49
Washe gari da yamma saiga Taheer da Joseph, dukda babu angon nata taji dad'i sosai, batada wasu k'awaye dasuka wuce y'an uwanta, sai maleeka da Tasleem, komai a hannunta suka damk'a, dukda tasanar dasu babu wani Abu dasuka shirya.
Kafin tafiyar nasune ya khaleel yakira wayar Taheer, bayan sun gaisa da maganganinsu yasanarmasa suna Kano.
"Kano kuma? Mikukajeyi a kano?".
Taheer yace, "Munje wajan amarya mana, kaibaka cemana komaiba gameda shirin biki, shiyyasa mukaga yadace muje".
"Uhmm OK, to yanzu yakukayi?".
"No babu komai, Gatama muna atare".
"Bata wayar".
Aysha dake magana da Joseph Taheer yamik'ama waya, ta amsa batareda sanin dawa zatayi maganarba Dan sanda aka kira Taheer matsawa yayi daga wajensu.
Asanyaye tace, " Assalamu alaikum".
"Wa'alaikissalam!, muryarsa tadaki dodon kunnenta, maganarsa takatse tunaninta"...
"Kinajina? Banason wani shirmen day day d'inan, karnaji ance kunhad'a wani events na banza da wofi, dan bana buk'ata, nabama Amatullah sak'o tabaki, tundasu ranar Friday zasu zo nan kano, ni saima ranar zan dawo dasafe".
Muryar Aysha a sanyaye tace, " ALLAH yatsare hanya".
"Ameen ya amsa" yana yanke wayar.Su Taheer sukamata sallama suka tafi.
_________________________,_
Ranar Alhamis aka sakasu Aysha a lalle, bawani taro akayiba, irin al'adar Malam bahaushe tada akamusu, matar yayansu Qaseem ta feshesu da turare da fauda, aka rangad'a gud'a akansu, shikenan.
Sukad'an cigaba da sabgoginsu Na a are da k'awayensu.
Aranar su Ameerah suka sauka daga Canada, Aysha tayi murna sosai tamkar anyi mata bishara, baby Raudat tayi girma sosai, yarinyar abin sha'awa wlhy, ifteehal tashige cikin k'awayen amarya anata abubuwan arzik'i, meerah kam tanataredasu Hafsat fadeeala dasu amal.
Washe gari su Anty Ama... Suka iso suma, harda Anty Mamie da Ammah, su inna ma y'an Jigawa sun iso.
Gidafa yayi dank'am dajama'a, abin ba'a cewa komai.
Ranar juma'a aka d'and'asama amare k'unshi, gaskiya sunsha k'yau abin har ba'a cewa komai, sunje wankin kai da yamma, sanda suka dawo gidan ko'ina bak'ine, anata aikin gyaran kayan miya dadai sauransu.
Aysha tafad'a jikin Anty Mamie tana murnar ganinsu.
"Eyee kaga d'iyata amaryar kamshi, k'unshin yayi k'yau sosai wlhy, waye yamukune?".
"Anty Mamie wata k'awar Anty Nasara ce".
"Wacece Anty Nasara?".
"Matar ya Qaseem.
Kai gaskiya ta'iya sosai, kunsha k'yau kuduka".
"A'a amaryar Yaya babu magana?"..
"Hannu Aysha tasa tarufe fuskarta, kai Anty Ama....ALLAH ban gankiba, dama kinzo?".
"Wai Aysha babumu abikin babban Yaya aii gayya ta 6aci, kintaho da kwana biyu Na iso, randa muka kawo kaya kuma kika 6uya mana, ya hidima?".
Y'ar dariya Aysha tayi kawai batace komaiba.Nan dai abokan wasa suka cigaba da tsokanarsu.
_____________________________
10:23am jirginsa ya sauka Nigeria, su Adams sukaje suka d'akkosa, yana bayan mota zaune, sai amsa calls na jama'a yakeyi, musamman abokansa dasukasan da dawowar tasa.
Bayan ya cire wayar akunnensa Adams yace, "aii Oga bak'ifa suncika tab wlhy, bakaga jama'aba, abin ba'a cewa komai, saidai ALLAH ya kaimu gobe a d'aura aurennan lafiya kawai".
"To ameen Adams, yanzuma youseef ke sanarmin su Sameer sunkusa sauka suma, yazata bamubar airport d'inba mutsaya mutafi dasu, nacemasa mun baro".
"Ai wlhy oga tunjiya babu abinda mukeyi sai kwaso jama'a kawai, a ciki da wajen Nigeria, aii mutum mai jama'a yamore arayuwa".
Murmushi kawai ya khaleel yayi, amma baice komaiba.
"Oga Asokoro zamuje kokuwa mai tama?".
"Adams muje mai tama tukun, zanyi magana da baffah, kuma zand'an k'imtsa ko, saiku barni a can kukoma d'aukar su Sameer d'in, zuwa dare zan k'arasa can gidan".
"OK sir, hakan yayi aii".'Dan gwari yabud'e musu gate suka shiga, nanma gidan akwai jama'a sosai, y'an uwan mahaifin hajia babba sunzo sosai, hakama 6angaren mahaifiyarta Wanda sukazama dangin gidan, tunda da Ammah da mamanta uwarsu d'aya uba d'aya, danhaka sai dangin sukazama d'aya, wasukuma suna kano sai an d'aura aure gobe su k'araso abujar.
