3⃣6⃣
Washe gari su Aysha basu tashiba sai around 9, wanka sukayi sannan mama takawo musu breakfast sukayi, bayan sun kammala suka fita gaida mutanen gidan.
Da Anty Mamie da umme Amaraya kawai suka gaisa, itama bata fita da wuri baneba, hajia babba kam tafita aiki, samarin gidan kowa yatafi uzurinsa, hakama su Amal, shiru gidan, 'yan ukuma sunfara makaranta shiyyasa gidan yayi tsit.
Sun d'an dad'e a 6angaren Anty Mamie sannan suka dawo d'akin mama.
Mama takallesu cikin soda k'aunar y'ay'an nata, tace, "kutashi Ku shirya baba bala yakaiku shoprite kuyo tsaraba.
To suka fad'a suna mik'ewa, Aysha tasaka wando da Riga sunmata k'yau.
Amma sai mama ta harareta, nifa matsalata da shiga al'adun wasu kenan, duk taka tsantsan d'inka sai yaro yakoyo abinda va tarbiyyarsaba, Aysha cire kayannan kisaka wannan less d'in, mama tayi maganar tana mik'ama Aysha farin less mai k'ananun jajayen fulawoyi.
Kamar Aysha zatayi kuka haka takar6a, itafa kayannan nauyi suke mata yanzu wlhy, amma bazata iya yima mama musuba, itama dai tasan masifar mama darashin d'aukar raini.
ALLAH yasotama siket ne ba zaniba, kayan sunyi masifar mata k'yau, gashi basu kama mata jikiba, bata d'aura d'an kwalinba, Dan bazata iya da wannan kayan nauyinba, siririn Jan gyale tayane katta dashi, gashinta datayi parking a tsakkiya yanata kyalli da k'amshi saiya zauna d'am a gyalen, har ana hango jelar gashin data kwanta a dokin wuyanta kad'an, saboda gyalen shara-shara ne, kasancewar yanda tayi acuci da gashin nata ya zauna sosai sai gyalen yad'an zama kad'an daga gaba, kwantaccen gashin gaban goshinta yayi luf-luf kamar atsaya kaita kallonta dan kyawun datayi.
Ita kanta mama saida tafurta masha ALLAH a zuciyarta, Dan tasan d'iyar tata abar kalloce.
Aysha tad'auki Ummu'hanee akafad'a tafita tana zun6ura baki, ita adole fushi takeyi ansakata saka kaya masu nauyi.
Fadeelah tabiyo bayanta rik'eda 🏧 d'in mama tana dariya.
Tunda suka Isa shoprite d'in k'irjin Aysha ke bugu da sauri-sauri, addu'a tafara karantowa ahankali, basuwani 6ata lokaciba suka fara duba abinda suke buk'ata, Aysha ce rik'eda keken🛒tana za6a tana sakawa bayan tad'an duba bayan, Anty fadelah Na rik'eda Ummu'hanee tana taya ayshar da shawara.Har sund'an gota shoprite d'in yadakatar da Emmanuel, Ema yataka burki ahankali yana fad'in yes sir.
Kamar bayason magana yace Ku koma baya mushiga shopping zan d'anyi.
OK sir EMA yafad'a a giramame.
Saida Ema yanuna ID cart d'insa aka bud'e musu gate d'in da sauri, motocin uku suka Shiga ajere.
Adams ne yabud'e masa k'ofa yafito, cikin takun Nutsuwarsa kamar kullum yake tafiya, yayinda su Ema ke take masa baya.
Sanye yake cikin Uniform d'in aiiki, amma babu hula a hannunsa, ko gun d'insama a mota yabarta, kallon yaransa yayi yace kowa yad'auki abinda yake buk'ata, baijira amsarsuba yay gaba.
Adams ne kawai yay saurin jawo keken yabi bayansa.
