Eighth

174 11 1
                                    

Page 8

"Kar ki damu, ki fito aikinki."
Barrister Waliy ya faɗawa Mariya yana kai hannu ya cire lock ɗin motarsa sannan ya juya yana kallonta.
Mariya ta buɗe murfin motar za ta fita ta dakata, cikin sanyin muryarta ta ce."To na gode."
Daga haka ta fita a motar, ba ta ko juya ba ta nufi cikin gida. Shi ma motarsa yaja yabar ƙofar gidansu.
...
Kamar kullum da sallama ta shiga cikin gidan, sai dai ji tayi da komawa tayi don hango Yaya Haydar zaune a bakin balcony saman farin kujera, saman cinyarsa laptop yana dannawa.
Ta san komawarta yin wani laifi ne, hakan yasa cikin tsoro da ya shigeta ta nufi falon. Tana isa wajensa ta durƙusa ƙasa saman gwuiwarta.
"Sannu da aiki Yaya." Ta faɗa kanta a ƙasa, ba ta saka ran zai amsa mata ba amma dolenta ta gaishesa.
Yaya Haydar da ya ji tamkar ya maketa yadda tazo ta sashi a gaba ta katse mishi aikinsa, ya ɗago ya wurga mata wani kallo ya mayar kansa kan laptop ɗinsa, tsaki ya buga cikin faɗa ya ce.
"Za ki bar kaina ko sai na canza miki kamanni."

Bai ƙarasa faɗa ba Mariya ta miƙe cikin sauri ta faɗa cikin falo. Nan ma da Abba ta ci karo zaune da yara babu Umma, ɗauke kanta tayi ta wuce ɗakinsu da sauri.
Abba da sauran yaran duk da kallo suka bita ganinta kamar a birkice, duk dawowar Yaya Haydar ya sake mayar da ita wata iri, ya sake canzata, kowa yana tsoransa amma na Mariya yafi nasu tsanani.
Mariya tana shiga da Haneefa taci karo zaune a gado, cikin sauri ta ƙarasa kusa da ita ta zauna tare da ɗaura kanta saman cinyarta. A hankali ta fara fitar da hawayen da take ɓoyewa cike da rauni.
Haneefa wayarta ta ajiye a bedside drower, ta ɗaura hannunta saman kanta ta zare mata baby hijab ɗinta tare da fara shafa mata gashin kanta da yake ɗaure a parke babu kitso mai tsantsi da tsayi, tausayin ƴar uwartan yana ratsata don tasan ba abu kaɗan bane ya sakata kuka haka ba, duba da yadda take da haƙuri da kawar kanta a komai.
Mariya sai da tayi kuka mai isarta ta fara sauƙe numfashi, ko ba komai ta ji zuciyarta tayi sanyi. Ta ɗago kanta tana kai hannu ta share guntun hawayenta.
Haneefa ta bita da kallo har ta gama sannan ta ce.
"Me ya faru ne? Wani ya miki wani abu a wajen aiki ne?"

Mariya girgiza kanta ta yi, ta kalli Haneefa cikin muryarta da take neman yin wani kukan ta ce.
"Yaah Haydar ne zai nema min sallama a wajen aiki. Ni kuma kin san yadda nake son aikin nan, shi ne burina da mafarkina."

"Kin masa wani abun ne?"
Haneefa ta tambayeta don ita kanta shaidata ce yadda Mariya take son wannan aikin nata, dalilinsa ya canza mata rayuwa da burinta na zama likita zuwa barrister.
Girgiza kai Mariya tayi tana kallon Haneefa.
"Wallahi babu abin da na masa, kawai don saura minti talatin a tashi na tashi, kuma ni duk gudun haɗuwa dashi ne."
Anan ta faɗa mata har yadda suka yi da Barrister Waliy, ta ƙarashe maganar tana share hawayenta ta ce.
"Ina tsoron Yaah Haydar sosai, zai iya dukana idan na fita."

Shuru Haneefa tayi ita kanta ta rasa mafita, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki shuru sai ajiyar zuciyar Mariya da take sauƙewa. Haneefa ta kalleta ta ce.
"Kin yi sallah?"

Mariya kai ta girgiza alamar a'a, ta miƙe ta rage kayan jikinta ta wuce bathroom. Ruwa ta watsa ta ɗaura alwala ta fito, ta samu Haneefa ta fita a ɗakin. Wardrobe ta nufa ta buɗe gefen nata ta ɗauki simple doguwar riga ta saka, ko bra da pant ba ta saka ba ta ɗauki hijab ta saka, ta nufi wajen da sallayarsu yake a shimfiɗe.
Sallar la'asar ta gabatar, tana cikin tahiya Haneefa ta shigo ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a ƙasa tana ajiye plate da ruwan hannunta.
Bayan Mariya ta idar ta juya tana kallonta, Haneefa ta tura plate ɗin da yake cike da abinci na semo da miyar zogale gabanta.
"Ki cinye tas kar ki rage, na san rabonki da abincin kirki kin manta balle naji labari wajen Ummi Aisha ko breakfast ba ki yi ba ki ka fita."

Mariya ba ta ce komai ba ta jawo plate ta fara ci cikin nutsuwa, sosai ta ci don ba ƙarya tana jin yunwa.
Ganin ta ci sosai yasa Haneefa gyara zama tace.
"Shi da Yaya Haydar waye oga a wajen aiki?"

GOBE DA NISA Where stories live. Discover now