20

4.4K 328 5
                                    

2⃣0⃣


Sunana na yanka Halematussa'adiyya, kasancewar sunan kakata naci iyayena  ke kirana Ameerah.
   Ni 'Yar asalin garin sokoto ce, amma yanzu muna zaune da iyayena a Kaduna, nima a Kaduna aka haifeni, mahaifina mutumin kirkine, yanada k'ok'ari wajen kare mana mutunci dukda bamai kud'i baneba.
   Ga mahaifiyata kam Sam bahaka baneba, macece mai son birga da son mu'a mullah da hajiyoyin birni.
    Mu 5 iyayenmu suka haifa, nice d'iya ta uku acikinmu, yayyena biyu Suwaiba da 'Daheera duk halin mama suka biyo, kuma suna bin hud'ubarta daki-daki, wannan yasa suka tashi a fand'are, abin nadamun mahaifinmu, amma bashida damar tankawa.
    Awajena kawai yake samun sauk'i da sassauci, Dan bana k'etare zancensa, ahaka muka kammala secondary, yayinda nikad'aice nayi sauka acikinsu.
    Mahaifinmu yakiramu tareda sanar damu mu fido mijin aure, yabamu watanni uku rak.
     Nad'an shiga damuwa, saboda bana kula kowa, amma inada samari masu sona, ahaka nafidda Aminullah acikinsu, yayindasu Anty 'Daheera baba nata fama dasu, saida ya tsoratar dasu akan zai saki mama sannan suka kawo mazajen aure.
    Ansaka mana biki wata 11 saboda baba yasamu kammala yimana kayan d'aki.
       Bikinmu yarage saura wattani hud'u ALLAH yayma baba rasuwa, sakamakon had'arin mota daga Kano zuwa Kaduna.
   Mutuwar baba tata6ani matuk'a kuma najigatu nida sauran k'annena biyu baza.
   Amma gasu mama da su Anty Suwaiba bahaka bane, domin sufa duniya sabuwa fill, ko arba'in d'in rasuwar baba ba'ayiba mama ta aika gidan samarinmu cewar tafasa aurar damu.
  Dan acewarta bamu gama morar kanmuba bazamuje muyita bautawa k'artan banzaba, nashiga tashin hankali Aysha, Dan alokacin auren kawai nake buk'ata kasancewata mace mai yawan sha'awa.
      Rashin mafita yasakani dagewa dayawan azumi domin kame kaina daga halaka.
    Humm awata ranar laraba nadawo daga islamiyya agajiye saboda inazuwa hadda alokacin, saina tararda su mama sunbaje kud'i afalo suna irga, kud'ine masu shegen yawa, tsoron kud'in yasakani zaro ido waje da tambayar ina suka samu?.
    Mamace cikin hasala tace satowa mukayi Dan ubanki.
   Shiru nayi, jiki a sanyaye nashige d'aki domin cire uniform d'ina.
          Damuwar ganin kud'innan tahaifarmin dayawan kuka, na tabbata bata k'yak'yk'yawar hanya su mama suka samu kud'inba, to amma tambayata itace a ina suka samun?.
   Bansaniba, wannan yasaka nasama zuciyata salama, sati biyu da kawo kud'inan akafara gyaran gidanmu, gyara kuma namasu kud'i ahannu, aikam kamar jira 'yan anguwa keyi akafara surutu mahaifiyarmu tasakamu karuwanci, dama shiyyasa ta lalata aurenmu.
      Maganarnan tana k'onamin rai, amma banida amsar gamsar da jama'a, Dan nima bansan tushen kud'inba.
      Hummm inafad'a miki Aysha ranar saiga wata hamshak'iyar hajiya tazo gidanmu, dakaga matar nan kasan kud'i sungama zaunawa agareta, sunyi maganganunsu da mama, daga k'arshe aka kirani, wai matar nan tad'auki nauyin karatuna zuwa turai, tunda takarduna sunyi k'yau.
    ALLAH sairki rashin Sani, sainaita tsallen murna, Dan aganina zanbar gidanmu da abubuwan bak'inciki suka tare aciki.
     Cikin k'ank'anin lokaci aka gama mana komai, muka cane k'asar India.

Wannan tafiya itace tazamarmin tushen nadama da Dana Sani. Itace ta wargatsa rayuwata daduk wani tanadina, itace ta zama hajijiya dake wajiga zaren rayuwata ayanzu, tayi maganar tana kuka maicin zuciya.
   Aysha ma natayata.
    Tacigaba dafad'in munsauka k'asar india, hajia Fanta Ce takawo mu, intak'aicemiki dai bantashi nadama ba, saida john yaketa haddina adaren Dana kwana 2 dashigowata k'asar India, saida suka shayar dani kayan maye a drink sannan yayi yanda yaso dani, nayi kuka nakuma yi bak'inciki.
    Ashe ba makaranta zanyiba, kawoni akayi nayi karuwanci kawai, ankawonine domin cin amanar ubangijina.
    Abubuwa sun kwa6emin Aysha babu mai lallashina ko tausaya min, tun ina d'ari-d'ari da harkar har zuciyata takarye saboda bak'incikin mahaifiyata nafad'a tsundum, na tabbata tasan komai amma tabadani aka taho dani wata k'asar, Aysha mahaifiyata fa, wadda duk duniya tafi kowa sanin zafina, kaico da hali irin nami Mamana.
     Meerah tafashe da kula.
  Aysha bata hanataba, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
     Meerah tace, ayshan shed'anci da shagala yasakani daina sallah, nadaina azumi, na daina karatun alkur ani, dukna maye gurbin wad'annan da shaye-shaye, kwana a club, wlhy Aysha har blue film anta6ayi dani.
    Bak'aramar zabura Aysha tayi da jin furucin meerah ba.
    Cikin tsoro tace, ''Anty meerah da gaske?.
     Murmushi mai ciwo meerah tayi, tacije le6enta nakasa, tareda fad'in humm Aysha kedai abar kaza cikin gashinta kawai, ni k'arancin tunanina nayi hakane dundan aita d'orama mahaifiyata zunubi, tunda itace silar komai.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now