55
......Tana nan zaune wajen tunanin kazar dazata biya yafito, da Alana alwala yayi, ya kalli Ayshan fake satar kallonsa ta gefen ido.
“tashi kije kiyi alwala”.
"Nafayi sallar isha'i har shafa'i da wutirima". 'Aysha tayi maganar a shagwa6e'.
Batareda ya kalletaba yace, "umarinine ba shawaraba".
Yanda yay magana cikin d'aure fuska sai tsoro Yakama Aysha, jiki a sanyaye tatshi zataje d'akinta, ak'asan ranta tana mamakin halayen ya khaleel masu rikid'a kamar hawainiya, yanzu zaimaka maganar arzik'i, yanzu kuma zai juya ta tsiya.........
"Ina kuma zakije?".
Maganarsa ta katse mata tunani, harta kama k'ofar tasaki, juyowa tayi garesa, amma kanta ak'asa takasa kallonsa.
Ya fesar da zazzafan huci daga bakinsa, a zuciyarsa yana fad'in matsalar auren k'ananun yaran kuma kenan, komai saika koya musu, ansaka surutu da ciwon kai, yaja guntun tsaki afili.
Aysha dai tana bakin k'ofa tsaye saikace dogariya.
" idan bazakiyi alwalarba kiwuce ki tafi".
Muryarta Na rawa tace, "kayi hak'uri, aii alwalar zanje nayi, daganan nad'akko hijjab.
Banza yamata Yakoma kan sofa ya zauna, tareda d'aukar wayarsa yahau danne-dannen k'addara.
Ganin ta 6ata masa rai, sai kawai tayi tunanin bara tayi a toilet d'insa, a d'arare tawuce tashiga toilet d'in, babu dad'ewa saigata tafito, shareta yayi, saida tace, " nayi alwalar".
Nanma ya6ata wasu mintuna sannan yamik'e, ya mik'a mata hijjab, kar6a tayi tana mamakin a ina yasamo?.
Jam'i yajasu raka'a biyu, sannan yadafa kanta yay addu'ar da addini ya umarcesa dayi, daga nan yazarce kwararo addu'oi akan musulmi baki d'aya, masu rai da matattu, marasa lafiya da fannin aiiki!.
Aysha dai y'ar amince, nima daga gefe ina amin, amma ahankali.😂.lolBatayi mamakiba, danta gama yarda da mijin nata a fannin ilimin addini, yayi zurfi bana wasaba, bayan shafa addu'ar yajuyo gareta suna fuskantar juna, yatsareta da wad'annan mayun idanun nasa, masu kwarjini da hasken aminci, cikin taushin murya dabatasan yanada itaba yafara mata tambayoyi akan addini, cikin harshen larabci.
Itama cikin harshen larabcin take amsawa, inda takeda rauni yakan tunatar da ita, daga k'arshe suka kuma rufewa da addu'a.
Ya Sanar da'ita zai samo mata islamiyya tacigaba, tunda yaga tayi nisa sosai a ilimin addini, aganinsa baikamata a dakushetaba.
Tamasa godiya cikin raunin murya, wadda tak'ara tsundumasa cikin wani yanayin shauk'i Na musamman.Hattara samari
yakamata idan kayi sabuwar amarya, adaren farkonku, bayan kun gudanar da sallah domin Neman tabarraki, kad'an kwankwasa amarya dankaji ya kwarinta a fannin addini, tanan zakasan wane mataki zaka d'auka domin gyara fagen tarbiyyar y'ay'anka tunkan suzo, kaga idan akwai rauni ta fannin addininta saika maidata islamiyya, kokuma idan kai kanada lokaci karinga d'ora mata agida, inaga hakan zai kawo gyararraki a gidajen ma'auratan da suke cikeda hargitsi a halin yanzu, Dan wlhy k'arancin ilimin addini Na taka rawar gain wajen ruguza tubalin ginin rayuwarmu baki d'aya, ko k'arancin tarbiyyarnan daya addabi al'ummarmu harda jahilcin ilimin addini, Dan munfi bama boko amanar kanmu da y'ay'anmu, ALLAH yasa mun fahimci sak'on.Da kansa yazarema Aysha hijjab d'in, itadai duk kunya da mamakin sun cikata, wannan sabon salon Na ya khaleel yad'aure mata kai.
Yaymata umarni akan tatashi takoma kan sofa, babu musu ta tashi, Dan babu wasa acikin al'amuran nasa, shikam yana d'aurewa ne dankar Aysha ta kawo masa raini.Nace.hummmm.🤪👍🏻sai babana.
