2⃣4⃣
Assalamu alaikum 'yan mata.
Atare suka d'ago kai, cikin tsantsar mamaki suke kallonsa, Dan basu ta6a tunanin jin yarensu abakinsaba.
Ya d'age gira sama tareda fad'in Ku amsa mana.
Aysha Ce tayi k'arfin halin amsashi.
Amma meerah har yanzu baki bud'e take kallonsa.
Shimad'in hankalinsa Na kanta, yace zan iya zama?.
Yanzuma Aysha Ce tabashi amsa cikin gyad'a kanta.
Zama yayi bisa kujerar dake kallonsu, kuyi hak'uri idan natakura mukufa.
Sai sanan meerah tasami bakin magana, a'a babu takura, sai daifa.........
Kinyi mamakin jin nayi Hausa ko?.
Yak'arasa mata maganar cikin murmushi.
Kanta tagyad'a masa.
Yayi 'Yar dariyar basarwa tareda mik'a hannu yad'ebi popcorn d'in cinyar Aysha, yakai bakinsa yana fad'in dukda ba'amin tayiba kam.
Sorry uncle, Aysha tafad'a tana langa6e kai.
Murmushi yamata, thanks my lil sister.
Yamaida kallonsa wajen meerah.
Anty meerah koba'ayi maraba dani baneba?.
A'a, kayi hak'uri, mamakine kawai dai nakeyi.
Karkiyi mamaki akaina, sunan Naufal yahaya Zubair, d'an asalin k'asar Nigeria, amma haihuwar Canada, babana d'an Nigeria, Mamana 'Yar Canada, so nayi rayuwar Nigeria sosai shiyyasa na'iya Hausa, yanzu haka mom & dad, brothers-Sisters d'ina duk suna Canada, aikine Na wattani 6 yakawoni nan Georgetown.
Yak'are maganar da d'age gira sama.
Murmushi sukayi suduka.
Yace, "friends nawafa?".
Meerah tad'an murmusa, mukam labarin namu bashida tushen dazakayi sha'awar jinsa.
Ko? To shikenan, nabada uzuri, afad'amin suna.
Ameerah & Aysha.
Nice names drillings.
Hira sosai yake musu, harsuka saki jiki dashi, Dan Naufal yanada saurin sabo kam.
Shine yakaisu har gida, bayan uwar sayayya daya narka musu.
Anty glo...... Sai Murna take meerah tayo babban kamu.Nace hummm.
____________________________
Biki kam ya kankama, bak'i suncika gidansu Aysha, sai hidimomi akeyi.
Gida yagama d'inkewa kasancewar gobene d'aurin aure.
Washe gari wajen 10am babu zato saigasu Anty Mamie akano, hardasu inna 'yan jigawa.
Mama rasa wane irin farinciki zatayi tayi, saikawai tarungume Anty Mamie suka saka kuka atare.
Nanfa akaita lallashinsu daban magana.
Duk wani ainan ainan da aunty Mamie akaita yinsa.
Hakama Amal, Hamdiyya, Naseeba, Shuhuda sunshige cikinsu Fadeela amare anata abubuwan arzik'i dasu.
Gabda d'aurin aure gayyar matasan gidan suka iso, ya khaleel ne kawai babu, danyana kasar Algeria tun jiya.
Bayan an d'aura aure, Anty Mamie tace mama taje falon Abbansu Aysha ana kiranta.
Bata kawo komai arantaba tatashi tafita.
Sanye take da jar atanfa mai ratsin brown d'in zane, tamata matuk'ar kyau, kasancewar mama batada k'iba kuma batawani haihu da yawaba sai shekarunta suka 6uya sosai, tana nan k'yak'yk'yawarta fara tas.Da sallama tashiga falon, k'amshin turarensa yafara mata sallama, cikin dakiya tashiga, amma ganinsa saiya sakata fad'uwar gaba, (waimi Alhaji Abdallah keso da'itane?)
Idonsa akanta yace, "kiyi hak'uri fad'ima ki k'araso ciki".
Kamar zata juya saikuma tadawo tashiga, kobabu komai hidimarta yahalarta shida iyalansa. Baikamata ta wulak'antasaba.
Zama tayi kujerar dake nesa dashi, kanta ak'asa tace ina yini, anzo lfy.
Murmushi yayi, haryanzu Fad'imarsa Na nan bata sauyaba, mace mai zafi da sauk'inkai.
Ya amsa mata gaisuwa tareda murnar aurensu fadeelah, yad'ora damata gaisuwar mijinsu.
Daganan shiru yabiyo baya.
Ganin haka mama tamik'e tana fad'in mungodefa, ALLAH ya maidaku gida lfy.
Da sauri yakatseta, sorry inaso muyi magana.
Komawa tayi tazauna, saidai yanayinta yacanja kam.
Ganin haka shima saiyaci serious.
Fad'ima nasan haryanzu abinda yafaru abaya yanasaki jin haushina, amma ina so kigane cewa k'addarace da rabon haihuwar wad'annan 'ya'yan, wani baya haihuwar d'an wani, ALLAH ya rubuto saikinzo kin haifesu anan, amma inaso kisan haryanzu kina cikin ruhin Abdallah Rufa'ee. Muba yara baneba, baikamata muzauna zancen yaraba, ina rok'onki arzik'i kidawo d'akinki, amatsayin matata, kenafaso aduniya, kuma har yanzu inasonki.
Bak'aramar razana maganarshi tasaka mamaba, muryarta narawa tace anya kasan mikake fad'a kuwa?.
Nasani fad'ima, yardarki kawai nake buk'ata, wlhy inhar kin amince ayau d'inan za'a maida aurenmu.
Zumbur mama tamik'e, cikin fusata tace, ban aminceba, bakuma zanta6a amincewarba, wanan maganar tatsaya iya ni da kai, Dan banaso takawo 6acinran mutane dayawa.
Tana gama fad'a tafice daga falon.
Baffah yadafe kansa dake sara masa, ahankali yafurta fad'ima ki canja mana, wlhy dolene ki amince da buk'atata koda yardarki ko babu.
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
AcciónLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.