Part 28

68 9 0
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌻🌻©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌻🌻*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

    
        *page 28*

_K'ASAR NIGER_

Cikin masarautar agadez...! wanda tin daga yanayin cikin garin zai tabbatar maka da cewa lallai ana mahimmin abu ne na manya...! har saida na tambaya aka shaidamin ai ana bikin y'ar gidan sarkin garinne mai ci a yanxu wato _FADIMATOU ALMUSTAPHA...!!_ Y'a tafarko a gurin mahaifinta data kasance y'ar gata ta bugawa a jarida,k'yak'k'yawa k'in wanda ya rasa...!

gimbiya fadimatou akoi kunya,izzza,hankali,nat'suwa dakuma uwa uba kyakkyawan tarbiya data samu daga iyayenta harma da sauran danginta...!

dikda kalar gatan da iyayenta da mutane da dama daga cikin masarautar dama way'anda basa cikinta suke nuna mata hakan baisa ta tashi a fand'are ba...!

sai ya kasance ta zamana yarinya mafi girma da daraja a cikin idanun mutanen gidansu dama yankinsu baki d'aya...!

saidae kuma dik wanda bai zauna da ita ba,ba lallai ne yafahimci kalar qualities d'indake tattare da ita ba,kasancewarta yarinya marason hayaniya...!

wannan kenan...!

kad'e kad'e ne kawai da busa kalar na gidan sarauta keta famaan tashi,wanda auren ma ba yau bane,sai nan da sati d'aya,kawai dai shagulgulan biki ne daya kama akeyinta sbd wannan d'in bikin y'ar gata ne...!

kusa kaina nayi can cikin shashen da matan sarki suke...! _HADIZATOU_ itace mahaifiyar fad'imatou data kasance uwar gida a gurin sarki almustapha,y'a d'aya suka haifa t'sakaninsu wato fad'ima...!

bayan ita kuma ako matansa guda biyu _AICATU_ itace matar sarki ta biyu,y'ay'anta uku ne a gidan,kuma dikkansu mazane _kamalou,isyakou dakuma fuad_ ...!

sai matar sarki amaryarsa mai suna _HINDATOU_ tana da yara biyu twins mace dana miji _shareefa da shareef_...!

akoi fahimtar juna sosai a cikin wannan masarautar,dikdama ance wai kowani gidan sarauta zaka samesu da kalar tasu mat'salolin,wanda kuma ba komai ne ke kawo hakan ba sai rashin fahimtar juna da shuwagabannin basu wanzar dashi ba daya kamata...!

Amni(k'anwar sarki almustapha ce,wato mamansu aliyu da inoussa kamar yadda na fad'a a baya idan baku manta ba...)...!

ba k'aramin so takema fad'imatou ba kamar ta goyata haka taje,wanda kuma hakan nada nasaba da rashin y'a mace da allah bai bata ba...! takuma gagara jawo y'ay'an mijinta a jiki ballantana suna rage mata kewar y'ay'a mata sbd dalilinta mara tushe(kishi)...! komai tasamu wani zubin kamin ta tuna da kowa ta tuna da fad'imatou ne...! wanda hakan yasa akoi k'yak'k'yawar shak'uwa t'sakaninsu kamar ya da k'anwa haka suke...! dikda basa k'asa d'aya hasalima fad'imatou bata tab'a zuwa nigeria ba idan ba amni bace taje niger amma kuma waya tana aiki sosai t'sakaninsu,wanda saida aka fara zancen aurennanne ma fad'imatou ke d'an zamewa amni sbd kunyar surkuwa...!

yau takama laraba...!sannan kuma an jera kwanaki biyar ana shagulgulan biki sosai ba kad'ann ba...! kama daga al'adu harma dasu k'auyawa dadai sauransu,yanxu yarage saura kwana biyu a d'aura auren...!

Dik wanda yaga yadda amarya fad'imatou tayi masifar kyau sai yace babu kalar masu kyawunta dakuma murjewar lafiyayyiyar fatar jikinta tayi a iya t'sayin rayuwarsa daya sani...! kamar wata aljana data k'irk'iri kanta t'sabagen k'yawunta datayi,wanda kuma an hana ta had'uwa da ango sbd gudun mat'sala kamar su oh oh(🤨)...!

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now