part 19

63 5 1
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌏©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌏*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

    
        *page 19*

A kwana a tashi asarar mai rai inji hausawa,wanda hakan kuwa gaskiya ne,domin kuwa a yau su husna suka tashi da murnar kammaluwar karatunsu a k'asar da ba tasu ba,wacce suka shafe a k'alla shekaru uku!

t'sawon wannan watannin daya gabata idan kuka ga su husna bazaku gane su ba,sbd yadda karatu yayu matuk'ar sasu gaba,kasancewar shekarar su ta k'arshe ce,kunsan ance dama idan aski yazo gaban goshi yafi zafi...! wanda kuwa hakan take ga husna y'ar gidan momma!

karatu suka sha babu kama hannun yaro irin na fitar hankali d'innan dikdan kawai su samu sakamako mai kyau dayafi na kowa !

wanda wani zubin idan karatu yayi karatu husna kan dakatawa ne da karatun ta k'ira momma tasa mata kuka kamar k'aramar yarinya wai ita tagaji da karatun,momma tayi ta d'aga hankalinta idan taji kukan y'ar lelen nata,gashi kuma babu yadda ta iya saidae tayi ta lallab'ata! wanda hakan yasa karatun nata dana deeya da banbanci sosai yanxu!

sukan gaysa da sauran y'an gidan nasu lokaci zuwa lokaci akanji lafiyarsu,wanda ya aliyu ma cikin watannin nan yakawo masu ziyara takanas ta kano a bisa ta umarnin baa!

gefe d'aya kuma ga saurayin husna na b'oye da yanxu soyayyar tasu tayi nisa sosaiii babu kama hannun yaro kasancewar bataji wannan bad'akalar da baa ya yanke ba har yanxu,tinda basu da labari koda wasa babu wanda ya fad'a masu...! wanda yanxu har waya yana kiranta suna shan love nasu kamar su kad'an ne a fad'in duniyar soyayya haka nan sukeji,saidae har yanxu batasan ya kalar halittar abin k'aunar nata yake ba...! fari ne...? bak'i ne...? dogo ne...? gajere ne...? kyakkyawa ne...? mummuni ne...? dik batasan komai akai ba,amma kuma dikda haka ita wannan bai dameta ba koda kuwa ace kuturu ne idan tagansa zataci gaba da sonsa har k'arshen numfashinta...!

su oga inoussa ma ana nan ana fafata soyewa da muradin zuciyarsa wato fad'imatou,zumud'i yaci k'aniyan na da,dikdama dae bai cika samun lokacin mutuniyar tasa ba a yanxu sbd jarabawar dasuka saka a gaba lokacin!

deeya ma anata fafatawa da yarima musa abinta kamar zasu lashe junansu..!

sannan kuma zuwa yanxu husna da fad'imatou ko daga nisa suka hango juna saidae su sakarma junansu harara,wanda hakan kuma yasamo asali ne a tun farkon fara ganin junansu,wanda kuma tun daga wannan ranar sai yazamana kusan kullum idan sun tashi fita makaranta sai sun had'a idanuwa...!

sunyi exam sun kammala lafiya inda aka had'a masu gagarumar party tare da dik malamansu dakuma danginsu da suka kawo masu ziyara,gida nigeria momma,sadam dakuma anty farida ne sukazo tare da baa...!

saikuma amni da itama tazo amma badan su husna ba saidan y'ar gidan yayanta almustapha wato fad'imatou tare da tasu tawagar ta y'an birnin agadez suma sukayi zugarsu...!

abu kam ya k'awatar k'warai da gaske,su husna ansamu kyaututtuka na ban girma daga malamansu hatta iyayensu da y'an uwansu...! kuma an dank'a ma kowa sakamakonsa wanda idan sukabar k'asar sun barta kenan idan ba suna son dawowa su ci gaba da karatu ba ko kuma wani yawonsu da dai sauransu...!

washe gari jirgin y'an nigeria ya d'aga suma y'an niger jirginsu na masarauta ya d'aga aka rabu cike da kewar juna...!

major general aliyu muhammad bama tare da d'an uwansa captain inoussa aliyu muhammad bama aiki yasha masu kai k'warai a t'sakankanin wannan lokacin,wanda haka yasa ba'a tafi dasu ba wajen taya y'an uwan nasu murna...!

ranar da su husna suka iso kowa ka gani cikin gidan yana farin ciki da dawowarsu,bama kamar su zainab da ilham kamar suyi yaya dan murna kasancewar ilham ma y'anzu an zama y'an mata tinda takai 7yrs...!

******** Kowa ka gani a dae dae wannan lokacin fuskarsa cike take da walwala dakuma annashuwa cikin tangamemen palon mahaifin nasu wato muhammad bama t'sohon soja,babu abinda ke tashi sai k'aran plate da cokala suna ci abincin dare haske tar kamar rana t'saka sbd k'oyayen da sukayima palon kawanya suna bada haske mai yalwa...!

husna na jikin momma dake ta bata abinci a baki tana ta zuba shagwab'a son ranta,su sadam,aminulla da areef suma sun zama zaratan samari masu cikar haiba ! a halin yanxu suma suna da muk'ami mai girma a aikin su na jami'an t'saro...!

sadeeya na gefen baa itama tana ta masa tab'ara ita wai tagaji da wariyar launin fata da momma ke nuna mata,sbd taga husna suna kama shiysa ita bata bata abinci a baki...! wanda hakan yasa kowa darawa a wajen,baa kuma dakansa yake bata abincin babu kunya ko take cin abinta...!

anty farida da kuma umma jameela dik suma suna wajen dasu ake hiran tinda mak'iyan nasu basama k'asar baki d'ayansu ballanta na asamu abin fad'a!
ansha hira sosai a wannan ranar kamar babu gobe,sai wajen 11 na dare kamin kowa yasamu wajen ajiye hak'ark'arinsa...!

washe gari da safe ma su husna bada wuri aka tashi ba an huce gajiya,wanda a wannan ranar ma suka yi ta raha cikin y'an uwansu...!

saida suka shafe sati d'aya cur da dawowa daga dubai kana gida yagama dawowa daidai wanda amni ta dawo daga niger itama kwana uku dasuka gabata,su husna sunje gaisheta ta ansa babu kunya irin ta masu allah yasa an gama a sa'a d'innan kamar yadda sauran y'an gidan nasu suka masu,wanda hakan yasa deeya buga uban t'saki ta bar wurin batare da b'ata lokaci ba,itakam iyayen hak'uri ko a fuska bata nuna mata ba suka rabu lahiya...!

misalin k'arfe 6:30am bayan su baa sun shigo tare da sauran y'ay'ansa maza daga masallaci kamar yadda d'abi'ar gidannasu yake suka yada zango a parlonsa,sannan kuma sauran matan nasa dakuma y'ay'an nasa mata baki d'ayansu sun shigo kamar kullum bayan an gama gaisawa baki d'aya baa yayi gyaran murya alamun zayyi magana mai mahimmanci wanda haka yasa suka zuba masa ido baki d'ayansu domin jin da wacce yazo yaukuma...!


*team nigeria*
*team niger*
*team ummie2018*

*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018🐎🐎*

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now