Ficewa yayi, babu dad'ewa saigashi yadawo d'aukeda fresh milk da glass cup, kusada ita yazauna, kan Aysha na k'asa tana wasa da yatsun hannunta da har yanzu lalle yake rad'am bai fitaba, hakama na k'afafunta.
Fresh milk d'in yazuba yasha kusan rabi, sannan ya d'ora cup d'in abakin Aysha, d'ago idanu tayi ta kallesa, ganin fuskarnan babu alamun wasa ta lumshe idanunta tareda bud'e baki tana sha, saida ta shanye tas sannan ya janye cup d'in, tashi yay dasu a hannu yad'ora bisa dirowar gefen gado, yashiga bayi, kusan mintuna 20 saigashi yafito d'aure da towul.
Aysha tai saurin rintse idonta, danta tsorata da ganinsa haka, shikam baimasan tanayiba, yace, "tashi kije kiyi wanka mu kwanta, koba kince barci kikejiba?".
Jinjina masa kai tayi, Dan babu bakin magana, miyyasa zaice wankanma ad'akinsa zatayi? Yana nufin barcinma tare zasuyi? Itakam yau taga takanta, mi ya khaleel ke nufi da itane?, da wannan tunanin tashiga bayinsa tayi wankan, tayi brosh, duk wani abin k'amshi datayi karo dashi a bayin saida tayi amfani dashi, tasaka farar rigar wankasa, tsaye tayi takasa fita saboda kunya.
Muryarsa tajiyo yana fad'in " kifito kiyi shirinki, ni Na fita falo", baijira cewartaba yafice abinsa, yasan inhar yana nan bazata fitoba d'in.
Tanajin alamar fitarsa tafito, cikin mamakin take kallon kwalliyar furanni da akama gadon, harta Shiga wanka dai babusu, kuma blue d'in bedsheets nema agadon d'azun, amma yanzu an lailayeahi da Fari tas, sannan aka k'awata tsakkiyarsa da furanni ja da farare, anyi love k'ato💝.Nace Aysha tunda rana mai d'akin yayi abunsa, ya lulu6a wani bedsheets d'in Asama Dan karki gani, 😏to ammafa batajiniba, Dan ina la6e a bayan labuloli, gudun kar ya khaleel ya ganni, ya koroni rahoto ya wuce daku🤥🤧.
Mansa tad'auka ta shafa, mai sanyin k'amshi, ta faffesa turarurrukansa, tunanin yanda zata d'aukar kayan barci d'akinta tatsaya yi, idontane ya sauka akan rigar dake gefen gadon, fara mai adon firanni jajaye, d'aukar rigar daketa wani bala'in k'amshi tayi tabud'e, kutt tafad'a tana zaro ido waje da bud'e baki😨, mi ya khaleel yake nufi? Ni shatu d'iyar Abubakar, waini zan saka wannan rigar natsaya agabansa?, kai impossible wlhy bazan iyaba, aii wannan rigar da ita da babu duk d'ayane, shiko kunyama bayaji?.
To amma kuma idan ban sakaba akwai matsalafa, bara kawai nasaka kafin ya shigo, saina saka hijjab, kinga Na rufama kaina asiri kenan.
Cikin hanzari tasaka rigar, cif taimata tamkar an gwadata, gashi Tamata bala'in k'yau, ta haska farar fatarta, tajuya tana fad'in woow! Ammafa Na had'u wlhy, ko a ina ya khaleel yasiyo rigar barcinnan? Nibamma ta6a ganin kayan barcin dasukamin k'yauba irin yau, da Sauri ta tufk'e gashinta (Dan Aysha dama can batason kitso, kullum kai atsefe, sai mama Tamata tsiya takeyi ko gudun dukan makaranta, tokuma zamanta a turai d'innan Yakuma lalatata akan k'in kitso).
Hijjab d'in datayi sallah tad'auka ta zumbula, tana gama sakawa kuwa ya khaleel yashigo d'akin, tsaye tayi jikin madubi tayi k'asa da kanta, takasa d'agowa ta kalleshi saboda kunya, gani takeyi kamar yana kallon rigar tata.
Cikin takunsa Na nutsuwa da k'asaita yak'araso Inda take, zuciyar Aysha tak'ara k'arfin gudu da sauri-sauri, saida ya kalli gadon yaga babu rigar sannan yamatso kusada ita, kumayin k'asa tayi da kanta.
