61
Wajajen 1 Momy tafarka, duk suka shiga suka dubata, kanta kawai take iya d'aga musu amma babu magana, ya khaleel dakansa yabata abinci abaki, Aysha Na mamakin irinson da ya khaleel kema mahaifiyarsa.
Baffah yace, duk sutashi su koma gida, itamad'in an sallamesu.
Kaya suka shiga harhad'awa, sai gida.Tunda suka dawo ya khaleel Na 6angaren Momy, yana zaune kusada ita yanzuma a bedroom d'inta, itakuma tana kwance, tarik'o hannunsa tana magana ahankali, "Ibraheem inaso aiima mufeedah aure, kazaunar da ita tafad'ama Wanda takeso kaimasa magana yafito, saika sanarma baffanku".
" amma Momy miya faru haka? Lokaci d'aya ace ta fidda miji?".
"Ninasan minagani Ibraheem, mufeedah Neman zubar mana da mutunci takeyi agidannan, gaban kishiyoyi da 'yan uba, mufeedah sotake amin dariya da eho agidannan", nan Momy takwashe duk abinda yafaru jiya tasanar masa.
Sosai ransa ya6aci, amma Momy tace yay shiru Dan ALLAH, fitowar maganar tamkar tonon asirinsune, kawai yasaka mufeedah ta fidda mijin aure, su aurar da ita kawai ahuta.
" shikenan Momy zan mata magana, Dan ALLAH kema kicire komai aranki, kingafa jiya ALLAH ne ya kiyaye fad'uwar dakikayi, bawuya saikiga ansamu matsalar ciwon 6arin jiki, kisama zuciyarki hak'uri".
''To ibaraheem ngd".
Ya jinjina mata kai, cikin hikimar iya zance yayta bata labari mai dad'i da kwantar da hankali, itama saitaita sakin jikinta, saida yaga tasamu 'Yar nutsuwa sannan yabarta._______________________________
Kusan kwanaki biyu Momy Na jiyya, Alhmdllh sauk'i yasamu.
Kulawa dai sosai tana samu wajen 'ya'yanta, musamman Anty shukurah da ya khaleel.
Anty zuwairah dai babu damar zuwa, saidai waya takira Tamata sannu.
Ayau kuma Aleeya zata iso daga England.
Sosai Momy tasaka akema zuwan NATA shiri Na musamman, d'aki guda tasa aka gyarama Aleeya a 6angarenta, komai Na buk'ata aka tanada mata aciki, kaikace wata sarauniyar bak'uwa zasuyi, (lallai Momy nason Aleeya kam).************
"Nikam dakinbar shayinnan natafi kawai, inada aiki sosai a office wlhy".
" please yafa huce, wlhy nasan katafi zaka mance da yunwar cikinka ne kawai, gashima ya huce aii".
Kar6an mug d'in yayi yana girgiza kai kawai, yay bismillah yafara sha, "rigimarki yawane da ita Sholy".
" nidai kadaina cemin wata sholy, wai a inama kasan sunan?".
"Bakinsa yata6e, yana shan tea d'in da dankali ad'an hanzarce, saboda saurin dayakeyi yafita, yajuyo yana kallonta, kinsan a ina asan sunan?".
Girgiza masa kai tayi, batareda tayi maganaba.
Ya maida kansa kan abincin, ''wajen meerah naji, nikuma sunan yamin dad'i, Dan haka dole abarni nake kira".
"uhm, Aysha tafad'a tana tunzuro baki".
Mik'ewa yayi yana gyara belt d'in wandonsa, danharya shirya cikin uniform d'insa masu k'ara masa kwarjini da cikar haiba, "idan Baki maida wannan bakinba yanzu zanyi maganinsa".
Da Sauri Aysha ta gyara bakinta, danta San sauran sarai.
Yad'auki jakkar laptop d'insa da wayoyi da hula zai fita, ya kalli Aysha "bazaki rakaniba?".
Da sauri tamik'e dantaji kunya, takar6i jakar suka fito, babu mai magana harsuka fito tsakar gidan, tom bani kayana ki koma ciki, su Adams najirana awaje.
Mik'a masa tayi, tanamasa addu'a. Saida ya kar6a sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshinta da la66anta.
Kunya yabata, tasaka hannunta tarufe fuskarta, kai Yaya, ko kunya bakaji?".
" Yaya ko?".
Da Sauri tamatsa bays o sorry sadauki, tayi maganar a shagwa6e".
Lallausan murmushi yasaki, sannan yajuya yatafi.
Saida yaje k'ofar gate dannan yajuyo ya kashe mata ido d'aya tareda d'aga mata hannu yafice gaba d'aya.
Dariya abin yabama Aysha, ta juya cikin gida tana mamakin ya khaleel da halayensa, yanzu takuma tabbatarwa ya khaleel murd'ad'd'en mutumne, Dan har yanzu yana nan yanda tasanshi, kwanakinta Tara kenan taredashi, amma kaf halayrnsa suna nan Tatare dashi, babu wani canji, wani lokacin kigansa mutum mai sauk'i, wani lokacin kuma amurd'e, dariya abuce mai tsada awajensa, hakama bashida yawan surutu, Alhmdllh tana samun kulawa bakin gwargwado daga wajensa, dukda har yanzu bai furta yana sontaba, bata damuba, aganinta watarana shima zai fad'ane, Abu mafi burgeta agareshi shine tsafta, ya khaleel akwai tsafta da gwalli tamkar mace, yamafi wata macen. Komai nasa k'al-k'al yake sonshi, shiyyasa tadage da bada himma wajen gyara kanta da muhallinsu, bata yarda tabar wata 6araka dazaiga gazawartaba, iya k'ok'arinta tanayi Dan ganin tak'ara daraja da kima a idonsa, halayensa kuma basu dametaba, insha ALLAH zata iya zama dashi a aduk yanda yake, kuma su zauna lfy.
Agurguje itama ta shirya driver yad'auketa zuwa Inda take aiiki.
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
ActionLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.