Sukuma sauran sunata Murna, da yabon adalin ogan Nasu, Wanda yasan darajar Na k'asa dashi, bashida bak'inciki ko kad'an, ga k'yautar ban girma, komai nasa abin sone, haka kowa yafara d'aukar za6insa suna zuba masa addu'a azuciyarsu.Bugun zuciyarta ne yatsananta, waige-waige tafara, Dan lamarin yafara tsoratata, babu wani alamar abinda yashafi rayuwarta awajen, Dan haka ta dake tacigaba da duba abinda take buk'ata.
K'un k'unan kuka da Ummu Hanee tafarane yasaka fadeelah komawa gefe tana jijjigata, Aysha kuma tak'arasa d'aukar abinda zasu d'auka.
Taku yakeyi cikin nuna shinfa jarumine mai wadataccen jini, kasaitarsa da kwarjini sun taka rawar gani wajen bayyana kwarjininsa, musamman kayan aikinsa dasuka k'ara haska chocolate colour d'insa mai matuk'ar taushi da d'aukar idanu, k'asumba tad'an taru masa afuska, hakama kansa akwai Y'ar kwantacciyar suma, hakan yanada nasaba darashin lokacin kai, Dan aiki ya cakud'e masa sosai a d'an tsakaninnan.
Yana tafiyane kunnensa manne da waya, magana yakeyi ahankali kuma cikin nutsuwa, Wanda baisaniba saiya d'auka da matarsa ko budurwarsa yakeyin wayar, fuskarsa babu walwala, yanayi yana duba abinda yad'auka, saiya d'an karanta kafin yajuyo yasaka a keken da Adams yake turawa.
Wannan salo nasa yayi masifar tafiya da y'an Matan wajen, kai hardama samari ma'abota son burga.
Dukda zuciyarta Na masifar harbawa hakan baisa tadamu da kallon wad'anda ke bayanta da gabantaba, anutse takai hannu zata d'auki wani kwalin biscuit, shima yakai hannu.
Akan nata hannun yad'ora nashi, da sauri kowa yajanye danjin wani masifaffen shock daya jasu atare, lokaci d'aya suka zubama juna idanu, burkitattun idanunsa masu girma da haske suka shige cikin Na Aysha manya masu yalwataccen gazar-gazard'in gashi.
Da sauri Aysha ta janye idonta cikin tsinkewar zuciya tace ya khaleel!, amma a hankali batareda yaji mitaceba, sai dai motsin la66anta dasukasha pink d'in janbaki.
Shikuma saiya d'an zaro idanunsa waje da mamaki yanunata yana fad'i you!!.
Itama saita dake tajuya idanunta dake matuk'ar d'aukar hankalin duk wani mai kallonta, ta murgud'a masa baki.
Ya salam! Yafad'a ahankali yana janye wayarsa daga kunnensa, yadafe kansa.
Ra6awa Aysha tayi tagefensa tawuce bayan tad'auki biscuit d'inta.
Ahankali yasaki siririn tsaki, aransa yace Aljana, mikuma tazoyi 9ja? Bayan a Canada yata6a ganinta?.
Murmushi Adams yayi, Dan ganin yanayin ogan nasa, addu'a yakeyi aransa ALLAH yakai damo ga harawa, kobai ciba zaiyi sukuwa akanta.
Ahankali ya sauke ajiyar zuciya tareda jan tsaki afili, yacigaba da d'aukar abinda yakeso.
Awajen biyan kud'i suka iske Aysha, Adams ne yabi layi dan biyan kud'insa Dana Oga hardasu Ema dakowa yad'akko abinda yakeso.
d'aukar Ice-cream da Aysha tatsayayi yasaka su ya khaleel suka zama sune abayansu wajen biyan kud'i, dayake Adams shiyyasa bata damuba.
Ya khaleel nacan tsaye gefe tareda wani abokinsa dasuka had'u yanzunnan.
Bayan anduba kayan tamik'a musu ATM d'in suka cire.
Dukda zuciyarta Na farinciki da ganinsa hakan bai hanata k'in kallon indama yakeba, kad'an yarage tafita wasu garadan samari suka fad'o wajen suna ihu, hannunsu rik'eda bindugu.
Gaban Aysha yafad'i, aranta tace 'yan fashi?.
