PART 26

67 7 0
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌻🌻©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌻🌻*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

    
        *page 26*

Kallon su momma keyi da jajayen idanunta dasuka kad'a sukayi jazur dasu sbd t'sananin tashin hankali dashiga rud'u...!

a sukwane kowannensu ya rarumo suturarsa da suka tafi xuwa wata jihar a lokacin da suke cikin gajimare suka suturta jikinsu ...!

batare data ce masu k'ala ba taja k'afafunta dasuka mugun yimata nauyi tabar d'akin tana zubda hawaye masu matuk'ar radad'i da cin zuciya...!

xubewa tayi a bakin gadonta tana ci gaba da kukan da takejinsa ya fiye mata komai a halin yanxu...! wai musan da take yabonsa da sallah zai gagara al'wala...? wanda take tunanin ko bayan ranta shi mai iya t'sayawa ne t'sayin daka na ganin ya d'aura su halima kan tafarkin t'sira amma shi takama dumu dumu ita ganau ba jiyau ba yana k'ok'arin ketama y'ar cikinta mutunci cikin shashenta...?

kai innalillahi wa'inna ilaihirraj'iun,wannan masifa dame tayi kama...!? badan allah ya kawota a daidai wannan lokacin ba shikkenan musa ya shiga gonar da bata gama zama mallakinsa ba...?

B'angarensu musa kam banda kukan nadama dakuma t'sant'sar kunya babu abinda sadeeya keyi a wannan lokacin...! ta sab'ama mahaliccinta...! gashi kuma ta sab'ama mahaifiyarta har tana zubda hawaye dik a sanadiyyar wannan shirmen dasukayi k'ok'arin aikatawa mara tushe...?

badan allah yakawo momma a daidai wannan lokacin ba kenan da yanxu sun aikata zina...? wanda bata da tabbacin musa zaici gaba da ganinta da daraja sbd ta riga data zubar masa dashi tin kamin su mallaki junansu a mat'sayin abu d'aya...?

kallonta musa yayi da rinannun idanunsa dasuka kad'a sukayi jazur yace "haleema biyoni muje wurin momma..." bai jira ansarta ba yafice itama ta rufa masa baya...!

cike da sanyin jiki suka shigo kansu a k'asa,takawa musa yayi zuwa gabanta ya zuba gwiwowinsa a k'asa ya shige jikinta yana zubda k'walla masu matuk'ar zafi...! yunk'urin ture kansa daga jikinta momma keyi amma yak'i bata daman hakan...! saima k'ara shigewa jikinta da yayi yana sakin kuka mai fidda sauti sosai ba kad'an ba...!

"na rok'e ki da girman allah momma ki yafemin abinda muka aikata...! wlhi wannan ba halinmu bane sharrin shed'an ne dakuma bin sharrrin zamani dake k'ok'arin kaimu ga aikata abinda bazamu tab'a daina dana sani ba har k'arshen rayuwarmu...! na aikata maki kuskure mafi girma da har ina kunyar had'a ido dake sbd yaddarki da kika bani d'ari bisa d'ari amma gashi na wat'sa maki k'asa a ido...!

momma dan allah ki daina zubdar mana da k'walla...! sbd hawayenki babbar musibace a garemu...! allah yana fushi da dik yaron daya kasance shine silar zubar hawaye a idanun iyayensa...! wanda kuma nasan kema bazaki so ubangiji yayi fushi damu ba...!  mama kamin ta rasu tacemin idan na zamana nine silar zubar hawayenki har gaban abada itama zatayi ta zubda k'walla,koda kuwa bata cikin duniyarne har sai idan ke kika yafemin...! momma dan allah ki yafe mana mun aikata babban kuskure..."

musa ya k'are maganar yana mai fashewa da kuka sosai...! wanda hakan yasa momma daina yunk'urin ture kansa daga jikinta...! saima rungumeshi tayi da kyau,wanda hakan yabama sadeeya damar takowa zuwa garesu itama tashige jikin momma! wanda hakan yasa momma ta had'esu duka a jikinta ta rungumesu bayan ta t'saida hawayenta...!

"wannan nasan ba halin yarana bane...! ku fad'amin mai yakaiku...? mai zaisa ku aikata abinda kukasan cewa haramunne allah na fushi ga duk mai aikata sa...? waya baku shawarar aikata hakan kuma...?"

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now