Part 31

84 10 2
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌻🌻©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌻🌻*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

        *page 31*

"Sannan kai kuma aliyu gadanga abinda nake so dakai shine...! dan allah badan muba...!dikdama dai abinda muke k'ok'ari aikatawa laifi ne babba amma kuma sbd gujewa tashin tashina na abinda kan iya zuwa da dawowa cikin zuri'armu ka sawwak'e ma yarinyar nan (fad'imatou),yaso a maida shi kan d'an uwanka tinda kaga bisa kuskure aka d'aura auren dakai kumama yarinya ta nuna ita sam bata ra'ayinka...! sannan gashi dik akan hakan babbar mat'sala na kunnowa t'sakaninka da d'an uwanka da baka da kamarsa wanda kuka kasance kun kwanta cikin mahaifar mahaifiyarku tare...! sannan ta haifo ku a rana d'aya kuka taso cikin soyayyar junanku...! wanda inada tabbacin yau ko ranka akace ka basa kai mai iya basa ne ballanta kuma mace...? kayi duba sosai cikin maganata kaduba kaga mutane nawane zasuyi farin ciki idan ka yanke alak'ar dake t'sakaninka da fad'imatou...? kayi ceton rai dan allah aliyu...!"

maa tak'are maganar tana mai sakar ma aliyu idanuwanta domin ganin yanayin yadda zai karb'i maganar...!
amma me...?

wani dogon t'sakin da aliyu yaja kamar zai t'sinke harshensa yasa wayanda suka fara k'ananun gulma t'sakaninsu suka maido akalar idanuwansu gareshi har yawu na d'ilala...! bama kamar inoussa dake bin aliyun dawani kalar t'sant'sar mamaki... !

"wlhi tallahi...! babu wanda ya isa yasa na saki matata a fad'in duniyar nan sai mutum d'aya yamin magana...! dikdama ko zan saketan ma bada son raina zanyi hakan ba...! bandama rashin sanin ciwon kai irin na mutane a wani dalili zaku d'auramin aure da yarinya sannan yanxu kuma kuzo kuce nasaketa sbd wani banzan mutum da har yake d'aukan k'azamin hannunsa yace zayyi fad'a dani...? toh allah ya t'sine ma y'an uwantaka da haihuwarmu da akayi a tare...! kai ni koma uban waye yazo billahillazi la'ila ha illahuwa bazan saki matata ba...!!"

tashin hankali kenan take amni ta k'ara farkewa da wani sabon kukan takaicin abinda inoussa yace,tana so ta t'sawatar masa kuma ta t'saida shi akann wayannan maganganun da yakeyi amma kuma sam ta kasa...! ita t'soronsa ma takeji kar taje yayi mata abinda bashi ne...! gani take kamar ba aliyu d'anta ba!

mik'ewa baa yayi da niyyar kwad'ama aliyu mari amma kuma saiya koma jagwaf kan kujera kamar wanda aka hankad'asa kan kujerar...!

kowa idan yayi wani yunk'uri na ganin ya dakatar da aliyu amma sai ya kasa...!

husna dasu sadeeya kam sun zama y'an kallo ne a wajen sai ido ne nasu...! umma jameela kam zuciyarta fari tas take na ganin wannan abu daya faru,wanda ko ita kanta bata tab'a tunanin faruwar wannan abu ba t'sawon rayuwarta...! amma kuma ta wani wajen tana d'an tausayin inoussa sbd itama tasan zafin kaso abu ammma kuma kananji kana gani yafi k'arfinka...! kamar yadda mahaifiyarsu(amni),ta shige masu hanci da k'udundune a cikin gidan...! wanda idan ta tuno hakan ma allah shi k'ara take masu cikin zuciyarta,tace wata kila sun fara girban abinda iyayen nasu suka shuka masu ne ta wannan hanyar...!

momma kam dikda abinda ke faruwa ma batayi yunk'urin tofa nata albarkacin bakinba...! tunaninta gaba d'aya ya karkata ne ta yadda zata gyara y'arta sosai na ganin zatayi farin ciki gidan aurenta batare data shiga cikin damuwa ba,tinda k'addarar husnar tazo akan zata zauna ne da abokiyar zama tin farko aurenta batare data d'an more kalar amarcinnan da akeyi ita da mijinta kad'ai ba...!
kowa dai da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa a wannan wajen...!

"shikkenan aliyu! ga nan fad'imatoun na bar maka ita har gaban abada...! kaje da ita!kuma a yau na fuskanci kalar ikirarin soyayyar da kakc cewa kanamin tin muna k'anana! kasha cemin kome na gani a duniyar nan idan ina sonsa muddin kana da hanyar mallakamin shi ! to kuwa na d'auka cewa ka gama mallakamin,amma gashi yanxu ka gagara aikata hakan a gareni? babu komai kaje da fad'imatoun,allah yabaku zaman lafiya cikin zamantakewar aurenku...!"

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now