part 4

101 10 0
                                    

    *NIGERIA KO NIGER...?*
         (wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

                 page 4

HAFSAT da halimatussadiya sunsamu ciki a lokaci daya ...  wayyo farin ciki idan kaga fuskokin makiya alokacin sai kasha mmk wasun kumaa kishi ne ke dawayniya dasu bawai basaso su haihun bane...

bama kamar cikin hafsat da akifi daukinsa kasancewar shine nafarko a gareta bayan ta shafe shekaru goma sha biyar da aure...

laulayi mai zafi halimatu ke fama dashi sosai ba kadan ba... ahaka sukayi ta rainon cikinsu wanda ba'asan wacce zata riga wata samun kanta ba...

wata safiyar ranar litinin halimatu ta tashi da tsananin nakuda wanda take shan wahala amma haihuwar baizo ba gashi kuma a gida suke ba'akaita asibiti ba...

hafsat bata da labari itama tana fama da kanta sbd yau ta tashi da ciwon mara amma babu wanda yasani...

irin kuskus dinda akeyi ne acikin gidan kasancewar duk suna gidan sarautar dazama a tsakanin bayi da yan aykin gida taji halinda yayarta take ciki...

tashin hankali kenan a kidime tawuce part na yar uwarta inda ta tarda farida ce ke kokarin karbar haihuwar kasancewarta likita ce mai zaman kanta amma bata ayki sbd kalan gidan datake rayuwar aurenta...

ganin halinda ta tarar da yar uwarta yasa cikin wani uban murdawa inda tazube a sume a wajen...

tashin hankali kenan bashiri aka kwashi hafsat da halima zuwa asibiti domin basu taimakon gaggawa tun a hanyarsu ta tafiya hafsat ta farfado sanadiyyar ruwanda farida ta shafa mata a fuska...

nakuda itama ta taso mata gadan gadan amma abin yaci tura ana isa asibiti aka wuce dasu dakin da aka ware musamman domin tun suna gida aka kirasu akan ana zuwa da matar sarki da yar uwarta...

farida ce akan hafsat tare da wata likita saikuma wasu likitoci mata guda biyu akan halimatu......

cikin mintuna 20 halimatu tasauka kuma alokacin hafsat ma ta suburbudo da yan matanta guda biyu...
ita kuma halima yar daya ta haifa...

inda take halima jini ya tsinke mata atake a wajen bata kara cikakken minti goma mai kowa mai komai wanda yafimu sonta ya dauke ta a fadin duniya mai cike da abubuwa na ban mmk...

hafsat bata gama dawowa seti ba taji shigowar shehu abdul tare da mohammad sun shigo suna mai maita kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un...

bata gama sani mai akewa salati haka ba taji ance ay yarinya ma takoma...

anan ne ta fuskanci abinda yafaru wai yayarta ce tarasu wacce suke uwa daya uba wacce bata da tamkarta a fadin duniya...

gawar halima shehu ya hade ya rungume wasu hawaye masu zafi suke zuba daga kuncinsa na radadin rashin mata ta gari wacce samun kalansu sai an tona acikin dari a samu masu kalan halinta guda biyar...!

kamar ba sarki ba haka ya kwakumeta ya gagata motsi ji yake kamar zata bude idanunta ko kuma yaji hannunta bisa kuncinsa tana share masa hawayensa tana fadin kuka bai kamace fuskarka ba jarumin miji na ... wanda hakan tamasa alokacin mutawar zainabu...

hafsat kam tazama speachless a wajen domin kanta ya dau zafi ko kallon inda yemmatanta suke batayi ba...

tambayar kanta take wai shi dagaske ne abinda takeji ake fada yanxu yar uwarta ta tafi kenan har abada bazata sake ganinta ba sai a darussalam...?

innalillahi wa innailaihir raji'un kawai take ambata daga nan kuma bata sake sanin abinda ya kara faruwa ba...

sai bayan awa takwas wanda zuwa wannan lokacin halimatu na gidanta na gaskiya tare da yarinyarta mai kama da ita...wayyo mutuwa mai yankan kauna allah yajikan yan uwa musulmai na fadin duniya baki daya a duk inda suke ameen...

kowa mutuwar tashiga jikinsa inda jinjiraye suke tare da farida tana kula dasu kamin farfadowar uwarsu tabasu abincinsu...

mariama kam ta tausaya ma hafsat wannan lokacin sbd tasan mutuwa bata bar kan kowa ba......

yaronta musa da hafsat sai shehu sune abin jimami alakacin sun fita a hayyacinsu baki daya sun zama abin tausayi sosai ba kadan ba...

ahaka akayi zaman uku wanda daga masarautu dama yan gomnati sun halarci wajen ta'aziyar margayiya halimatu.........

kuma har zuwa lokacin bata saka yaran a cikin idanunta ba tana fama da kanta farida kuma ke kula dasu da duk abubuwan daya kamata tabasu sbd karsu zauna da yunwa...

da dare wajen karfe goma ga tsohon shehu wato mahaifin su muhammad,shehu abdul rahman,muhammad,hafsat,farida dakuma maa wato asma'u...

inda suke wani takaddama amma ga dukkan alamu hafsat na tsanani farin ciki ganin yadda fuskarta ta washe daga damuwa zuwa tsantsar farin ciki...

Aliyu dayazo shiga part na kakansa jin abinda ake fada yasa shi labewa shima tsaf yaji abinda ake fada wanda bazai taba mantawa dashi ba tsawon rayuwarsa...

sadaf sadaf ya fece abinsa kamar babu abinda yaji...

washe gari dasafe ma akayi ta karban masu zuwa ta aziya itakam tasamu kyakkyawar sheda wanda akewa duk wani musulmi na kwarai fatar hakan......

ranar sadakan bakwai aliyu dalhat dakansa ya radawa yan biyu suna hassana taci suna HALIMATUSSADIYYA saikuma hussaina taci suna ASMA'UL HUSNAH……

Akoi banbancin kamanceceniyar halitta kwarai da gaske a tare dasu sbd kou kadan basa kama itama halimatu photocopy na mai sunar ce...itakuma husnah hafsat ta dauko sosai harma kuma kyawunta ya zarce na hafsat din dakomai da komai...

musa kam tunda yaga mai kama da mamarsa kuma mai sunarta har hanawa yake a dauke ta saidai shine zai riketa ko nono za abata sai anyi dagaske...

mariama tunda ta kyalla ido taga tsantsar kyawun da bata taba gani ba a wajen husna taji sam ta tsani yarinyar ga kuma wani kishin yar da ya shigeta farat daya  (kunjimin mata pha jama'a kishi da yar mijinki)...

yanda take son yaranta nan amma taga sun rabi inda hafsat da yayanta suke har dukansu takeyi kan miyasa zasuje wajenta...?

dan haka inoussa yashama kansa lfy yadaina zuwa amma aliyu kam satan hanya yakeyi ya tafiyarsa...

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now