14

4.1K 289 0
                                    

1⃣4⃣

      Shiru kakeji kowa yanatsu afalon Ammah yana jiran labari,  Aysha & bishirama suna ala6e tacan baya, dansunji lokacin da Ammah tace da daddare zata fad'amasu Naseeba tarihin ya khaleel, sukam suna buk'atar ji.
    Saida Ammah tagama dama fura kowa yad'iba sannan tafara bada bayani kamar haka.
                       👇🏻

      to dafarkodai kunsan mahaifinku da sana'arsa, Laure dai itace matarsa ta lalle ta farko kenan, da mahaifiyar Laure dani uwarmu d'aya ubanmu d'aya, ninasha nono nabata. alokacinda mahaifinku Abdullahi yafara samun kud'i sai kakanku Malam Rufa'ee yamatsa masa akan yayi aure, nayi biris dasu kasancewar shine d'ana nafari, bansaka musu bakiba har tsawon shekara 1, nima rashin aurensa Na damuna.
   Ninakawo shawarar ahad'a Abdullahi aure da Laure d'iyar k'anwata, kasancewar nasan tana sonsa amma yak'i bata fuska.
   Badan Abdullahi yasoba akayi aurensa da Laure, watanta Tara da kwanaki 17 agidansa tahaifi d'iyarta mace wadda taci suna Zuwairah, bayan haihuwar Zuwairah da shekara d'aya Abdullahi yace zai k'ara aure, yasamu wadda yakeso anan cikin garin Kano.
       Naso nahanashi amma kakanku yahana, yace nabarsa tunda ALLAH ya halatta masa.
      Ansha bikin Abdullahi da Fad'ima, yarinyar kirki, saidai bak'aramin tashin hankali Abdullahi yafuskanta awajen Laureba, sosai tatada hankalin kowa. Kokad'an Fad'ima batajin dad'in zama da Laure, ana haka ALLAH yayima kakanku rasuwa, Rasuwar tata6a Abdullahi sosai shida d'an uwansa Ma'aruff dukda alokacin yana makaranta.
         Bayan Rasuwar kakanku Abdullahi yadawo damu Abuja da zama, saboda kasuwancinsa yadawo nan.
         Dawowarmu da shekara 2 Laura takuma haihuwar mace aka sakamata Shukrah, alokacin kuma Fad'ima tayi 6ari itama.
         Alokacinne Babanku yak'ara aure ya auro Bilkeesu, tashin hanakali yakuma k'aruwa agidan, sosai Laure Tahana kowa zaman lafiya.
     Bawani Abu ne kuma Kecin zuciyartaba illah haihuwar mata datakeyi, ita a haukanta kishiyoyinta zasuzo su haifi maza su kwace gida, bayan tun Abdullahi Na talakansa ta aura.
     Batasan ba'ayima ALLAH wayauba.
   Tsakanin Fad'ima da Bilkeesu babu wata Matsala kam, zamansu lafiya kamarma ba kishiyoyiba, hakane kuma ke k'ara hasala zuciyar Laurah
          Bayan shekaru uku suka kuma samun cikin suduka uku, saida cikkunansu suna kai watanni 5 Fad'ima tayi 6ari Wanda yabama kowa mamaki, amma saboda hak'urinta tace haka ALLAH ya k'addara.
         Bayan wata biyu da 6arin Fad'ima itama Bilkeesu tayita zubar da jini, da'akaje asibiti sai akace maganin zubda cikin akabata tasha aruwa, amma cikin ikon ALLAH cikin bai fad'iba.
     Alokacin hankalin babanku yatashi. yatsare Matan NASA yana bincikarsu, kowacce tashiga kare kanta, ganin abin zai kawomusu 6acin rai nace yabarsu nizan bimko komai dakaina.
         Rana d'aya ALLAH yakawoma Bilkeesu da Laure haihuwa, amma laurece tafara nak'uda.
    Laure tahaihu amma k'awarta kaltume tak'i sanar damu abinda ta Haifa, sai yawo da hankali suke mana.
       saboda Bilkeesu tana cikin tsaka mai wuya har ana shirin yimata theater, shiyyasa bamu damuba, tunda dai Lauren tahaihu lfy.
    Dr yajanye mahaifinku danya saka hannu a yima bilkeesu aiiki, nikad'ai aka bari ak'ofar d'akin da Bilkeesu take nak'uda, Fad'ima kuma taje siyo ruwa za'a sakamata. Ina nan tsaye saiga Nurse d'in dake kula da Bilkeesu tafito tace tahaihu mace, amma yarinyar batazo da raiba.
          Munji babu dad'i nida mahaifinku, amma Bilkeesu nata tausarmu akan muyi hak'uri.
     Alokacinne kuma mukaji Laure tahaifi d'a namiji, babanku yayi murna dahakan.

