part 12

61 6 0
                                    

    *NIGERIA KO NIGER...?*
         (wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

                 page 12

Haka rayuwar gidan ke tafiya cike da abubuwa na takaici da ban mmk...

saida su aliyu suka shafe tsawin wata daya a nigeria kana sukayiwa garin agadez tsinke inda aka masu tarba ta ban girma a matsayinsu na jikokin sarki...

A wannan lokacinne aliyu ya fara haduwa da fadimatou inda daya ganta sai yacika shima da mmakin ganin tsantsar kyawunta da take dauke dashi...

basa wani sakewa tsakaninsu da ita sbd kowa jinin sarauta na yawo a jikinsa dan haka dama idan kaganta tana dogon hira saida iyayenta dakuma yayanta inoussa...

wanda zuwa wannan lokacin kowa yasan akoi soyayya tsakanin fadimatou da inoussa jira ake tagama makarantarta a daura masu aure sbd manya ma sunsan da zaman zance kuma akayi zama...

saidai kuma itama fadimatou tana da burin taga tayi dogon karatu koda ace baxa a barta tayi ayki ba karatu na bata sha'a wa a halin yanxu itama tana da shekaru 15 sa'arsu husna ce saidai sun girmeta da kwana arba'in...

saida suka masu one month acan kana suka juyo zuwa nigeria inda sukayiwa garin bama tsinke sbd su gayda shehu abdul dakuma tsohuwa mai ran karfe maa asma'u...

aykuwa sunga gata a wajen kakarsu dakuma yayan mahaifinnasu... saida sukayi sati biyu a garin bama kana musa yayi ma garin dirar makiya inda hakan yasa suka karajin dadin zaman garin sosai kasancewar yana da sakin fuska bashi da matsalar komai saina kasaita da akasan duk wani jinin sarauta dashi kuma shima sai abin ya motsa masa bawai kullum ba...

maa duk tasashi a gaba kan lallai ya fidda matar aure amma ya buga kasa yace sam baisan zancen ba sbd shi har yanxu matarsa bata gama girma ba kuma shima da sauransa...kuma a lokacin fa yanada shekaru 30 a duniya...

shehu abdul dayasan akan wacce yake magana sai bai daga hankalinsa kan saiya takura masa yayi aure yanxu ba sbd sanin cewa aure lokaci me kuma shima yayi na'am da zabin dannasa abin alfaharinsa...

Kaf cikin yayansa yafi son musa kuma hadda soyayyar mahaifiyarsa ne yashafe sa dan haka yake matukar tausayinsa amma kuma hakan baisa yayi ragon azancin da baa ke kwabawa a cikin gidansa ba...

hakanne yasa kan yayansa duk a hade yake sbd kowa an ajiyesa a matsayinsa... saidai kuma matan suna dan kishin yaron kunsan gidan sarauta da jarabar son mulki...?

rayuwar garin bama tayiwa su aliyu dadi fiye da tunanin mai karatu daan haka suka shantake sukayi zamarsu acan sbd sun ajiye ayki sai bayan shekara daya wanda lokacin yayi daidai da kammala makarantar su husna...

saida suka shafe wajen wata 2 da sati 2 kana suka dawo maiduguri cike da kewar kakar tasu kasancewar ita bata cika zuwa mai duguri ba saida ita aje mata kuma idan kaganta kamar ba itace ta ajiye jibga jibgan jikoki kamar su musa ba...

sadeeya da husna an shiga ss 3 karatu suke babu kama hannun yaro sbd kusantowar waec nasu  dan haka dole suka natsu suka maida hankali abinsu...

bangarensu aminullah kowa uwarsa taja masa kunne kan su fita shirgin baa idan baso suke yace su farayiwa kansu komai ba sannan yazare hannunsa akansu ba sbd sun lura indai kan yayan goal ne to zai iya batawa da kowa...

dole suka zubawa sarautar allah ido amma ko duk suna da mugun kudurinsu akan su koda kuwa ba yanxu bane dan haka yanxu rayuwar cikin gidan anayinsa kadaran kadahan...

ko da su aliyu suka dawo suka tadda wannan chanjin yayi wa aliyu dadi sbd shi bamai son kananun maganganu bane dan haka yake jan yan uwansa a jiki wanda haka yasa sadam yasake jiki da yayannasa amma ko har yanxu bai manta komai ba sbd akoi shi da dan banzan riko kamar me...

haka rayuwa ke tafiya da dadi babu dadi harsu husna suka kammala secondary school nasu kuma a lokacin suke da 16yrs inda duk wanda yagansu sai yayi tunanin irin yan 18yrs dinnan ne sbd cikar dasuka kara da kuma girman jiki...

Alokacinne suka tada ballin sufa sai sunyi karatun jami'a baa da shehu sam ba haka suka so ba sbd sunso ace saisun cika kudirinsu kan yayansu amma maaa tace sam ba wanda zai tilastawa jikokinta yin abinda bashine ra'ayinsu ba...!

dan haka dole suka hakura aka tambayesu makarantar dasuke so aykuwa cike da zumudi sadeeya tace DUBAI  suke so suyi karatunsu acan...

nan fa baa yadire kan sam baisan da zancen ba...wannan karan kam husna har kuka tayi inda itama tace nan take so...

baa yacika da mmk sanin cewa husna bamai yin magana bace akan duk abinda ya yanke akansu amma sai yaga sabanin haka nanma dai hankalinsa bai kwanta ba ya kira yynsa ya fada masa halinda ake ciki...

wai aykuwa gwanda ma baa domin ko shehu yace sam ba acikin zuri'arsu baa sbd shi bay taba ganin inda mata na gidan sarauta ke fitayin karatu har wata uwa duniya ba dan haka baza'a fara akan tasa zuri'arba!

momma kam dama tunda tanasu mgn na farko taga yadda suka kafe saisun tafi ta zuwa sarautar allah ido tasan abu ne mai wuya...

aliyu ma saida suka saka sa agaba kan lallai sai yaje yataya su rokon baa yabarsu suje wannan kasar aykuwa shima dayaje baa ya fatattakosa wanda hakan yasa shi basu hakuri kawai su hakura da zancen dubai su nemo wani makaranta wanda sukasan cikin nigeria yake...

husna taso karaya ganin yadda kowa ya bijire amma kuma deeya takara zugeta kan muddin ta hakura tasan itama ba za'ayi ba sbd burinta kawai taganta a kasar dubai tana karatu tun tana karama...tasan ba barinta za'ayi ba dan haka dole sukayi ta nacinsu tare amma fur baa yashafa ma idonsa toka yace baisan zancenba...

duk wainar da ake toyawa maa batasan da zancenba sbd babu wanda ya tunkareta da zancen...nan kou deeya ta kwadawa maa kira da safiyar lilllahi...!

IDAN NAGA KUNA COMMENT YADDA YAKAMATA KAM ZAN KARA YAWAN TYPING IDAN BAKWAYI KUMA GASKIYA ZAN RAGE...!

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummie2018*

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now