Part 32

85 11 0
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌻🌻©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌻🌻*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

        *page 32*

Ikon allah ne kad'ai yakai inoussa cikin garin maiduguri lafiya sbd kalar tuk'in gangancin dayakeyi...! yana shiga cikin gida ya wuce shashinsu ya kulle kansa a d'aki yana kuka sosai ba kad'an ba na tausayin kansa dakuma bak'in cikin abinda aka aikata masa da babu k'wak'k'waran dalilin dazaisa ya yarda bada son ran baa aka rabasa da farin cikin rayuwarsa ba...!wanda hakan yasa sosai yaji zafin mahaifinnasa ba kad'an ba...!

tin yanayin kukan na kad'an kad'an har abin ya girmama yafara tari sosai ba kad'an ba...! wanda hakan yasa wani dunk'ulallen jini mai had'e da t'soka yake t'satuwa a dik lokacin da yayi tarin...!😭

a haka wani wahalallen bacci yayi gaba dashi cikin wannan yanayin...!

bai wani jima sosai ba su aliyu ma suka iso...! saidai shikam gidan da baa ya gina masu ya shiga...! gidan yakasance sama da k'asane daman,sama aka zuba kayan jeren husna da aka mata...! k'asa kuma empty ne...!

kamo hannunsu yayi da suke ta tirje tirje suna masa bori amma yayi kunnen uwar shegu dasu yayi biris...!

suna shigo cikin parlon k'asa daya kasance yalwataccen parlo ne sbd babba sosai mai d'auke da k'ofofi wajen guda hud'u...! saikuma ta gefe can inda mutum kan iya hawa upstairs nasu dake ta jikin bango wanda mutum idan zai sakko ma ba lallai a iya ganinsa ba idan yaso...!

labulaye ne kawai cikin wannan parlon kalan peach masu matuk'ar kyau da t'sari,inda pentin cikin parlon ma ya dace da t'sarin yanayin labulayen...!

husna ta d'ago da niyyar kartama aliyu rashin kunya da yazo mata gadan gadan idanuwansu ya sarke tare da fad'imatou a bazata...! wanda hakan yasa su zabura kusan lokaci d'aya suna nuna junansu jikinsu na b'ari sosaii ba kad'an ba,baku nansu yagaza furta koda kalma d'ayace...!

sam basu san junansu ba dik wannan budurin abubuwan da akeyi,sai yanxu suka shaida junansu...!

sosai zuciyoyinsu ke bugawa cike da mat'sanancin wani mai kama da kishi game junansu(😎 anzo wajen fa🏋🏻‍♀️)...!

kamo hannun ya aliyu husna tayi jikinta na b'ari ta rungumesa ta kwata bisa faffad'an k'irjinsa tana sauk'e ajiyar zuciya kamar wacce tayi t'seren gudu...! shiko aliyu dama yazama statue ne yana kallonsu kamar tv cike da mamaki...!

fad'imatou ma sosai zuciyarta ke bugawa na ganin yadda husna tayi kanekane a k'irjin aliyun,wanda har cikin zuciyarta taji zafin hakan sosai...!

"ya aliyu,dan allah idan wannan ce wacce ya inoussa ke kuka akanta ka taimaka ka sakar masa matarsa ya aura...! wlhi baku dace da ita ba ko kad'an...! dan allah kasake......"

tun kamin ta k'arasa fad'ar abinda tayi niyya aliyu yayi mata wani shegen bangaza data kusan kaiwa k'asa allah ya tak'aita ta dafe bango,amma dikda haka saida ta buge k'ugunta ...!

wani mat'siyacin kallo aliyu kebin husna dashi kalar na baki da hankali amma...! "wato sai yau na tabbatar baki da hankali asma'u! matar tawa kike ambata da matar wani banza wai shi inoussa...? to wlhi ahir d'inki...! ki kiyayeni! idan ba haka ba kuma billahillazi la'ilaha'illahuwa saina koya maki hankali cikin gidannan...! wawuya shashasha kawai...!" yana gama fad'ar abinda ke ransa ya kamo hannun fad'imatou da har cikin ranta taji dad'in abinda aliyun yayi,amma kuma fa bawai don tanajin wani sonsa bane cikin zuciyarta(🤓)

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now