Najwa d'iyar Anty zuwaira tazo da gudu kamar zata rungumeshi, amma saitaja birki, Dan wargima waje yaka samu, "uncle oyoyo".
Murmushi yamata tareda fad'in "dota ank'araso kenan?".
"Lah uncle yau kwananmu 6 fa a Abuja".
"Eye kunsha Abuja abinku, muje ciki to".
Kar6ar jakarsa tayi suka k'arasa ciki, tun afalo suka fara gaisawa da jama'a, wasu nad'an tsokanarsa da ango kasha k'amshi, amsarsa d'ayace murmishi.
Saida yashiga 6angaren Momy suka gaggaisa da jama'a sosai, itama momyn sun gaisa a tsaitsaye saboda bak'i, yafito zuwa 6angarensu.
Duk samarin gidan sunan hardama k'arin bak'i, sunbaje afalo kowa na harkar gabansa, wasu kallo wasu gugar kayansu na kwalliyar biki, masu danna waya nayi, masu hira nayi.
Duk suka Shiga masa sannu da zuwa da gaisheshi.
Ya amsa fusakarsa d'aukeda murmushi.
Saida yashige sannan "Hafiz yace a lallai Yaya nason aurenan, irin wannan fara'a haka".
Ramadan yace, "dagedai yajika, dawani kankan like kwakwa".
Dariya sukayi gaba d'aya.
So rayuwar families d'in tana burgeni gaskiya, komai nasu cikin mutunta juna.
Bayan kamar awanni biyu yafito, ya tambayi su Musleem Anty Mamie fa? Yaga baigantaba da sauran yaran?.
"Ya khaleel ai wad'annan sun tsufa a kano, tuda asuba suka tafi, dagamu sai baffa da umme amaryar saikuma Momy dasu Anty zuwairah aka bari"..
Jinjina kansa yayi sannan yafita, yana nazarin hidimar bikin nasa.
Yaje sun gaisa da baffa, Wanda shima yana tareda bak'i abokansa dasukazo daga Turkey, dakuma dad d'insu ya Naufal.
Baffa yajashi gefe suka tattauna sosai, akan d'aurin auren na gobe, dakuma walima da aka shirya bayan d'aurin aure, wadda aka gayyaci manyan malamai dazasuyi lectures awajen, sannan baffah yabashi akwati guda na d'unkunan biki dayamasa.
Godiya sosai yayma mahaifin nasa sannan ya sallamesu yatafi inda bokansa suke.
bayan Momy takar6i kud'ad'e masu yawa a hannunsa.
Acewarta sisinta bazaiyi kuka a bikinba, shida ya yarda sai dai ayi da gumimsa.
Bai nemi ba'asiba yamata transfer yatafi.
Yana shigowa abokansa suka saka ihun ganinsa, shima yayi farincikin ganinsu sosai, wasu andad'e ba'a had'uba, tun'a schools, harda wad'anda sukayi Secondary dakuma University, abokan aiki dakuma na kasuwa, y'an uwa da abokan arzik'i, nanfa akashiga hirar yaushe gamo da firar abokan ango dakowa yasani.
Abdul'azeez yace, "wlhy mamaki nakeyi wai J! Da mata?".
"Aii bakai kad'aiba cewar Nawaff, kasanfa wasanmu na k'arshe a k'asar Argentina damuka had'u nake masa maganar aure, cemin yayi babu rana".
Mahmud yace, "aii mutumin namu akwai taku, amma dai bahaka zakajema yarinyar mutane kana mazuraiba?".
Hararsa j yayi, "kai banason iskancinkufa, kai ince mazuran karingama Noor da billy, kaikuma Nawaff saboda jarabarka dafad'a kuka fara da Yasmeen ahad'uwar farko, su mai mata uku Abdul'azeez (Dady) kam aiba'a magana".
Harara Dady ya wullah masa, "kai Malam yanzu matata d'aya my Munnerah kaji".
Dariya suka shek'e da ita, Sultan yace, "wlhy auren mata biyu da dad'i, Juwairiyya takula dani, itada ikram d'ina haka, uncle G dake gefe yace kai malam my sopy ma ba bayaba, auredai dacene kawai". Mus'aff yace, "wannan gaskiyane, idan INA gaban My Nazeefa tamkar kwai a cokali nake". "Muzzaffar ya kar6e dafad'in wlhy haka Ameedah na take, tauraruwata kenan".
Isma'il yace, "kukefad'a anaji, aii soyayya sai Iman d'ita wlhy". hummm kowa nasa yasani, kuje gidana kuga yanda Rahma ke riritani Cewar Abdulmaleek bobo. Umar Fharuk yashek'e da dariya, "amma sanda aka aura maka ita kanata wani dojewa kai na Ni'ima, hakanayi a lokacin aurena da Asma'u, amma yanzu kam babu kamarta". "kana nufin har Uwargida Lubna?".
"Daga baya kenan malam".
Shureim ya shek'e da dariya, "aiini nida my badar sai mutuwa".
Khaleel da sauran abokan daketa binsu da kallo suka shek'e da dariya, "to iyayen soyayya, sannunku da k'ok'ari".
"Yauwa Wanda bai iya soyayyaba, kaima aii zaka shiga layinmune, daga gobenefa".
Sameer yace, "ALLAH kasadamu da matan kwarai, bilyn Abdull nimafa yakamata labarina yashigo layi gaskiya".😂👍🏻.
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
ActionLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.