Guntun murmushi yasaki, sannan ahankali yakai hannu kanta yana k'ok'arin cire hijjabin.
Da sauri tadafe tana fad'in "please ya khaleel kabarmin". 'Tayi maganarnr kamar zata masa kuka'.
Harara yasakar mata, wadda tasakata cire hannunta dole, shikuma yacire hijjabin, da k'arfi Aysha ta rintse idanunta, siraran hawaye nabin kumatunta, yanzukam tadaina mamaki saidai tsoronsa daya fara shigarta, tarasa dalilin ya khaleel nayimata hakan.
Ya khaleel kam yagama mutuwa atsaye, saboda k'arema halittar Aysha kallo dayakeyi daki-daki, rigar tayi masifar yimata k'yau fiyema da zatonsa, tamkar an halicci rigar ajikintane, baisan sanda ya furzar da sassanyan huciba, yasaka hannunsa yana sharema Aysha hawayen dake zirara a kumatunta, har yanzu idanunta arufe suke, yad'an lumshe idonsa yana sakin guntun murmushi, tad'an bashi dariya, Ashe duk tsiwar tata matsoraciyace haka?".
Jitayi kawai ya mannata da jikinsa, atare suka saki sassanyar ajiyar zuciya, cikin wata irin muryan da Aysha bata ta6a zaton ya khaleel Nada makamanciyarta bama bare itad'in yake mata magana acikin kunne, " Ashe duk tsiwarkinnan ked'in matsoraciyace sholy?".
Gaban Aysha yafad'i, danjin sunannan akaro Na biyu daga bakinsa, yacigaba dafad'in ked'infa jarumace mai kare mijinta daga harbin bullet, matar police aii police ce inji masu iya magana.
Gaba d'aya kalamansa sun dulmiya kwalwarta a awata duniyar tunani tadaban, kafin tadawo hayyacinta yacirota daga jikinsa, yakamo hannunta da'aka k'awata da zanene lallale ya sumbata, sannan yace, "bud'e idonki".
Babu yanda zatayi, dole tabud'e idon nata, amma takasa kallon inda yake, shiyamata jagora har gaban gado, danta kasa bud'e idonta da k'yau saboda kunya da tsoro.
Yace, " bud'e idonki ki kalli gadonnan".
Bud'e idonta tayi sosai bisa gadon, an lailayeshi da da farin bedsheets, Flowers d'in sunyi k'yau sosai agadon, sai k'amshi furannin sukeyi, anyi wani rubutu da flowers d'in a tsakkiya, Wanda ayshan takasa ganewa, amma saitaga kamar tata6a ganin rubutun, to amma a ina?, wannan shine abin tambayar.
Batakai k'arshen tunanintaba taji an sureta andire bisa gadon, kafin tayi wani yunk'uri taji bakinsa cikin nata🤫.
Abubuwa masu wuyar fassara ga Aysha suka cigaba dagudana, tuni tsoro da firgici sun gama cikata, jikinta sai 6ari yakeyi, shikansa boss d'in jikinsa tsuma yakeyi, abinka da sabun shiga🤭.
Da zafi-zafi yake sarrafata, (hummm auren tuzuruma aii had'arine alkur'an🤣).
Yaukam Aysha tagane batada wayo, yayinda ya khaleel yanufi yin mai gaba d'aya sai Aysha ta rikice masa da kuka da magiya, abinda yaso faruwa tsakaninta da john yafad'o mata rai, tatuna yanda ya kacaccala Ngozi ranar a maimakonta, tuni k'arfin kukanta yak'aru, ganin zata masa tonon silili yarufe mata baki danasa🙊.
Anzo wajenda alk'alamin bilynku bazai iya aikiba😒, dan haka nakwaso akorikurar k'afafuna da d'an littafina da alk'alami nayo waje, inama Aysha addu'ar fitowa lfy,🚶🏻♀, Dan irinsu ya khaleel tuzurai sai anhad'a da addu'ar🤐😫😝.Cikin sand'a da dabara suka hauro katangar, sukusan 6 ne, kuma duk garada majiya k'arfi da k'uruciya.
Ahakankali suke zagaye 6angaren nasu ya khaleel, wanda yajia khaltum tamusu kwatancensa.
Gwaska yace, "mufayi komai da lura, kunsandai mijinta kowanene, amma haija ta tabbatarmin baya cikin gidan, ita kad'aice, Dan haka mu kwamusota cikin taka tsantsan mu fice kawai............✍
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
ActionLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.