Harbin da macen cikinsu tayine yasaka illahirin mutanen wajen zubewa a k'asa, saidai banda ya khaleel dako gezau baiyiba, ita kanta ayshar ALLAH bai saka mata tsoroba, Dan kunnenta kawai tatoshe saboda k'arar bindigar, bayan tasaki ledojin hannunta.
Ya khaleel yafara ta6a aljihumsa, amma saiyaji babu gun ko d'aya, hankalinsane yad'an tashi, gashi babu yaronsa ko d'aya akusadashi, abokinsa kam tuni yabi layin masu kwanciya ak'asa, sai ta6a k'afar ya khaleel d'in yakeyi waiya kwanta.
Ya khaleel bai kulashiba, hankalinsa Na wajen ta'ina zai samu bindiga?.
Aysha talura sarai da nufinsa, wannan yasakata kallon garjejen k'aton kusada ita, Wanda shi kansa tsaye ya khaleel yayi attack.
Hankalintane yatashi lokacin dataga yafara saita kunamar bindigarsa.
Cikin wani salon jarumta Wanda batasan tanadashiba ta wulla handbag d'inta tadaki hannun guy d'in, bindigar da bullet d'in daya harba sukayi wani tsalle.
A cikin salon samun cikakken training ya khaleel ya ca6e gun d'in.
Budurwar tayo kan Aysha da bindiga, yayinda saurayi d'aya Yakuma sakin kunamarsa akan ya khaleel, hankalin Aysha yayi masifar tashi lokacinda taga bullet d'in gadan-gadan a tsakkiyar kan ya khaleel daya juya baya zai sauka.
Wani wawan tsalle tayi, saigata gabansa, tayi masifar hankad'ashi iya k'arfinta, kad'an yamatsa saboda batakai matsayin iya turashiba, hakanma tayi jarunma, dan dukkan k'arfin datake tak'ama dashi tasaka.
Turashin datayi saiya zama bullet yadawo saitinta zai sauka bisa k'irjinta.
Adai-dai lokacin kuma ya khaleel d'in yajuyo dansan ganin Wanda ya hankad'ashi haka?.
Cikin zare idanu yakai mata wawura, jikinsa har rawa yakeyi yaymata runfa da faffad'an k'irjinsa, bullet d'in yasauka a gadon bayansa, kasancewar akwai Riga, makarin bullet ajikinsa sai bai shigaba yafad'i.
Tana rungume a k'irjinsa, yayinda yake aduk'e da ita, cikin salon iya aiki ya harbi k'afar d'an fashi d'aya, yakuma juyawa cikin zafin nama yaharbi k'afar d'ayan, macen kuma sai harfi takeyi babu ka'k'k'autawa, amma babu Wanda yasamu ya khaleel ko Aysha acikinsu, Dan sosai Aysha ta mamuk'e ya khaleel saboda a tsorace take yanzu.
Su Ema dake shigowa tabaya suka hankad'a macen tadaki keken baskets d'in dake jere agefe suka tafi suuuu itadasu.
Sai asannan ya khaleel yad'ago, amma haryanzu yana rungume da Aysha datayi lamo ajinkinsa.
Kowama awajen yamik'e tsaye ana kallon ikon ALLAH, wasukam har yanzu a tsorace suke da lamarin.
Sunkama 'yan fashin su hud'u, ya khaleel sai alokacin yasamu damar janye Aysha daga jikinsa, itama lokacinne tadawo hayyacinta, hannunta yarik'e GAM anasa, batareda wani tunaniba.
Cikin 'yan fashin guda d'aya dake hannun Adams yak'arasa, haryanzu hannunsa rik'eda nata, baiyi wata wataba ya harbi k'afarsa d'aya kamar yanda yayma sauran, wata razananniyar k'ara kuwa yasaki, da sauri Aysha ta fisge hannunta daga cikin Na ya khaleel ta toshe kunnenta.
Saima yanzu yatuna da hannunta Na cikin nasa, sakin hannun yayi da sauri, Dan baya buk'atar azargi wani Abu daban, amma tabashi mamaki over, wai ita wacece?, yarinya kamar aljana, ga rashin kunya ga jarumta, wani gefen zuciyarsa yace gakuma taimako, dam badan itaba da dolene cikin harbi biyu da'aka masa bai saniba dolene d'aya yasamesa .
