88
Monday morning
KOTUA yau ranar litinin 8/9 aka shiga shari'arsu momy, abbabban kotun k'asa da k'asa ta Abuja.
Anyi zammne misalin 10am, tareda lauyoyi masu kare gwamnati dakuma lauya mai kare 'yan ta'addar wannan k'ungiya.
Bayan Alk'ali ya saurari k'arar dakuma jawabai abakin lauyoyin guda biyu.
Am fafata sosai, amma ba a yanke hukuncinba, sai azama Na gaba insha ALLAH.Ran khaleel yad'an 6aci, soyayi ayita kawai yau ta k'are, amma babu komai, ALLAH ya kaimu randa alk'alin yasaka.
Aysha Na zaune afalo zama da k'yar tashi da dabara, dukda cikin nata bawani uban girma yayiba, kunsan cikin fari dama bakowanne keyin k'atoba.
Sallamar ya khaleel yasakata d'ago ido ta kalleshi.
Cikin murmushi tace, "sannu da zuwa sadauki na, yau da wuri haka?".
Kusada ita ya zauna yana murmushin shima, yadurk'uso ya sumbaci cikinta, " babies na inafata kuna cikin k'oshin lfy? Injidai maah-maah tabaku abinci?".
"Tab abinma dariya, ALLAH Sadauki idan kana wannan abun dariya kake bani, waya gayamaka yara biyune to?."
Matsawa yayi sosai, ya mannata da jikinsa, acikin kunne yarad'a mata abinda nima banjiba.
Aysha ta tureshi tana fad'i ''kai kai ALLAH nidai babu ruwana, saima Na fad'aka da Ammah".
"Hhh dubeta kamarma zata iya".
" OK haka kake zaton bazan iyaba ko? Kajira sammaci". 'Tayi maganar tana komawa k'asa'.
K'afarsa takamo tafara k'ok'arin cire masa takalman.
Shikuma yana fad'in "kibari kawai, kinma tunamin wlhy, wai shegen alk'alinnan dukda hujjoji da lauyanmu yabayar yad'aga zaman kotun nan harsai next week".
" to aii babu komai sadauki, dayau da wani satin duk d'ayane, insha ALLAH za'a yanke musu hukunci dai-dai dasu, wahalarmu bazata tafi abanzaba aii, mugodema ALLAH ma da nasarorin daya bamu duk aka kamasu".
"Hakane kuma sholyna, su john ma k'asarsu hukuncin kisa ta yanke musu".
" woow! Dan ALLAH da gaske sadauki!?".
"Wlhy kuwa my luv"
" kai alhmdllh, amma naji dad'i sosai wlhy, nasan Anty meerah saitafi kowa farinciki dahakan, tsinanne, dama dukmasu hali irinnasa k'arshensu kenan, sugama tara dukiyar kuma daga k'arshe tazama mara amfani agaresu, saidai wasu suci kuma".
"Hakane wlhy sholyna, gadai su momy nan inda suka k'are, ita wannan ciwonma data tsinci kanta kad'ai ya isheta, munyi magana da Anty zuwairah akan dukkan kud'ad'e da kaddarorin momyn, kawai zamu kaisu gidan marayu, danbanga amfaninsuba, baffah yace babu Wanda zaiyi amfani dasu agidannan".
''Hakan shine dai-dai aii sadauki, to Amma su Lola fa? naga suma sakasu akayi bashiga sukayiba".
" eh, hakane, amma kinsan mutanenmu da bushewar zuciya, dukda sunga an hukunta wad'annan bazaisasu dainaba suma, sunrigada sun saba da iskancin, dakuma kama kud'ad'e masu nauyi, yanzu koda an sakesu suma tasu dabar zasuje su kafa. Amma dai munan muna tattaunawa akansu, sauran yaran kuma duk mun maidasu hannun iyayensu".
