*⚜️BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*⚜️
{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}
*🌷WAYE SILAR*
*LALACEWATA??*🌹A very painful story....💔
Story and written by Fati-teejay
IG _fati _teejay _www.fatimatijjani121@gmail.com
Wattpad-FatimaTijjani030
D whole book is dedicated to my love SIYAMAH IBRAHIM❤️...
Alhamdulillah jiki yayi kyau sosai sai godiyan Allah.... Inagodiya sosai da yadda kuke nuna kaunarku gareni....nagode kwarai kwarai....Allah yahadamu a aljannarsa...🥰
66-70
Da isarta waje ta tadda ankawomata wata mahaukaciyar mota daga gurin alajinta...motanda ya amsa sunansa mota yakuma taka ta aisha...dukda ranta abace yake hakan baihanata farinciki sosaiba...itakam bariki tagama mata komai...saida tagama farincikinta ta sallame wadanda suka kawo sannan tanufi honourable wanda yaketa zare idanu datunanin inda zata da uban akwatuna....
Bayan sungaisane takoromasa bayanin halinda akeciki..sam abin baimasa dadiba gashi baisan dije takoma danshidai tunda yahaduda ita bukatarsa sosai takebiyamasa...ta iya barikanci ta iya duk wani abu dazasu saka mance waye kai..kowayene namiji komin matsayinka dole inkaje gabanta karususna dan itadai tafi gaban wasa......
Jintana jan majina alamar kukane honourable din yayi hanzarin jawota jikinsa yadunga sarrafata harsaida jikinta yamutu murus sannan yakefadamata shifa dama tasan a abuja yake...yanadai zuwa nanne idan bukatar hakan tataso...gabadaya yarikice jinyanda takafe kaida fata itafa babu abinda zaihanata kwanan gidansu yau......dakyar dasudin goshi irinnasu na en bariki sannan yasamu tayarda zatabishi abujan.....hakadai suka lallaba suka tafi hotel donkwana acan goben saisu tafi....bayan ya ajiyeta yaje yaimusu booking flight sannan yadawo suka cigabada sheke ayarsu....tuni tamanta dawani zancen kauyensu jinzata inda bata taba zuwaba wato abuja.....
Dukwanda yakalli iyayenta saisunbashi tausayi bamadai kamr mallam din...don ita uwarta kowa yafita hanyarta duk inda taje zaginta akeyi anafadin ta sallamawa duniya yarinyarda tahaifa dacikinta.....tun abun baidamunta haryazamanto shidaya takkk yatarwatsa duk wani kofofin farincikinta...sam yanzu bata fita donwasuma tsabar tsiya randa tafita dayake cikin duhune jifanta sukahauyi sunafadin uwar sallamamma....itakadai tadan halinda takeciki..gawasu mafarkanda takeyi bila adadin akan dijen...waitana gudu wasu kattai nabinta tana kiran innaaaa...koshikadai akabarta dashi tasan zata shiga wani halin barega tsangwamar mutanen layi..gana mijinta dayanzu jikinsa kam Alhamdulillah donyama fara iya mikewa sai dai tafiyarce bai iyayi sai an taimaka antayashi.....sam yanzu basira bata gabansa duk wani gidan sadarwa yasanya abokansa zuwa tunda shi baida isasshen lafiya amma inaaa amsar dayace babu dije cikin kauyennan don inda tananan bazatayi wahalen nemaba cikin dankaramin kauyenda baifi gida gomane cikiba.......
Washegari kam babu bata lokaci su dije sukaje airport aka gama komai sannan suka wulla sama donzuwa abuja sosai jikinta yake kyarma ganinta asama tanayawo wani irin tsorone yamamayeta tundaga sanda jirgin yayi kwana yalula sama saitakejin kamr inyaje zai fado kasane dakarfi duksu mutu dakyardai yakwantarmata da hankali yana jawota jikinsa ....koh acikin jirginma honourable dinbaibartsba sai lalubarta yakeyi kamr tsohon kwarto gashi shima da iya barikanci donyalalubota tahanashi saiwani kama fuskanrnan yashagwabeta kamr yaronda uwarsa tayayesa bata fadamasaba....ahakadai tafiya tayi tafiya cikin mintunanda basu haura ashirunba sukayi landing a nnamdi azikwe airport dakecan jahar abujan..ahankali jama'a suka fara fita daga cikin jirgin harsu dije dakecan last seat suka fito... gam tarufe ido tareda sakin wani irin sassanyar numfashi t jinta shaki iskan abuja...garinda kohh amafarki bata taba tunanin zuwaba yagata cikinshi kuma jirgima tahau tsabar dadi itakam aibariki taimata rana kuma koyanzu kasuwa ta tashi tabbas dankoli yayi ciniki...........
DIJE A ABUJA......
*KALU BALE GAREKU IYAYE*
*Fati-teejay*💓
#Covid 19 is real
#Take responsibility
#Stayhome
#Staysafe
YOU ARE READING
WAYE SILAR LALACEWATA????
Historical FictionIt signifies how some parents behave towards their children and how it lead them to danger..