Amma duk itace tabashi kariya, gata 'Yar ficit, yay maganar yana k'aremata kallo sama da k'asa.
Itakam Aysha har lokacin hannunta Na acikin kunne takuma lumshe idanunta.
Maganar Adams ce tasakashi janye rikitattun idanunsa daga kanta, yamaido kan Adams, Adams yay salute nashi, yana fad'in sir! Mukira police mubasu su?.
No, yafad'a atak'aice.
Nufar inda gyalen Aysha yake a yashe da handbag d'inta yana fad'in Adams inason binciken kwana biyu akansu, Dan da'alama ba fashine yakawosuba, wani suka biyo.
K'arewar maganarsa tayi dai-dai da dawarsa kusada Aysha data fara bud'e idonta yanzu a hankali.
Batareda yace mata uffanba ya yafa mata gyalen akanta kamar yanda yaga tayi d'azun, yamik'a mata handbag d'inta fuskarnan ahad'e babu walwala.
Kar6a tayi fuskarta akwa6e, kokad'an yagaza fassara yanayinta, ya kauda kansa daga kallonta, ahankali yafurta *_Thanks_*, yacigaba da takunsa cikin nutsuwa harya fice batareda yakuma ko waiwayotaba.
Adams ne yadawo yad'auki kayansu, yamatso kusada Aysha datake tattara nasu wad'anda suka zube, cikin ma'aikatan wajen wani Na tayata.
Mungode sosai 'Yar uwa, Adams yafad'a yana murmushi.
Itama murmushim tayi ta jinjina masa kai dafad'in babu komai yiwa Kaine.
Godiya yakuma yimata sannan yafice da sauri.
Itama takar6i ledojinta tana waige-waigen Neman Yaya fadeela.
Can ta hangota tafito daga wani lungu rik'eda Ummu'hanee.
Ajiyar zuciya tasauke, tace Yaya Fadeela kina lfy keda my dota?.
Lfy lau muke Aysha, keza'a tambaya wannan, sannu da k'ok'ari, irin wannan jarumta haka?.
Murmuahi kawai ayshan tayi tace muje to.
Sai kallonsu mutane keyi, ma'aikatan wajen kam godiya suketaima Aysha, itadai tafita tana mamakinsu, azuciyarta kuma tana farincikin tabama abin sonta kariya da k'arfin ikon ALLAH, Dan ba wayonta baneba.
Koda suka fito tuni motocin ya khaleel sun fice daga wajen, baba bala yataresu arikice da tambayarsu suna lfy?.
Lafiya lau baba bala suka bashi amsa da gamsuwa.
Mota suka shiga Yaya Fadeela naba baba bala labarin yanda abun yafaru.
Aysha kam tayi shiru, hankalinta nakan ya khaleel, tana tunanin randa zasu had'u yakuma ganata acikin gidansu, Dan taga yayi mamakin ganinta a 9ja, bayan kuma a Canada yasanta.
Wayarta tazaro tanemo layin Anty meerah, dantayi kewarta, wayar akashe, tamaida akalar kiran kan Ifteehal, itama Switch up, d'an tsaki tayi, Dan batason kiran maheer ya takura mata.
Tamaida wayar bag danufin zuwa anjima zata sake gwadawa.
Ahaka suka k'arasa gida, suna shiga harabar gidan taci karo da motocin ya khaleel Na niyyar fita daga gidan, da'alama sun kawoshine yace suma suje su huta, dama haka yake musu, saboda sanin hakkin d'an Adam, yasan yanda yake da uzuri, suma sunadashi, wasunsuma harda masu iyali, kuma aii suma suna buk'atar hutu, kamar yanda duk lokacin dazaizo gida danufin ya huta yake zuwa.
Saida suka fara sauke 'yan fashin a inda yadace, sanan suka kawoshi gidan.
Gaban Aysha Na lugude suka fito daga motar, cikin gidan suka shiga kai tsaye.............✍🏿
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
ActionLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.