45
Zama yayi kujerar dake kallonta, momy barka da dare.
Adak'ile tace barka.
Shiru babu Wanda yasake cewa uffan, hajia babba sai cika takeyi tana batsewa, Dan jitake tamkar karta amince da shawarar hajia khaltume, amma kuma wani 6angare Na zuciyarta Na nunamata hakan shine dai-dai.
Ta saci kallon khaleel d'in Wanda idonsa ke kan TV, amma azahirin gaskiya yana nazarin momyne.....
Ibraheem!!.
Na'am momy! Ya amsa yana maido kallonsa akanta.
Na amince da aurenka, amma da sharad'i.
Shiru yayi yana saurarenta, gakuma maganar tata ta dakesa, Dan baiyi tunanin yardarta da wuri hakaba.
Amma momy miyasa kika amice? Miye kuma sharad'in?.
Karka damu da dalilin amincewata, wannan sirri nane, sharad'in kuma shine nangaba zaka auri Aleeya itama.
Wani guntun murmushi yayi, Wanda yafi kuka ciwo, ya kauda kai daga kallonta yana cije le6ensa Na k'asa, babu damuwa momy ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi.
Tsura masa idanu tayi cikeda mamakinsa, ko kad'an batayi zaton taurin kansa zai saka ya aminceba cikin sauk'i, anya kuwa bawani Abu yaronnan yake shiryawaba? Koda yake ance basu kama barau modibbo ba.
Yana kallon, kallon da momy kemasa da gefen idonsa, aransa yay k'aramar dariya, yana fad'in momy kenan, *'DAN HAKKIN DAKA RAINAFA....* shike tsone maka ido watarana.
Afili kuma yace momy kokinada damuwane?.
A'a Ibraheem babu komai, amma yanzu ina zaka zauna?.
Zan zauna inda gidana Na Asokoro.
A'a kazauna anan gidan, kaima indasu mujahedeen sukayi gini.
Miyasa momy? Kefa kikace bakiso Na zauna agidannan da matana idan nayi aure, miyasa kuma yanzu zaki canja?.
Haka kawai.
Ananma dariya yayi azuciyarsa, afili kuma yace shikenan momy duk yanda kikeso haka za'ayi to.
Farin cikine ya lullu6e kasan ranta, Dan ganin duk abinda tace baya mata musu.
Daga nan tasaki fuska sukad'an ta6a hira, cikin hikima irinnansu Na manya take sako masa tambayoyi akan aikinsa.
Amsa yake bata kai tsaye batareda tunanin miye manufartaba.
Itakam dad'i takeji yau tasami Ibraheem yanda takeso.___________________________
Washe gari girkin mama, bayan tagama had'ama baffah breakfast agabansa tace Alhaji su Aysha zasu koma gida zuwa jibe idan ALLAH ya kaimu, Dan fadeelah zata koma d'akinta mijinta NATA waya.
d'ago idanunsa yayi yana kallon mama, baice komaiba yacigaba dacin abincinsa, saida ya mammala tsaf sannan ya fuskanceta sosai, fad'ima fadila ce kawai zata koma, amma Aysha tazo kenan, Dan bilyamin yabani, ita kanta fadeelah badan aure takeba da babu inda zataje, akoda yaushe inaso ki gane sud'in y'ay'a nane koda banine mahaifinsuba, inajinsu azuciyata tamkar su Mu'azzam wlhy.
Yanzu haka zancennan danake miki angama komai akan bautar k'asar Aysha (NYSCE) insha ALLAH k'arshen watannan zata fara, anan kusadamu. Dan munyi sa'a abin yazo daidai daza'a d'auki sababbi.
Hawayene suka cika idonmama saikuma taji kunyar abinda tayi, cikin hikima tabama baffah hak'uri.
Murmushi yayi tareda jawota jikinsa ya rungume yana fad'in babu komai first love d'ina, Dan bakisan irin matsayin dakike dashiba azuciyar Abdallah bane shiyyasa kike Raba d'aya biyu, amma namiki uzuri, daga yau karki sake.
Dad'ine ya lullu6e mama, Dan itama tana k'aunar mijin NATA, tak'ara k'ank'ameshi da k'yau kamar mai gudun kar'a kwace matashi.🏃♀a 100 nafito, Dan lamarin yafi k'arfina, wannan fagen Na manyane😂 irinsu baffah😉.
_____________
Akwana atashi babu wuya wajen ubangiji, rayuwa tanata tafiya, yau kusan watanni uku kenan da saka bikin ya khaleel da Aysha.
Saidai babu mai shiga harkar wani shida Aysha, ita bautar k'asar datakeyi ya d'aukema hankalinta gaba d'aya.
Shikam yawon k'asashensa yahanashi zama waje d'ayama.
Yanzu haka yana Mexico kusan kwanaki 13 kenan, daga nanma France zai sauka a gaba d'aya headquarters d'insu dake Lyon city, sosai aiki ya d'auke hankalinsa a y'an kwankinnan, shiyyasama yakan manta dawata aba Aysha, dama ko number d'inta bashida ita, koyayi waya dasu mama kuma baita6a cewa abataba.
Ya gyara kwanciyarsa yana mai tunanin yanda rayuwar aure zata d'ore babu soyayyar juna.
K'aramin tsaki yayi, lokacin daya tuno rashin kunyar yarinyar, yatuna bakinnan nata maikama Dana tsuntsu dake masa murgud'e, kwafa yayi tareda fad'in zan kama kine aii afili.
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
AcciónLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.