Page 11
Cikin sanyin muryarta mai cike da tsananin tsoro ta yi sallama tana shiga falon, shuru falon tsit duk da akwai mutane a ciki, daga Abba, Umma, Yaya Haydar, Ummi Aisha babu sauran yaran. Can idanuwanta ya hango mata Haneefa a zaune ta haɗa kai da gwuiwa da alama kuka take.
Jikinta ne ya fara rawa, tsoro ya sake shigarta, ƙafafuwanta har rawa suke da ƙyar taja su ta nufi ɗakinsu don ta rasa ina za ta yi. Taku biyu ta yi taji mugun tsawar da ya nemi tarwatsa ƙwaƙwalwarta.
Cak ta tsaya tana juyawa lokaci ɗaya ta durƙushe ƙasa don ba ta da ƙarfin tsayuwa.
Haneefa wacce ta ɗago jin tsawar Abba ta rarrafa ta nufi wajen Mariya, jikinta ta faɗa tana fashewa da kuka. Kukan Haneefa ya karya zuciyar Mariya taji nata idanuwanta sun cika da kwalla, ranar da take guje musu kenan.
Falon shuru sai tashin kukan Haneefa, Mariya kam sai sharan hawayenta take waɗannan suka samu zuba.
Umma daga inda take ta taso ta ƙaraso wajensu, lafiyayyan mari ta sakarwa fuskar Mariya wacce ta ɗago kanta don ganin Umma tsaye a kansu. Babu shiri ta runtse idanuwanta jin zafin marin har tsakar kanta.
Kafin kiftawa da bismilla Umma ta rufe Mariya da duka, ta ko'ina dukanta take iya ƙarfinta tamkar an aikota. Mariya tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta kasa ta barwa Allah tana ci gaba da kukanta.
Haneefa ma kuka take iya ƙarfinta tana rokar Umma ta rabu da Mariya. Tsakanin Ummi Aisha da Yaya Haydar babu wanda ya yi ƙoƙarin tashi ya taimaka musu, haka Abba da yake ji bai ko motsa ba.
Sai da Umma ta yiwa Mariya lis sannan ta rabu da ita, lokacin da ƙyar take iya kukan.
Umma tasa kafa ta haureta sannan ta ce. "Don ke shegiya ce uban naki za ki yi wa sharri? Ubanki ne fa Mariya?"Abba daga inda yake zaune ya tashi, ya ƙarasa gabansu ya durƙusa saman ƙafafunsa. Ido cikin ido suka kalli juna da Mariya wacce ta ɗago kanta da ƙyar ta kalle shi, ya sakar mata wani shegen murmushi da kullum ya mata yana tsinka zuciyarta kafin ya ɓata rai lokaci ɗaya.
Ita kaɗai ta lura da hakan, cikin sauri ta yi ƙasa da kanta wani hawaye yana zubo mata a kumatunta. Maganganunsa ne suka sakata ɗago kanta da sauri ta kalle shi inda yake faɗin.
"Salon aikin kuma a kai na zai fara? Sharri za ki min Mariya? Ni za ki yi wa ƙaryar lalata miki rayuwa? Don kin ga jiya ban ɗauki mataki akan abin da ya faru ba. Me yasa ba za ki same ni mu yi maganar ba? Balle ma ina da niyar yi don ɓullowa abin akan yau idan na dawo, sai kuma na iske wannan takardar tuhumar mai cike da sharri. Amma tun da hakan ki ka nema mu haɗu a court."Umma cikin ɓacin rai ta bar gurin tana faɗin. "Ai ko duniya za su taru babu wanda zai yarda da hakan. Wannan abin kunyar har ina? Uba da lalata ƴarsa."
Abba daga faɗin haka ya yayyaga papers na hannunsa ya watsa a fuskar Mariya. Ya miƙe ya mata wani kallo ita da Haneefa ya ɗauke kansa ya ce.
"Na ba ku minti goma ku tattara komai naku ku bar min gida."Haneefa da Mariya an rasa mai magana a cikinsu, Haneefa kukanta ne ya karu yayinda Mariya take juya kalaman Abba a ranta.
Umma da take zaune kusa da Yaya Haydar wanda idanuwansa sun kasa sun yi ja, ya ma rasa ya zai fassara abun yasa bai tanka ba, ta kalle su cikin daka tsawa ta ce.
"Don uwarku ba magana ake muku ba, dangin mayu."Mariya idanuwanta ta runtse jin zagin da ta musu, ta miƙe ta miƙar da Haneefa tare da jan hannunta suka nufi ɗakin su. Zaunar da Haneefa ta yi saman gado, ita kuma ta miƙe ta ɗauki manyan akwati uku ta buɗe tare da fara ɗaukar kayansu tana zubawa a ciki, duk da ciwon da jikinta yake mata da kanta haka ta daure.
Babu abin da ta bari nasu a ɗakin, ta rufe akwatinan ta miƙar, ta koma wajen Haneefa da ta daina kukan sai ajiyar zuciya take sauƙewa.
Durƙushewa tayi a gabanta, ta kamo hannunta suna kallon juna. Mariya cikin sanyin murya cike da rauni ta ce. "Tashi muje.""Ina? Ina muke da shi bayan nan gidan iyayenmu." Haneefa ta faɗa cikin dashashshiyar muryarta tana neman yin wani kukan.
Miƙewa Mariya tayi ta ce. "Duk inda Allah ya nufa."
Haneefa miƙewa tayi ta ɗauki hijab nata ta saka saman kayanta na nursing. Don dawowarta kenan ta shiga ɗaki taji hayaniya ta fito, anan ta samu Abba yana lallashin Umma wacce take ta faɗa akan abin da aka aiko mishi, ganinta yasa suka rufeta da faɗa ko tana da masaniya akan abin da Mariya tayi.
Tuni ta fara kuka tana musu rantse rantse amma sun ƙi yarda musamman Umma, a cikin haka Abba ya ƙira Yaya Haydar ya dawo, hakan yasa sauran yaran suka watse, sai Haneefa da Ummi Aisha da ta kasa faɗin komai tana tattara dukkan abubuwan da suke faruwa a ƙwaƙwalwarta zuwa waje ɗaya.
Haka suka fito janye da akwatinan su, har lokacin suna falo a zaune Umma sai maimaita zance take, Abba yana faɗi ta kwantar da hankalinta su da suke da Yaya Haydar, balle ma ƙarya ne kowa ya sani.
Mariya da Haneefa babu wacce ta kalle su, suka ja akwatinan su suka fita a falon. A haka suka fita a gidan da suka taso, gidan iyayensu da suka basu dukkan gata da kulawa tsawon shekaru.
Suna janye da akwatunan su babu wacce tayi magana haka suka isa bakin titi, Mariya ce ta tara musu napep suka shiga. Bayan yaja ta sanar masa inda zai kaisu.
Haneefa dai bata ce komai ba har lokacin, ta jefa zuciyarta cikin tunani abubuwada dam.
Har ƙofa ya ajiye su, suka sauƙa Mariya ta cire kuɗinsa ta ba shi yaja napep ɗinsa.
Haneefa tana kallon Mariya ta ce. "A tunanina gidan Aunti Yahanasu zamu je."
YOU ARE READING
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...