Page 10
Mariya gani ta yi Yaya Haydar ya nufi ɗakinsu da ita, da sauri ta tsaya turus cike da tsoro, ba za ta iya kwana a ɗakin nan ita ɗaya ba, gani take za a sake zuwa mata.
Yaya Haydar kallonta ya yi ganin ta tsaya yaga kanta a ƙasa, murya a cunkushe ya ce. "Mene ne kuma?"Cike da tsoron me zai ce ta girgiza kanta, ruwan hawaye ya taru a idanuwanta ta kalle shi, da ƙyar ta yi ƙoƙarin kallon cikin idanuwansa ta ce."Ni ba zan iya kwana ni ɗaya ba."
"Ina Ummi Aisha da Haneefa." Ya faɗa yana juyawa ya dubi Umma da Abba, sai lokacin ya lura babu su duk hayaniyar.
Maganar Mariya yasa ya dubeta lokacin da ta ce. "Ba ta nan, Haneefa tana asibiti."Bai ce komai ba yaja hannunta suka nufi ɗakinsa da yake daga can ƙarshe. Ai Mariya ji ta yi da ba ta sanar da shi ba, jikinta rawa ya ci gaba da yi yadda yafi na farko. Ita tun da take ma za ta ce bai fi sau biyu ta shiga ɗakinsa ba, shi ma sai ba ya nan gudun ya ce ta mishi laifi ya daketa.
Tana ji tana gani babu damar mishi musu, haka ya buɗe ɗakinsa suka shiga. Ɗakinsa mai kyau da shi komai fari da blue, tsaf da shi kamar ɗakin mace sai ƙamshi da sanyin AC. Fagen tsafta Yaya Haydar ba baya ba ne domin yana da mugun tsafta da kyankyami.
Suna shiga ya sakar mata hannu ya nufi wardrobe ɗinsa, hakan yasa ta tsaya ta ka sa ƙarasawa ciki.
Yaya Haydar duvet ya ɗauka sabo ya dawo wajenta, miƙa mata ya yi babu musu ta karɓa da sauri. Gurinta ya bari yana fadin.
"Ki kwanta a saman sofa."Daga haka ya haye saman gado ya kwanta ya rabu da ita. Mariya ta kusan mintuna uku a tsaye, ta ka sa ko motsawa, mamakinsa take yadda yake nuna mata kulawa, abin da hakan bai taɓafaruwa tsakanin su ba.
"Za ki zo ki kwanta ko sai na ɗaukoki." Ta ji mugun tsawarsa da ya dawo da ita hankalinta, ta dube shi da sauri ta ga ya tashi zaune.
Kanta ta sunkuyar ƙasa ta ja ƙafafuwanta ta nufi sofar da yake facing ɗinsa ta zauna."Tashi ki fita min a ɗaki." Ya faɗa cikin tsawar da ya tsorata Mariya.
Da sauri ta kalle shi ta ga ya watsa mata wani kallo da manyan idanuwansa masu tsoratata, cikin azama ta ɗauke nata ta gyara kwanciyarta ta rufe jikinta har saman kanta, zuciyarta sai bugawa take da sauri na tsoron kasancewa da Yaya Haydar da kuma abin da ya faru.
Tasan Allah ne kaɗai ya ceceta daga afkuwar komai, da ba ta san ya za tayi ba, kuma ba ta san wa za ta tuhuma ba. Ba ta hayyacinta balle ta bambamce wanene, har ta gano ina ya shiga lokacin da ya gudu dalilin ihunta.
Tana wannan tunanin har bacci ya ɗauketa ba ta sani ba, sai dai cike da tsoro take yi don cikin baccin ma sai mafarki take.
Yaya Haydar bayan ya kwanta shi ma da ƙyar bacci ya ɗauke sa tuna abin da ya faru, yasan Allah ne kawai ya rufa asiri yau.
Ƙiran sallar asuba ya farkar dasu, shi ya fara miƙewa ya shiga bathroom ya ɗaura alwala ya fito. Wajen Mariya ya nufa ya tsaya a kanta, gaba ɗaya jikinta a rufe ta kudundune sai fuskarta da ta buɗe.
Innocent face nata fiyau, gashin kanta da yake a wargaje ya bazu a saman pillow wani a gefen fuskarta, ta ɗan turo ƙaramin bakinta alama ba ta jin daɗin baccin ko sanyi ya dameta duba da yadda ta dukunkune.
Ruwan hannunsa ya watsawa fuskarta da yasa Mariya firgita tana neman yin ihu. Ganin Yaya Haydar yasa ta nutsuwa tana yin ƙasa da kanta ganin ya watsa mata wannan kallonsa.
Gurinta ya bari bai ce mata komai ba ya fita a ɗakin. Numfashi ta sauƙe tana mamakin halinsa, duk abin da yaga dama yi yake babu ruwansa, idan mugunta ne yasan duk ta inda zai yiwa mutum.
Miƙewa ta yi ta ɗauki duvet ɗin da ta rufu da shi ta linke, ta ajiye a saman sofa ta bar gurin tana fita a ɗakinsa, sam ba za ta iya shiga mishi bathroom ba, salon ya zo ya samu na jibgarta ya ce ta mishi wani abun.
Ɗakin su ta buɗe ta shigar da ƙyar don tsoro, hakanma ganin asuba ne kuma kowa ya farka, bayan ta shiga key ta sawa ƙofa, tabi ɗakin da kallo yana nan yadda yake, sai lokacin mamakin yadda aka fitarta a ciki take. Tasan dai tana tunani da jiran ko Ummi Aisha za ta shigo har bacci ya ɗauketa, ba ta sake sanin komai ba sai lalubarta da taji ana yi tamkar a mafarkinta farka.
Kawar da tunanin tayi da sauri ta wuce bathroom, kulle ƙofa ta yi kafin ta yi fitsari ta yi tsarki ta ɗaura alwala ta buɗe ta fito. Rigar jikinta ta cire ta saka wani, ta ɗauki hijab ta saka ta nufi inda sallayarsu yake shimfiɗe ta fara gabatar da sallar.
Ko da ta idar ka sa komawa bacci ta yi, ta zauna tana azahar, ƙarshe ta miƙe ta ɗauki Alkur'ani ta fara karantawa. A haka har gari ya yi haske rana ta fito, ƙwanƙwasa ƙofa da aka yi yasa ta miƙe tana rufe Alkur'anin ta miƙe ta isa bakin ƙofa ta buɗe.
Umma ce tsaye, Mariya ta gaishe da ita cikin nutsuwa. Umma ta bita da kallo cike da tausayinta.
"Kin farka lafiya?" Ta faɗa tana amsa gaisuwarta.
Mariya kanta ta ɗaga alamar lafiya. Umma ta kamo hannunta suka shiga ɗakin, a bakin gado suka zauna tana binta da kallo ciki da waje kusan mintuna.
Murmushi Mariya ta yi ta ce. "Babu komai fa Umma."
YOU ARE READING
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...