabari harna gama shan tea d'inan batayi abinda naceba taga yanda zanyi da'ita.
Anty Mamie tace a'a babana ba'ayi hakaba, Aysha zauna kici kinji, zama da yunwa bashida dad'i, INA kallonki bakici wani abincin kirkiba kam, kobak'yasonsa?.
Da sauri Aysha tace a'a Anty Mamie, to maza kici kinji.
Kai tad'aga, idonta tab da hawaye, bawai ta k'oshi baneba, har yanzu takasa sabawa da d'and'anon abincin 9ja, tafison taci snacks kawai tad'ansha Ice-cream d'inta.
Baffah dai baice komaiba sai murmushi, yatashi yabar wajen, daga haka kowa yafara zare jikinsa kafin ta shafesa shima.
Dagashi sai ita aka bari, tura abincin kawai takeyi badan dad'iba.
Saida taci mai yawa sannan ta saci kallonsa, harta fara hawaye tace ni wlhy nak'oshi, cikina zai fashe.
Banza yay mata, saida takuma maimaitawa sannan ya harareta, daga yau kikuma min rashin kunya, ALLAH saina saita wannan bakin naki, faratun banza, tashimin anan.......
Baikai karsheba tamik'e, d'an tsaki taja Wanda yasakashi d'agowa da sauri ya kalleta, ta murgud'a bakinta ahankali tace ALLAH ya isana kuma.
Da gudu tabar wajen.
Shiba gunkiba shiba butun butumiba haka Yakoma awajen, hanyar databi kawai yabi da kallon, dolensane ya saita wannan matsiwaciyar yarinyar, shi baima ta6a ganin wadda ta rainashi kamar yarinyarnanba, wai yama akayi hakan tafaru?, tunda suka fara had'uwa a Canada yarinyar nan tafara masa rashin kunya, dolene ya gyara mata zama kafin lamarin ya wuce haka, tashi yayi zuwa 6angarensu, zuciyarsa cikeda tunani matakin daya kamata yad'auka akan yarinyar._______________________________
Bayan su Aysha sunyi wanka mama tamusu iso zuwa wajen baffah, yana zaune afalo shida Nuredin, Noor da y'an uku.
Su Aysha sukayi sallama.
Cikin fara'a ya amsa musu, suka zauna ak'asa suna k'ara gaidashi, nanma cikeda kulawa ya amsa, ya kar6i ummuhanee yamata addu'a, to fadeelah da ankoma yakamata kuma ki koma gidan mijinki kinji, wankan yayi haka.
Kan fadeela ak'asa tace to baffah insha ALLAH.
Ya maida kallonsa kan Aysha da itama kan nata na ak'asa tana wasada zoben hannunta, Aysha ya karatun? Anyo nasara dai ko?.
Kanta tad'ago fuskarta d'aukeda murmushi, eh baffah, komai Alhmdllh, nasamu result mai k'yau, yanzu hakama bautar k'asa zanyi.
Yayi k'yau, ALLAH yayi jagora.
Mama datun d'azun bata saka bakiba tace, ''dama kin cire wannan batun aranki, babu wata bautar k'asa dazakije, kawu bilyamin yace aure zai muku, domin k ma ya jinkirta saka ranar su Rufaida, gwarama kinutsu ki fidda mijin aure.
Hawaye suka zubo a kumatun Aysha, baffah ya kalli mama ransa ad'an 6ace, haba fad'ima, miyasa zaku hanata cikar burinta?, Aysha dai d'iya tace nima, kuma ina bata goyon baya, zankira m. Bilyamin d'in muyi magana.
Muryar mama a sanyaye tace kayi hak'uri to.
Baice komaiba yamaida hankalinsa akansu Aysha, nasiha yamusu sosai dakuma nuna musu shima mahaifinsune, Duk sanda suke buk'atar Abu babu wani shamaki su sanar masa, ashirye yake damusu komiye inhar baifi k'arfinsaba.
Godiya su Aysha sukayi masa, dajin k'aunar tsohon mai mutunci dasanin darajar d'an Adam, suma suna kallon sane tamkar mahaifi, zakuma sucigaba da hakan har karshen rayuwarsu, Haka yayta jansu da hira, har suka saki jiki dashi, sund'an dad'e awajensa sannan suka fito.
Mama tace suje su gaida hajiya babba.
Saida gaban Aysha yafad'i.
Tunda suka doshi 6angaren suke jiyo dariyarsu Husnah, da alama rayuwar tamusu dad'i, koda su Aysha sukayi sallama babu Wanda ya amsa musu sallama, saboda dariya taci k'arfinsu, har itama hajia babba dariyar takeyi, kowannensu da dawani kati a hannu saikace hotuna, kuma tabbas abinda sukema dariyar kenan.
Sallamar suka k'arayi dad'an k'arfi, sai sannan Mufeeda dake kujerar kusada k'ofa taji, waygowa tayi zata amsa......amma ganin fadeelah yasakata fasawa, ta gimtse fuska.
Suma su momyn daina dariyar sukayi, kowa yaci magani, Aysha da fadeela suka durk'usa k'asa momy ina kwana? Munsameku lfy?.
Wata yatsina hajia babba tayi, cikin ko inkula tace lau.
Daga nan babu Wanda yasake tankawa, durk'uson ne ya ishi Aysha da kallon banzar da'ake musu, tad'anja tsaki tareda yunk'urin mik'ewa tsaye.
Da sauri suka kalleta suduka, gaban hajia babbane ya fad'i, sai yanzu talura da Aysha, gani take kamar ta ta6a ganinta.
Ganin yanda tadasa mata idanu yasaka Aysha kauda kai tana Neman tsarin ALLAH daga sharrinta, tareda k'arajin tsanarta azuciya.
Hasnah tace k! Ubanwa kikema tsaki?.
Kalon banza Aysha tamata ta ta6e baki, kinga Yaya fadeelah tashi muwuce kinji, Aysha tayi maganar cikeda salon tura haushi.
Da sauri hasnah tamik'e tayo kan Aysha, kam balastin, aikam yau saina sauke miki abinda ke kanki.
Murmushi Aysha tayi, Wanda ya k'ona ran Hasnar, tace ni mai saukemin kayan kaina saiya shirya y'an mata, Dan nafi k'arfin manyankima balle ke, Aysha ruwan daminace, kona wuce saina dawo, kumani k'adan garen bakin tuluce, akarni akar tulu, abarci Na 6ata ruwa.
Sak'o Na Isar ba shawaraba🙅♀.🤣magana cikin magana Aysha tafad'a.
Amma babu Wanda yafuskanci zancen nata, tara6a hasnah dake tsaye tamkar gunki tafice abinta, fadeelah ma ta take mata baya, itama zuciyarta cikeda nazarin maganar k'anwar tata, Dan bata fuskanci inda zancen yadosaba..................✍
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
ActionLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.