part 16

55 10 1
                                    

    *NIGERIA KO NIGER...?*
         (wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_'''( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight our readers)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

         
 
*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI MAI KOWA MAI KOMAI DAYA BANI DAMAR CI GABA DA KAWO MAKU WANNAN NOVEL DIN―― AMMA PHA KAN MAGE YA WAYE IDAN NAGA BAKWA COMMENT NAKU AKAN BOOK DIN NIMA ZAN BAWA KAINA HUTU NE KAWAI🤦‍♀️KARKUMA A BIKA PC ANA CEWA MAKA BULA BULA,WAYA MUTU WA YA TASHI 😂🤣……ZANGA KAMUN LUDAYINKU AKAN PAGE DINNAN*

               page 16

kallon cikin ido sukeyiwa junansu,kowacce da abinda taje sakawa cikin ranta wanda suka barwa zuciyarsu sani... ga kuma mamaki shimfide bisa kyakkyawar fuskar ko waccen su...

husna ce tafara kauda kan cikin sanyin jiki dakuma fargaba da tarasa na mainene...inda tamaida kanta bisa ga littafanta,bawai kuma dan tana fahimta ba.

fadimatou ganin yarinyar ta dauke kanta yasata itama maida kanta kasa bisa ga karamar laptop nata badan tana fahimta ba,saidan tsananin mamakin kyawun yarinyar da kuma mamakin kanta,ta yarda ta kure ta da kallo abinda sam ba tsarinta bane...

deeya kam batama san sunayi ba ko kadan sbd kocokan hankalinta na bisa ga littafanta tana nazarinsu...

fadimatou tattare kwamutsanta tayi ta wuce apartment nata sbd ji tayi sam wajen bai mata ba yaukam...

kamar ance ma husna daga kanki taga gurin wayam babu kyakkyawar budurwar da tagani babu dalilinta,hakan yasakata jan zaki kasa kasa,data rasa dalilin yinsa...

saida suka ga magriba ta doso kai kana suka tattara shirginsu suka bawa iska ajiyar wajen...suna hirar su kasa kasa.

kowa room nata ta wuce inda suka dauro alwala suka gabatar da sallar magariba,sai bayan isha'i kamin kowaccen su tafito parlo inda house maid nasu takawo masu dinner,suna ci suna hirarsu gwanin sha'awa...

wayar deeya ce tafara naiman agaji bayan sun gama cin abinci,batayi wata wata ba ta kule bedroom nata,bayan ta nitse bisa ga tangamemen bed nata tayi picking,inda takashe murya kamar ba deeya mai kwarapniya ba...wanda haka yasa banji ko mi ba,dan haka na lallabo na dawo ga husna...

murmushi na tarda ta tana ta zubawa bayan hankalinta kwacokan yana kan wayarta,wanda hakan ya tabbatarmin da abu mai mahimmanci akeyi...tana matukar son masoyinnata.

saida tagama ta mike cike da annashuwa ta wuce ha a  en bedrom nata...wanka tay bayan ta fito ta mulke jikinta da daddan humra kamar kullum,sai tabi jikinta da wani body spray mai daddadan kamshi da sanyaya zuciya.....

lumewa tayi bisa bed nata, ta latsoma baa kira cikin second goma ya   auka,bayan sun gaysa cike da tsantsar soyayyar   a da mahaifi sukayi sallama kamar badazu suka gaysa ba wai ita tayi kewar gida sosai...

umma jameela ta kira bayan sun gaysa cikin sakin fuska,sabida itama jameela bata da wani matsala sosai saina jarababben kishin daya zame mata jiki...kuma shima bada kowa takeyi ba sai mariama(amni)...

duk wanda yakamata ta kira hatta ga yayunta maza,sannan takira shehu abdulrahman ma sun gaysa,sbd yadda take matukar kaunar wan mahaifinnata...

last ta kira momma suka sha hiransu,kasancewar husna bata da saurayi dan haka take waya da yan uwanta aduk lokacin da kewa ta dameta,

saida sukayi sallama tayi alwalar kwanciya baccinta ta tofa addu'ointa ta kara lumshe lumsassun idanunta daniyar yin bacci! sai kuma ya *haydar* nata ya fado mata a rai...shaf ta mance bata kirasa ba duk rububin kirayen kirayen da takeyi,hakan yasata mika hannunta ta janyo wayarta da tasaka a silent...

