"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na kurman makahon da baya jin sauti a kunnensa, idanuwansa basa rarrabe masa lokutan jirkiɗewar yanayi. *** Shin mutane nawa ne irinta a duniya? Mutane nawa ne suke da ƙawa zuci irin nata? Mutane nawa ne ke ɗauke da baƙin mikin da ke damfare a zuciyar su irin nata? Ba ta sani ba! Amma tabbas idan rayuwa ta bata dama zata alimo lammuran su, zata kuma tsaya musu kamar yadda bishiya ke tsayuwa domin rassanta. Zata ƙawata rayuwarsu kamar yadda korayen ganye ke ƙawata idanuwa da lafiyar jiki. **** Cikin kowanne daren rayuwarta da fargaba take kwana da take ganin GOBE TA MATA NISA. Gani take kamar gari ba zai waye ba burinta ya cika, tamkar wani goben ba zai zo ba har goben cikar burinta ya zo, hakan yasa take yiwa ranar ɗaukar fansarta lakabi da GOBE DA NISA. Ina fatan kun shirya? Wa za ta ɗauki fansa? Akan wa za ta ɗauka? Shin burin ƙaramar yarinya da ba ta da ilimin boko ko sanin mai taimaka mata zai cika? Ba zan ce babu soyayya ko kauna a ciki ba, sai dai ba kamar sauran ba ne. Akwai ƙaddara, sadaukarwa, kauna d zazzafar so da aka kafata tun tushe. #Law #Shari'a #Judicial