"Aii kunyi dai-dai wlhy, jaridun k'asarnan gaba d'aya wannan satin labarinkune kawai aciki, nasan gaba d'aya idanun al'ummar Nigeria Na kanku yanzu, kai duniyama baki d'aya, jira kawai akeyi aji irin hukuncin daza'a yankema wannan k'ungiya".
"Hakane wlhy, yanzufa da k'yar Na kufto daga hannun 'yan jarida, Taheer nabar musu nagudo, saiya bar wajen yayta tsinemin azuciya d'an iskan".
Dariya Aisha tayi, tace, " aiini wlhy birgeni kukeyi, yanda kuke tafiya da rayuwarku a tsari, idan fannin aiki kuke komai cikin girmamawa suke makashi, basa kallon kaid'in abokinsune, hakama idan aka dawo fannin abota kashige cikinsu kuyita barkwanci, baka kallon kai ogansune awajan aiki, lamarinku daban dana sauran jama'a sadaukina."
"To miye duniyar Sholyna, watarana komai saikiga yazama tarihi, saidai atuna sunanmu badai mud'inba, su Youseef mutanene masu kwazo, kinga tunda nabasu shawarar mukafa k'ungiya taimakon matasa babu musu suka amincemin, yanzu haka nake fad'a miki mun samama matasa kusan 200 aiki wlhy, banda wad'anda muka samama sana'oi, dakuma wad'anda suka koma makaranta, aikinga wannan nasarace, watarana basaikiji sunkai irin dubu biyar d'innanba, inaga hakane yakamata masu kud'in k'asarmu sunayi, musamman ma 'yan arewa dan mutanan kudancin k'asarnan tuni sun waye da irin wad'annan taimakon, amma 'yan arewa ina, kowa burinshi akirashi wane, zakiga kowanne banki mutum yanada kud'i, gawasu agida, motocin hawa Na alfarma, saka manyan kaya masu tsada, agogo wannan saikiji Na million d'aya ahannunsa, 'ya'yansa kowanne yanada account nakansa, ga hannun jari a ma'aikatu daban-daban, shin dukmi zakayi dasu?, kasan dai baza'a gina rami arufeka dasuba ko?, kiga mutum yak'are rayuwarsa kaf aneman dukiya, babu kwakwkwarar ibadar dazai rik'e tazame masa guzurin shiga kabari, wlhy kaiconmu dawannan makauniyar rayuwa, bazakasan kana cikin babbar asaraba sai mala'ikin mutuwa yazo kanka, lokacin babu tsumi babu dabara kuma?".
"Wlhy hakane Sadauki, ai gaskiyafa 'yan arewa muna cikin halin hau, kowa dagashi sai 'ya'yansa, shiyyasa kullum kuma mune abaya, masu k'aunarmu da gaskiya dason dawomana da martabarmu irinsu BUHARI kuma toshewar basira tahanamu ganewa, munfison awatsa mana tsaba mu tsatstsage alokacin, batareda munyi tanadi wa gobenmuba, inhar za'a cigaba da tafiya haka aii wataran sai'an shafe tarihin arewa da al'ummar cikinta, shiyyasa nake tausayin 'ya'yanmu wlhy".
" dolene subaka tausayi, ayanzuma jibi yanda duniya take walagigi, inaga nanda shekaru 20 masu zuwa, ALLAH ka gafarta mana dai kawai."
"Ameen to". 'Aysha tafad'a tana yunk'urawa zata tamik'e'.
Saida ya taimaka mata sannan tasamu tatashi.
"Sannu sholyna kinji, insha ALLAH saura kad'andai ki juyomin babies d'ina ki huta muma mu huta".
"ALLAH ya kaimu, dama nagaji nikam, tashige kichin".
Shima mik'ewa yayi yana dariya dafad'in ''k'ya gaya musu yarinya, kina juyewa zankuma ajiye wani aii".😂😜
YOU ARE READING
CIKI DA GASKIYA......!!
AkcjaLabari mai taɓa zuciya, cakwakiya, darajar ɗiya mace, cin amanar ƙasa, kishi, makirci, soyayya.