47
Tunda suka tafi babu maima wani magana, duk tsoro yacika Aysha, tunani takeyi ina zai kaita.
Yamik'a mata hijjab Fari tas, sai k'amshi yakeyi.
Kar6a tayi tana dubawa, yadin yamata k'yau sosai, batace dashi komaiba tazame gyalenta tasaka, tana k'unk'uni k'asa-kasa akan INA zai kaitane?, batayi zaton yajitaba.
Saidaki zanyi bak'auya kawai, muryar ya khaleel taji batareda tayi zatoba.
ALLAH yabaka hak'uri, tayi maganar a sanyaye, Dan ita wlhy tsoronsa k'aruwa yake aranta, tunda taga yajibgi guys d'innan, dakuma Marin daya mata.
Bai tanka mataba.
Gani tayi sun shiga cikin makarantar A.B.U. zariya, mamaki takeyi mizasuyi anan kuma?.
Guri yasamu agefe yayi parking, d'alibai nata hada-hada, dukda yaud'in ba ranar karatu baceba.
Harya fita Aysha bata motsaba, yalek'o yana hararta, kosaina fiddokine?.
Jiki a sanyaye tabud'e motar tafito, nanfa idon d'alibai Yakoma kansu, y'an mata anga had'ad'd'en gaye duksun rikece, su kallonma ayshar sukeyi amatsayin k'anwarsa, k'ilan yazo nema mata addimetion a school d'inne.
Cikin takunnan nasa Na jarumta yake tafiya, dolene duk mace mai lfy ta k'yasa.😉.lol.
Dukda cikin nutsuwarsa datazama tamkar halittarsa yake tafiya hakan baihana ya zarta Aysha ba, ita tanama had'awa da y'an sassarfa atata tafiyar.
K'ofar wani office sukaje da aka rubuta professor Al-hassan ibn Mahmud, Knocking yayi aka bashi izinin shiga.
Dattijone maicikeda kwarjinin kamalar addini, zasuyi sa'anni da baffah.
Cikeda fara'a yake fad'in lale marhababinka Ibraheem bin Abdallah.
Ya khaleel yak'arasa suka rungume juna kamar yanda larabawa keyi, sanan ya durk'usa har k'asa ya gaidashi, ganin haka itama Aysha tadurk'usa ta gaidashi cikin girmamawa.
Cikeda fara'a ya amsa yana fad'in masha ALLAH sannunku dazuwa d'iyata, bismillah kuzauna kuzauna.
Ya khaleel da Aysha suka zauna a kujerun dake gaban babban tebir nasa, Aysha tayi k'asa da kanta saboda kunya.
Mamaki yayi mugun kama Aysha lokacin dataji ya khaleel yajuya harshe suna larabci shida dattijon, dole tad'ago manyan idanunta masu yalwar gashi ta kallesa, suka had'a ido Dan lokacin yajuyo yana gabatar da ita wajen dattijon amatsayin matarsa dazai aura.
Janye idanunsa yayi yamaida kan sheaik Al-hassan.
Masha ALLAH Ibraheem khaleel, masha ALLAH, cikin harshen larabcin yayma Aysha barka dazuwa akaro nabiyu.
A mugun mamakin ya khaleel d'in shima saiyaji Aysha ta amsa da larabcin, daganan tacigaba da amsa tanbayoyin sheaik Al-hasan da larabcin.
Shagala yayi yana kallon bakinta dake sarrafa larabcin cikin kwarewa danuna tabbas ta ilimantu a 6angaren addini, bak'aramin birgeshi tayiba, Dan baiyi zaton hakaba tunda baffah yasanar masa daga k'asar waje tadawo karatu.
Sheaik Al-hassan ibn Mahmud malamin ya khaleel ne, ahannunsa yay karatun addini a Abuja, aikine yadawo dashi A,b,u zariya.
Sundad'e basu had'uba saboda yanauin aikin ya khaleel d'in, shiyyasa dayazo d'aurin aurennan yaga yadace yazo ya gaidashi, shine daya kirashi yasanar masa yasameshi acikin makaranta.
Yakawo Aysharne Dan malaminsa yaganta tunda baida tabbacin zasu sake had'uwa dukda yanada burin malamin NASA yay Iuctures alokacin aurennasa.
Sheaik Al-hasan yaji dad'in wannan ziyara sosai, yayimasu nasiha akan aure da muhimmancin auren kansa, da girmama juna, yanda zasuyi zamantakewar dazasu amfanar dajunansu batareda samun sa6aniba ko k'osawa da junaba, sund'an dad'e sosai a makarantar Dan har saida baffah yakirasa, yasanarma baffah Inda sukaje.
Baffah yace shikenan mukam zamu wuce saikun taho, ka gaidamin da Malam sosai, kace insha ALLAH nima inan zanzo wajensa zuwa Na musaman.
Zaiji baffah, saimun taho, to kutahodai dawuri, karkuyi dare kajiko, Kasan hanya babu k'yau.
Insha ALLAH yanzu ZAMU taho baffah.
Bayan sun Yanke wayar ya isar da sak'on baffah wajen Malam, yaji dad'i sosai kuma ya amsa.
Littatafan addini masu muhimmanci akan rayuwar aure dawasu fannonin yahad'ama kowannensu, sai godiya suke masa.
Ya khaleel ya ajiye masa alkairi mai tsoka sannan sukafito.
Har k'ofar mota Malam yamusi rakiya, saida yaga fitarsu sanan yakoma office yanamai jin dad'in ziyarar, Dan har ransa yana k'aunar khaleel d'in, yarone mai kwazon gaske alokacin daya koyar dashi, ga gaskiya da suffar kamala Na mutanen kwarai batareda yaron, yaga kuma haryanzu halayyar Na taredashi.
________________
Tunda suka d'auki hanya babu Wanda yace uffan, har sunshiga cikin kaduna.
Shi yanata tuk'insa dajin wa'azin sheaik Jafar Mahmud Adam, itama Aysha wa'azin take saurare, yayinda wani 6angaren zuciyarta yatafi wajen tunanin ya khaleel d'in, komai nasa na burgeta, tako ina ya khaleel cikakken mutumne, saidai abinda ba'a rasaba, Dan d'an adama Tara yake bai cika gomaba, babu yanda za'ayi kace wane yakai 100%, dolene saika samu wani d'an taumashe koyaya ataredashi.
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
AzioneLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.