    Saidai wata sabuwa kuma, tunda muka dawo yaron Laure yak'ishan nononta, daga baya da'aka bincika sai akaga nonon nafita yellow ne, anbashi madara yak'isha, gashi yanata tsanyara kuka, yatada hankalin kowa, ganin halinda jariri yake aciki nace akawosa Bilkeesu tagwada bashi nono, Laure tayi tsalle tadire tace bata aminceba, saida namata biji-biji sannan tabari Bilkeesu tabama jariri nono, abin mamaki anabasa yakar6a kuwa, abin yabama kowa mamaki da al'ajabi, amma bamu kawo komai aranmuba.
        Hummm wata badak'ala kuma babanku yayma jariri hud'uba da sunan mahaifin Bilkeesu, wato Ibraheem khaleel, babu Wanda yasani sai ranar suna.
   Bak'aramin rikici akayi da Laure ba, amma mahaifinku yace bata isaba, haka yakeson sunan d'ansa kuma babu mai canja masa.
        Daga nan Bilkeesu tacigaba da shayar da Ibraheem, watan Ibraheem uku babanku yasaki Fad'ima saboda maganin zubar da ciki daya gani ad'akinta, wai shitakesha tana zubar da cikinta, itacema tabama Bilkeesu alokacin data zubar dajini.
    Harga ALLAH banyardaba alokacin, dayayi shawara danikuma bazai saki Fad'ima ba. Bilkeesu ma tasha kuka sosai dantanason Fad'ima, hakadai Fad'ima tatafi muna kewarta saboda mutuniyar kirkice.
         Shekarar Ibraheem 1 Bilkeesu tasamu ciki, itama ALLAH ya azurtata da haihuwar namiji shine marigayi rufa'ee 
          K'iyayyar Bilkeesu takuma k'aruwa ga laurah, tatsaneta sosai, wani abumma tana tsoron aikatashine sabodani agidan.
    Tundaga haihuwar Ibraheem kuma Laure bata sake haihuwaba har Bilkeesu tayi haihuwa biyar.
   *Rufa'ee, Sultan, mujahedeen, Amatullah, Ramadan, Zunnurain*.
     Saikuma suka haifi Hameeda da Musleem atare, daganan Bilkeesu takuma haihuwar Muhseen, itakuma 'yan biyu, Hasnah & Husnah.
    Alokacinne kuma babanku ya auro Saude, itamadai tanada nata mugun halin, amma tafi Laure, Laure taso suhad'ema Bilkeesu kai itada saude amma sauden tak'i amincewa.
    Saude tahaihu tahaifi Hafeez,
    Daganan suka haihu tare itada Bilkeesu kuma, Bilkeesu Amaliyya, saude Shuhuda, suka k'ara Tasleem da Maleekah, suka k'ara Ummunoor da Nureeden, daganan kuma haihuwar taimusu adabo.

