Part 27

67 5 0
                                    

  *NIGERIA KO NIGER...?*
       _(wacece bora)_

*🌻🌻©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION🌻🌻*

*_'''( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍🏻)️'''_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍🏻*
*whatsapp number:09076427357*

    
        *page 27*

washe gari da safe misalin k'arfe 7 na safe kamar kullum na al'adar gidan...!zaune suke a babban parlon baa,bayan anyi gaishe gaishe...!wanda har xuwa lokacin babu alamar momma ballantana su husna a wajen...!

musa kam na zaune ta gefen baa kansa a k'asa kamar t'sohon munafuki,hakanan yau yakejin kunyar iyalan gidan baki d'ayansu...! gani yake kamar kowa yasan abinda ya aikata a daren jiya...!

amni,umma dakuma anty suma na zaune acikin parlon tare da sauran yara,husna,sadeeya da momma kawai basanan,saikuma inoussa...!

kallon aliyu baa yayi da fuskar d'an bacin rai yace "maza tashi kaje ka kiramin mamanka da sauran k'annennka...!" domin ko shi ko irin tunanin lafiya d'innan basuzo ba baiyi ba...! saima gani yake kamar da gayya suka k'i zuwa sbd wani dalilinsu daban na shirme wai...!

cike da ladabi aliyu ya ansa da kansa ke k'asa tin d'azu yamik'e ya fice zuwa shashin momma,batare da yayi knocking ba ya tura k'ofar shashinnata,kuma cikin sa'a a bud'e take...!

d'akinsu husna ya fara shiga,inda ya tadda su sunyi daidai sai shek'a uban baccinsu sukeyi kamar babu gobe...! k'afofinsu ma dik sunyi gabas da yamma alamun baccin na masu dad'i sosai...!

fuskar husna yayi tozali dashi da yayi rud'u rud'u,alamun taci kuka ta k'oshi abinka ga farar fata babu sirri...!

gashin kanfa dasuke gazar gazar marasa laushi kamar irin yadda na india wa yake akoi yawa sosai amma kuma gazar gazar me dik sun cark'wad'e akan nata sbd bacci...!

juya akalar kallon nasa yayi zuwa ga fuskar sadeeya,inda ya fahimci itama ba k'aramin kuka tayi ba,dikdama dai ba kasafai ake gane hakan ba duba da yanayin fatar tata,sai wanda ya mata farin sani...!

ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauk'e,inda ya d'an d'aga murya ta yadda zasuji shi yafara k'iran sunayensu...!

sadeeya ce ta fara farkawa tana mut'sit'st'sika idanuwan masu kyau da t'sari dasuka koma d'an ja kad'an,alamun taci bacci kenan...!

ganin aliyu t'saye kanta yasata d'an waro ido kad'an,alamun mamakin abinda yakawo ya aliyun d'akinsu war haka...!

fahimtar hakan da yayi ne yasa shi t'sare gida cikin shan k'amshi yace "maza jeki ma momma magana baa ma k'ira a babban parlonsa yanxu...!"

bayi ta fad'a ta wanko bakinta kamin ta zumb'ula hijabi har k'asa ta fice zuwa d'akin momma...!

fitarta yasa aliyu takawa zuwa bakin gadon nasu yana sakin murmushi k'asa k'asa...! tattausan hannunsa yasa ya d'ago husna,wacce kamar ya d'ago babyn robber haka yaji sbd rashin nauyinta...!

wafce jikinta tayi ta mik'e zumbur tana sosa kai kamar wata munafuka wanda hakan yasa aliyu darawa kad'an yakuma gimt'se...!

"wato asma'u kema kin koyi rashin kunya ko...? kina jina wato ina k'iran sunanki amma t'sabagen rashin kunya kin gagara d'agowa ballantana ki ansamin sbd ga d'an iska na magana ko...?"

har yanxu kanta na k'asa batare data d'ago ba cikin rawar murya tace "kayi hak'uri ya aliyu bazan sake ba...!"

k'wafa yayi kawai alamun zamu had'u yayi hanyar k'ofa yanace mata "ki samo mu a shashen baa...!"

NIGERIA KO NIGERWhere stories live. Discover now