digits nasa ta latso wanda saida yakusa tsinkewa kamin aka daga,daga bangarensa ...

a daidai wannan lokacin yana kwance bisa daya daga cikin luntsuma luntsumar kujerun parlon su yana buga game na zuma cike da nishadi...sbd game din na matukar birgesa...

jikinsa sanye da pyjmas haddu sai tashin kamshi yakeyi,ga gashin kansa dasuke kwance luf gwanin sha'awa...sbd bashi da niyyar kara fita a halin yanxu

lumshe zaratan idanunsa masu matukar kaifi da kwarjini,dayake birkitama yemmata,mara gaskiya lissafinsu a duk lokacin da sukayi tozali dasu...

bayan ya dauki wayar shuru yayi,bayan ya hade fuska kamar a filin daga waishi ala dole ya babba baya son raini...

daga bangarenta jin yayi shuru yasata zumburo baki cike da shagwaba tafara masa kananun kukanta data saba masa idan abin yar farin ya motsa mata...

har zuwa wannan lokacin bayyyi magana ba saima wani killer smile dayakeyi kasa kasa batare daya bata damar fahimta ba...yana dan sosa kasar habarsa wacce ke kyawace da kyakkyawar suma...

jin yamata shuru tasa hannunta da niyyar sauke wayar bisa kunnenta taji muryar dan uwannata cike da sautin lallaba "Asma'uuu"inda yadan jaa karshen sunan nata wanda hakan yasa taji takasa aiwatar da niyyarta ta farko...

cikin sheshsheka kamar wacce aka mata wani abu tace "ya aliyu na"

murmushi yasake mara sauti yace "sai yanxu aka tuna dani kenan?"

"am curry yayana wlhy na shafa'a ne,yanxu ma saida har na kwanta natuno ban kira ka ba"

yatsina fuska yayi kadan,alamar i don care dinnan yace "naji,dama ay nine makiyan wasu da ba'a damu dani ba ake manta ni"

"um um ya haydar"

ajiyar zuciya yasauke inda yadan saki fuska suka dan taba hirar da bata da hayaniya sbd ko wanne danasa  shariyar... a haka suka kare sukayi sallama...

ajiyar zuciya tasauke itama ta kashe wayarta kamin ta janyo blanket ta rufe har fuskarta,bacci yafara fusgarta sama sama fuskar budurwar dazu ya fara mata gizo...dakyar ta yakice tunanin a ranta bacci yayo gaba da ita,cike da mafarkai barkarai marasa kan gado, daya tsaya mata a rai...asuba ta gari husna.

bangaren deeya saida ta gama soyewa da tuzurun yayanta kuma rabin ranta wanda suka shafe tsawon gud 3hrs sunayi kamin sukayi sallama...

itama wanka tayi kamin ta shafe jikinta da humra mai dadi kalar na husna,bayan tasaka sleeping dress nata tayi switch off na wutar dakin,ta wuce dakin husna,wacce takai 30mins dayin bacci...

shigewa bargon tayi ta tofa addu'oi ta shafa kana ta shafawa yar uwarta ganin yadda take gumi...daganan ta kulle idanunta bacci yayi gaba da ita...

   ――――――――――――――

Bangaren fadimatou a lakacin da ta mike tawuce apartment nata tayi wanka kamin ta shige kitchen da kanta ta hado simple noodlea sai tashim kamahi yake ta cinye abinta ... daganan tamike bisa ga resting chair dake cikin parlon irinna yan sarauta...

tunani tafada da fuskar husna wai shin dama ana samu kyawawa irinta zamanin nan...? a haka dai tana ta tunane tunane bacci yayi gaba da ita cike da mafarkin fuskar yarinyar da ta gani,

magriba ta farka bayan sallar isha'i tayi bitar karatunta daganan tayi wanka da alwalar kwanciya tabi lafiyar katifarta inda suka sha luv nasu da inoussa rabin ranta.....asuba ta gari.

*Gayu ban manta ba yasin,daga yanzu yanayin comment yanayin typing,idan ba haka ba kuma a jingine rubutun baki daya🤕*

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummie2018*

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now