58
Zazza6i dai yak'i sakin ya khaleel, yana kwance a d'akinsa cikin bargo, Ammah da Anty Mamie duk suna d'akin, kowa jigum-jigum, Aysha ma tana gefe ta zabga tagumi, tunani a zuciyarta barkatai, dama haka mazan keshan wahala idan hakan tafaru? yawanci alabarai saidai kaji ance matace tasha wahala a daren farko, to amma ita nasu sai yazo da ban, dukda tasan tasha wahala, har yanzuma zata iya cewa bata gama dawowa dai-daiba, ammah ya khaleel yafi bata tausayi, danya fita wahaltuwa, jiyamafa haka suka kwana yana rawar sanyi, wannan wane irin ciwone haka?......
Shigowar baffah da doctor ne yakatsema Aysha tunani, yau Dr Faisal ne zai dubashi, Wanda yakasance family doctor nasu.
Anty Mamie tajanye bargon da ya khaleel yarufe har fuskarsa,, yad'ago idon yana kallon Anty Mamie, sunyi jajur dagani kasan bayajin dad'i kam.
"Sannu babana kaji".
Cikin murmushin k'arfin hali yad'agama Anty Mamie kansa, baffah yamatso ya taimaka masa yatashi zaune ya jigina da fuskar gadon, yakai dubansa ga Aysha dakecan zaune ta zabga tagumi, kasancewar itama shitake kallo suka had'a ido, ita tafara janye nata, sannan shima ya d'auke nasa yamaida kan Dr Faisal dake masa tambayoyi.
Ganin kamar yanajin nauyin amsawa Dr Faisal yace, "please Alhaji kozaku d'an bamu wajene?".
Baffah yace, "OK babu damuwa doctor, bismillah kayi aikinka".
Har Aysha tamik'e zata fita Ammah race, "a'a kekam yi zamanki".
Babu yanda zatayi, dole takoma tazauna, sukuma suka fice.
Ya khaleel yayma Dr Faisal bayani kamar yanda yayma Dr Abraham jiya, Yakuma Sanar masa Dr Abraham yabashi magani harda allura.
Dr Faisal yakar6i magungunan yaduba, "kwarai yabaka magani mai k'yau, zazza6inne kawai yamaka naci, kuma inaga hakan yahad'a da buk'atar Hutu da jikinka keso".
Guntun murmushi ya khaleel yayi, "Dr aii Hutu bai ganniba nikam, kasan yanayin aikin namu".
"Hakane Ibraheem, amma gaskiya kad'an dinga dubawa, kana ayyukan dasukafi k'arfin jikinka sosai, garashin isashshen barci, amma tushen matsalar gaba d'aya shine tuzuranci". ' yay maganar cikin zolaya'.
Murmushi ya khaleel yayi, "Dr kaima zaka ta6ani kenan".
"Hhhh aikai d'innefa, shekaru kusa 37 babu mata? Amaryama tayi k'ok'ari data iya kar6arka".
"Hummm Dr kenan, bazaka ganeba ne kawai". 'Ya khaleel yay maganar idonsa nakan Aysha, datum d'azun take cikin matsananciyar kunya, saboda bayanin da ya khaleel kema Dr ko kunya babu, bawai fallasa sirrinsu yakeyiba, a'a musabbabin ciwon nasa yafad'amasa.
"yanzu dai bara ak'ara maka magunguna, saikuma nasaka maka k'arin ruwa".
Ya khaleel ya amsa da to yana janye idonsa daga kan Aysha.
Dr Faisal yasakama ya khaleel k'arin ruwa, sannan yace a samu towel k'arami a d'an jik'a da ruwa ana dannama ya khaleel d'in goshinsa, saboda yaji kansa yayi matuk'ar zafi.
Godiya baffah yamasa sannan yatafi, Anty Mamie tace, " Aysha tashi ki d'akko towel, saiki zubo ruwa ak'amin roba".
"To".
Aysha ta amsa tana mik'ewa.
Koda tadawo saita Taras su Anty Mamie duksun fice, wannan ya tabbatar mata cewa aikin natane, ganin idonsa alumshe tad'auka barci yakeyi, saman gadon tahau ta zauna kusada Kansa, tamatse towel d'in dagan ruwan ahankali tad'ora bisa goshinsa.
Ajiyar zuciya ya saki tareda bud'e lumsassun idanunsa yasauke kan Aysha saboda sanyin ruwan.
"sorry ruwan da sanyi ko?", 'tafad'a kamar zatayi kuka'.
Guntun murmushi yasaki, sannan yamaida idonsa yalumshe, k'in cigaba dayi tayi, saima ta6ige da kallon fuskarsa, jin shiru bata cigababa Yakuma bud'e idanun nasa akanta yace, "miya faru?".
Daburcewa Aysha tayi, bataso yakamata tana kallonsaba, shikuma saiyayi tamkarma baisan mitakeyiba, "cigaba Dayimin mana, kobakiso nasamu sauk'i?".
Girgiza masa kai kawai tayi, amma takasa magana, cigaba tayi da saka masa towel d'in tayi, ahankali kan yafara hucewa.Kamar daga sama Momy tafad'o d'akin ko sallama babu, kunyace tad'an kamata, dataga ansakama ya khaleel k'arin ruwa, amatsayinta Na mahaifiyarsa bashida lafiya har haka amma batazo ta dubashiba, alhalin kuma tasani sarai, ko yanzun zuwa tayi tamasa fad'a akan wai yak'i yaje inda take saboda yayi aure, saikuma tazo ta taras Ashe jikin nasane.
Batareda Aysha ta kalletaba tace, "Momy ina kwana".
Harar Aysha Momy tayi, batareda ta amsaba tamatso kusada khaleel, cikin d'an rikicewa tace, " Ibrahim! Dama bakada lfy amma aka gaza sanarmin? Tunkafin ayi nisa son rabani dakai akeyi kenan?".
Aysha data fahimci zancen Momy tsaf da ita take, saitayi murmushi, tana cigaba da goga towel a goshin ya khaleel tace, "uhmm to k'ila laifin Anty shukurah ne, Dan itakam jiyama kusan anan tawuni tareda kowa na gidannan, Momy inagama dai kekad'aice bakizoba sai Anty zuwairah dasu mufeedah".
Ya khaleel najinsu, amma kokad'an bai fahimci bak'ar magana sukema junaba, musamman yanda yaji Aysha nama Momy magana cikin girmamawa.
Magana Momy zatayi ya khaleel yabud'e idonsa, shiru Momy tayi tadawo da hankalinta kansa, saitakama borin kunya wai ank'i sanar mata.
Murmushi kawai yamata, amma baice komaiba.
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
AkcjaLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.