part 37

84 4 2
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌻🌻©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌻🌻*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

        *page 37*


*bayan kwana uku*

A yau aka tashi da shirye shiryen tarban major general aliyu muhammad bama bayan t'sayin watanni goma da baya tare da ahalin nasa...!

sosai aketa farin ciki da dawowarsa bama kaman matansa,dik kuwa dai da agefe d'aya na zuciyar fad'imatou na zullumin kalar tarbar da zata samu daga wurinsa...! amma haka nan ta daure itama tana kyautata masa zatoh cikin zuciyarta...!

sosai husna da fad'imatou da masu aikinsu da aka had'osu jattijuwa d'aya dakuma matashiyar y'arta suka kint'sa komai da komai...!

sannan kuma suka mawa oga girki mai rai da lafiya kala kala...! wanka fad'imatou tayi ma baby yumna aka kint'sata cikin kayanta mai matuk'ar kyau da t'sada da dik cikin kayan da ubanta inoussa ya saya mata...!

shareefa ma ta shigo taya su aikin,dan haka itace ta rik'e yumna sbd itama uwar yumnan tasamu damar kint'sa nata jikin...!

k'arfe biyu daidai jirginsu aliyu ya sauk'a a filin jirgin maidugurin...!inoussa,aminulla,areef dakuma sadam ne suka tarbosa daga filin jirgin ...! ya buk'aci zai fara xuwa gaishe da iyayen nasu kamin ya wuce gidannansa...! babu musu sadam dake driving na motar ya danna horn a makeken gate d'in dake gidan nasu wani ingarman soja ya bud'e musa bayan ya tabbatar da cewa y'an gidane...!

a parking space suka ajiye motar dik suka fiffito,inda suka wuce part na mahaifinnasu dasuka samu sauran yaran dik acan sai hira akeyi cike da walwala dakuma k'aunar junansu...!

iyayensu mata ne kawai basa wurin,saikuma ilham da yanxu itama sam zaman gidan baya mata wanj armashi sbd an d'auke mata yayun nata baki d'aya tana daga gefen mahaifinnasu tana ta mat'sar k'walla alamun dai wani abu take so aka hanata...!

kowa yayi farin ciki da dawowar aliyu cikin k'oshin lafiya...!inda ya shiga dikkanin part na matan baban nasa yagaida su daga k'arshe ya shiga part na mahaifiyarsa da itama sosai tayi farin ciki da dawowar d'an nata cikin k'oshin lafiya...!

saida akayi sallar la'asar kamin aliyu yayi sallama da y'an gidan nasu,suka d'auki hanyar gida a motar inoussa ana take masu baya...! horn inoussa ya zuba wanu kurtun soja ya wangame masu k'ofa suka kunna kan motar tasu cikin gidan...!

wanda hakan yayi daidai da fitowar shareefa hannunta d'auke da yumna da niyyar wucewa gidanta da yarinyar,inda kuma allah ya taikamaka ma yarinyar bamai hayaniya bace da an banu...!

da fara'arta ta k'ariso wurin nasu wanda itama take sanye cikin wani alkyabba kalar na gidan sarauta d'innan...! hakan yasa ko ina na jikinta a rufe yake ruf ko kayan datasa ta ciki ba'a gani...!

"sannunku da zuwa yaya's..." take fad'a fuskarta shimfid'e da murmushi!

cikin murmushi sosai aliyu yake ansa mata a lokaci d'aya kuma yana ansar baby yumna a hannun shareefa sosai ya rungume yarinyar for d first time cike da t'sant'sar shaukinta dakuma soyayyarta ba kad'an ba shikuwa oga inoussa ko kallon inda suke baiyi ba,sbd shifa babu wani jituwa kona second d'aya t'sakaninsa da yarinyar sam...!

karb'ar yumna inoussa yayi a hannun aliyun suka wuce gidansa bayan yayi sallama da aliyun shareefa ma ta take masa baya cike da sanyin jiki na halin ko in kula da mijin nata ke nuna mata...!

da kallon tausayi aliyu ya rakasu...! sosai yake tausayin d'an uwannasa yanzu shima...! sbd shifa shaida ne da kalar yadda inoussa keson fad'imatou tin tana k'ank'anuwarta amma gashi nan laifin da basu suka aikata ba yasa k'addara tayi ma d'an uwannasa yankan k'auna da muradin zuciyarsa...!

ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauk'e bayan yaga fitarsu daga cikin gidan ya maida akalar kallon nasa akan sojojinsa dasukayi zuru zuru dasu...! fahimtar mai ogan nasu ke nufi yasa su sara masa dik suka wat'se suka barsa shi kad'ai a haraban wurin...!

cike da takunsa na izza dakuma t'sant'sar jarumta ya doshi main entrance na gidan,wanda sosai zuciyar y'an mazan yafara bugun kalangu sbd rashin sanin tak'amaimai kalar tarbar da zai samu daga matan nasa...!

sassanyar k'amshin turaren wuta gauraye da wani daddad'an room freshner ne yayima aliyu welcome a lokacin da ya sako kansa cikin parlon...!

lumshe mayun idanuwansa yayi yana baza hancinsa domin yaba hancinnasa hak'k'insa...! saida ya shafe a k'alla mintina uku kamin ya bud'e idanuwansa tar ya sauk'e a cikin parlon  da a halin yanxu yazama mallakinsa ko kuma ince main parlon nasu gaba d'aya...!

husna ce ke zaune cikin shiga ta alfarma na bugawa a jarida...! sanye take cikin wata laffaya y'an ubansu na asalin kanurin borno ...! kallo d'aya idan mutum yayima laffayar zai tabbatar da cewa ba k'aramin kud'i aka zuba ba wajen sayansa...! fuskaarta zane yake da kwalliya mai matuk'ar t'sari da fasali wanda a kallon farko ga wanda baisanta ba sai yace yayi gamo ne hurul ain😎

sosai ta tafi da imanin aliyu haka nan itama tin shigowarsa ta zubama yayannata kuma mijinta idanuwa tanajin wani abu na taso mata can k'asa zuciyarta mai kama da ......😎

sosai suke kallon junansu kamar wayanda suka soma kallon junansu a yaud'in...! a hankali yake takowa zuwa inda take yanaji kamar ana ingizasa ne izuwa ga k'anwar tasa kuma matarsa a halin yanxu...!

tin kamin ya k'araso husna ta rigasa mik'ewa da wani kalar tafiya mai matuk'ar jan hankalin dik wani lafiyayyen namiji ta tinkari yayan nata ...!

ajiyar zuciya mai masifaffen k'arfi suka sauk'e kusan lokaci d'aya jin yadda sukaa samawa kansu kyakkyawan masauk'i bisa ga jikin junansu...!

sosai aliyu ya k'ank'anme husna kamar zai maidata cikinsa t'sabagen yadda yayi kewarta fiye da tunanin mai karatu...! notikan kansa ne yafara kwance k'warai jin yadda wani shegen k'amshi ke masu bugun waken k'osai a hancinnasa...! k'ara cusa kansa cikin wuyanta yayi yana baza hanci yana kwasan k'amshin da bai tab'ajin kalarsa ba t'sawon rayuwarsa...!ga kuma wasu abubuwa dayakeji sun tokare masa k'irjinsa masu matuk'ar laushi da girma danima na gaza gane ko minene🤸‍♂️😎🤸‍♂️

su goggo husna ma an samu masauk'i a kan k'irjin gwarson nata aliyu sosai ta k'ank'amesa itamaa kewar mijin nata dakuma sonta na samun muhalli mafi girma cikin zuciyarta...!

wani k'amshin da hancin aliyu ya shak'a ne a daidai wannan lokacin wanda yake da tabbacin badaga jikin husnarsa yake yankowa ba yasa shi bud'e idanuwansa dasuke lumshe t'sawon wannan lokacin...!

karaf idanuwansa suka sauk'a jikin na fad'imatou dake t'saye a t'sakiyar parlon,sanye take da wani tattausan tissue (material) wacce takama jikinta sosai doguwar rigace ta k'asa kuma ta bud'e...! sosai ya fidda yanayin t'sarin halittarta mai matuk'ar girgiza zuciyar y'ay'a maza...!
fuskarta babu kwalliya ko kad'an sai powder dakuma lipstick dana shafa kad'an a bakinta saikuma kwallin data zirara a idanuwanta...! hmm sosai tayi kyau na ban mamaki kasancewar labban bakinta marun ne asalin sai yazamana kamar ta shafa jan baki...!
gashin girarta bak'i sid'i dashi abindai sai wannda yagani...!

takai minti uku da fitowa sosai tayi yak'i da zuciyarta a wannan lokacin domin allah ne kad'ai yasan kalar kishin mijin nata dake mak'ale cikin zuciyarta...! kamar zai waske,saikuma yaga rashin dacewar hakan ya bud'e mata hannunsa ta gefen husnar ta shigo cikinsu ya had'e su ya rungumesu wanda suka sauk'e kyakkyawar ajiyar zuciyar zuciya kusan lokaci d'aya...!

*team aliyu and husna*
*team inoussa and fad'imatou*
*team ummie2018*

*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018🐎🐎*


  *INA MASOYAN KARANTA LITTAFAINA NA HAUSA NOVELS...?? GA HANYA NAN MAFI SAUK'I DA ZAKU NUNAMIN SOYAYYARKY TA HANYAR BIYAN KUD'IN KARATUN LITTAFINA MAI TAKEN "ANYA KUWA...?" AKAN FARASHI MAI SAUK'I NAIRA D'ARI BIYU KACAL NA KATIN AIRTEL KO MTN ZAKUYI SCREENSHOOT NASA KU TURA SHI TA WHATSAPP A WANNAN NUMBER👉🏽09076427357 ...! SAINA JIKU MASOYAN LITTAFAINA A DIK INDA KUKE😘 A HALIN YANXU MA KUMA AN D'ANYI NISA DA FARA PAID PAGES🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️*

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now