Page 9
Mariya da ƙyar taja ƙafafuwanta zuwa gare su, yayinda zuciyarta ta ci gaba da bugawa. Abba da kansa ya buɗe mata gidan gefen Yaya Haydar.
Da murmushi a fuskarsa kamar koyaushe, yana kallon Mariya ya ce. "Shiga ku je Daughter."Ba ta iya musu ba haka ta shiga ta zauna a dadare, tabbas da tana da dama ko su biyu ne da Abba da tuni ta bijire mishi, amma tasan yin hakan tamkar yin gaggarumin laifi ne a gurin Yaya Haydar.
A murfin mota ta takure kanta waje ɗaya, motar banda ƙamshin mayen turarensa da sanyin ac babu komai ko karatu balle kiɗa. Tana ji ya yi hon mai gadi ya zo ya buɗe mishi get. Cikin sauri ya fizgi motar suka fita a gida.
Sun yi nisa a tafiya a tsakiyar hanya taga ya gangara gefen titi, ita dai bata ce komai ba don numfashi ma da ƙyar take ja balle wani motsi, tsoronta ɗaya kar ya mata maganar nema mata sallama a aiki da ya faɗa .
Yaya Haydar juyawa ya yi ya kalli Mariya, ta haɗe cikin baƙin coat nata da ƙaramin baby hijab fari, jakarta ma fari, dole ta burge mutum kasancewarta ƙarama kuma mace cikin shigar manya.
Gare shi kam ko kusa bata burge shi ba, baki ya taɓe yana ɗauke kansa daga kallonta.
"Fice min a mota don ni ba driver naki bane." Ya faɗa mata cikin muryar nan nasa mai tsoratata.
Kafin ya gama rufe baki Mariya ta buɗe ƙofar mota ta fice fit. Sam ba ta ji haushi ba, sai ma daɗi da nutsuwa da taji na ganin sun raba hanya.
Figar motar yayi yabar wajenta, ba ta ko juya ta kalle shi ba ta hau tsayar da napep, bayan ya tsaya ta shiga tana faɗa masa inda zai kaita.
Suna isa ta biya shi ta wuce ciki, can wajen fakin idanuwanta ya hango mata motar Barrister Waliy da Yaya Haydar. Ɗauke kanta tayi ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwarta wanda yake ɗaukar hankalin mutane, wanda kamar da gayya ko yanga take tafiyar.
Office ta nufa kai tsaye ta shiga musu da sallama, wanda suka ji suka amsa mata. Saman table nata ta nufa ta zauna da bismilla."Oga ya aiko ƙiranki." Faɗin ta gefenta mace.
Mariya cikin mamakin da ya bayyana a fuskarta ta kalleta ta ce.
"Ni ko wa?""Ke dai, ko ba ke ce Mariya ba?"
Ta faɗa mata tana mayar kanta kan computer nata.
Mariya jiki a sanyaye ta miƙe ta fita, ba ta tsaya ko'ina ba sai upstairs da zai sadata da office ɗinsa, haka ta zo ta gifta ta office ɗin Yaya Haydar a tsorace ce tamkar za ta gansa, inda aka yi rashin sa'a wucewarta ta yi daidai da buɗe office ɗinsa ya fito.
Ba ta lura dashi ba, don ta basa baya a lokacin ta buɗe office ɗin Barrister Waliy ta shiga da sallama.
Yana zaune kamar kullum yana aiki, ƙyam ta tsaya kanta a ƙasa ta ce. "Ina kwana sir"Sai lokacin ya ɗago kansa idonsa ya sauƙa a fuskarta. Karantar yanayin fuskarta ya yi duk da ta dukar idanuwanta ƙasa. Fuskarta kamar koyaushe babu son hayaniya sai alamun tsoro kaɗan.
Ɗauke kansa ya yi daga kallonta, ya sauƙe numfashi da bai san daga ina ya fito ba. Murya a hankali tamkar ba nashi ba har Mariya sai da ta ɗago, a lokacin ya ce.
"Koma aikinki, anjima zamu fita tare."Kanta ta mayar ƙasa ganin ya sake ɗagowa sun haɗa ido, a hankali ta juya ta fita. Office ɗinsu ta koma, computer nata ta kunna don fara duba aikin ciki taji ƙarar wayarta.
Barin abin da take yi tayi ta buɗe jakarta ta ciro, sabon lamba ta gani, kamar ba zata ɗauka ba sai kuma tayi tunanin ko ƙiran yana da mahimmanci, hakan yasa ta ɗauka tare da sallama a hankali.
Daga can ɓangaren taji muryar Nabeela cikin rawar kannan nata, ta amsa tana tambayarta aiki.
Murmushin ƙarfin hali Mariya tayi tana faɗin.
"Allahamdulillahi. Ya karatu?""Lafiya lau sai wahala. Ga Ammina ku gaisa kullum ina ba ta labarinki."
Nabeela ta faɗa daga ɓangarenta, kafin Mariya tayi wani yunkurin ko magana ta ji ta zare wayar, ta ji muryar Dattijuwar mace tana mata sallama.
A kunya ce cike da nauyinta Mariya ta amsa tana gaishe da ita. Ammi daga ɓangarenta tuni ta sake yabawa da nutsuwar Mariya, cikin farin ciki ta ce.
"Sai haƙuri da shiriritar Nabeela, kullum tana bani labarinki."
YOU ARE READING
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...