Ibraheem yatashi yaro marason hayaniya, yanason 'yan uwansa, akwai hak'uri da zuciya idan kakai hak'urinsa k'arshe, tun yana primary yarone me shegen naci dabin kwankwanto akan Abu, yana son kallon film na bincike, lokacin daya shiga secondary dole aka sakamasa TV ad'akinsa, saboda son kallon film Na bincike-bincike, akwai wata basira da ALLAH yayma yaron. Inhar za'ayi laifi agidannan arasakuma Wanda ya aikata, inhar yaji kuma, tofa saiya gano mai laifin acikin bincikensa, wannan tunanin yasaka mahaifinku barinsa shiga d'an sanda, Dan acewarsa irinsu Ibraheem ake buk'ata a police saboda iya bincike da naci.
      Ibraheem yasamu nasarar shiga d'ansanda cikin sauk'i saboda yanayin k'irarsa, dogon mutumne tsayayye, ALLAH yabashi suffar k'arfi irinta masu d'amara, gashida kwakwalwa da jajircewar aiki, daganan yasamu k'arin daraja zuwa hukumar 'yan sanda ta duniya, kukuka San sunanta da turancinku😑.
    Dariya su Hamdiyya suka kwashe dashi saboda furicin Ammah Na k'arshe.
    Sukace Ammah sunanta Police Interpol (NIS).
    Oho kudai kukasani nidai nagama nawa.

_______________________

*_Ibraheem Abdallah Rufa'ee jigawa shine sunan jarumin namu, mahaifinsa nakiransa da suna mu'azzam saboda sunan mahaifin aunty Mamie gareshi, aunty Mamie tana kiransa babanta, hajia babba tana kiransa Ibraheem saboda tabak'anta zuciyar aunty Mamie, (Dan sunan mahaifi bawasaba). Awajen aiki suna kiransa J! Saboda tak'aitawa. J kyakykyawan Namijime dogo, wankan tarwad'ane, yanada cikar zati irinta zaratan maza, a6angaren k'yau kam masha ALLAH, komai najikinsa yadace da halittarsa, kokad'an bayason raini, kuma mutumne ma'abocin tsare gida, bazaka ta6a ganinsa cikin dariyaba, murmushima saiya gadama yayinsa, wannan yasa mutane suke ganin yadace da aikinsa Na d'ansanda._*
    *_idan tsautsayi yasa kafad'a tarkon j kagama shiga uku, zaiyi amfani da basirarsa ya cafkoka, wannan yasa yasamu d'aukaka fiye da sauran 'yan uwansa awajen aiki, j baya shaye-shaye, baya Neman mata, bazaka ta6a ganimsa awajen wani ashararanciba, mutumne kamilalle ma'abocin bin dokokin ubangiji, yanada ilimin addini dana zamani Alhmdllh._*
     _yadad'e yana bibiyar Oga David, kusan wata uku, awannan lokacinma  tundaga k'asar Japan, yabiyo sahunsa, yasamu damar kamashine kuma tadalilin tatsar bayanai ga wani yaron Oga David dasuka kama, khaleel yanashan shiga aiki mai had'arin gaske ALLAH ne kawai ke ku6utar dashi, yana samun taimako daga abokansa taheer, Yousuf, Joseph, saidai shi ogansune awajen aiki._
    *tuntuni aketa fama dashi yayi aure amma yak'i, saiyace akwai lokacin, koya la6e akan aiki yamasa yawa, bakuma 'yanmatan yarasaba, a'a bashida ra'ayin aurenne kawai, Dan ya khaleel akwai farinjini, turawan da bak'ar fatar ko ina 'yanmata binsa suke da Nuna masa tsantsar soyaya, amma kokad'an baya basu fuska, yafison auren yarinyar d'anya, saidai bansan dalilinsaba nikam, to komadai miye baffa dai yana d'aga masa k'afane kafin yamasa sambad'e-bad'e. Yanzu yanada shekaru 32 yanacikin ta 33 da haihuwa. gakuma k'anne cikeda gida.*
     Wannan shine j 👌🏼...........🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now