Three

184 13 0
                                    

    Page 3

  Motsi da Mariya ta yi ne ya farkar da Haneefa, ta ji Mariya ta rumgumeta, ba ta iya hanata ba ta sake ƙarfin riƙeta a jikinta da kyau, domin mafarkin da Mariya take yi ta fara sabawa dashi, sai dai har yau ta ka sa tambayarta dalili, ta bar abin a mummunar mafarki ne da kowa yana yi. Haka suka koma bacci.
  Da asubanin bayan sun gabatar da sallah basu koma ba, Mariya ta hau gyara kayanta, Haneefa ta tattare ɗakin tas, suka barwa Ummi Aisha shara tunda tana gida ita.
  Wanka suka yi suka shirya zuwa aiki suka fita, a falo suka samu Umma da sauran yara da suka shirya zuwa makaranta. Gaishe da ita suka yi yaranma suka gaishe dasu, daga nan suka yi breakfast suka mata sallama suka fita a gidan.
  A hanya suka rabu kowacce ta hau napep ta wuce wajen aikinta.
Mariya kasancewar yau tayi sauri sai bata damu ba, a cikin nutsuwa ta ƙarasa cikin office ɗinsu. Wayam ta gani alamar babu kowa amma kuma a buɗe. Agogon ɗaure a tsintsiyar hannunta ta duba taga takwas da kwata saura mintuna kafin tayi latti. Abin ne ya ɗaure mata kai da tunanin ko basu zo bane ganin lokaci yaja.
  Rasa mai bata amsa yasa ta taɓe bakinta ta fara ƙoƙarin zama, kamar daga sama taji maganarsa. "Me ya hanaki zuwa meeting?"

  A hanzarce ta juya taga Barrister Waliy tsaye a bayanta, suna haɗa ido ta ɗauke nata shi ma ya janye nashi yana barin wajen, dama wucewa yazo yi don zuwa meeting ya ga office ɗin a buɗe ya leƙa ko akwai wani a ciki.
  Mariya cikin sauri tabi bayansa don ba sanin ina za ayi tayi ba, kuma sam bata da labarin meeting ɗin sai dai idan yau da safe suka haɗa.
  Babban compress room taga ya shiga, ita ma tabi bayansa ta shiga bakinta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. Jama'a ta tarar a wajen har da wanda bata sansu ba a ma'aikatar, manyan baristoci da suka jima a aikinsu, alkalai har da su register, ga sabbi irinta. A cikinsu ta samu guri ta zauna cikin sauri.
  Tamkar ita ake jira ta zauna gurin ya ɗauki shuru. Barrister Hamza ne ya miƙe ya fara jawabi da musu sannu da zuwa, tare da karfafa musu guiwa akan aikinsu su jajirce sannan kar suji tsoro ko shakkar kowa. Haka ɗaya bayan ɗaya manyan suka gabatar abin da zasu yi.
Barrister Waliy shi ne a ƙarshe.   Cikin muryar nan nashi mai saka tsoronshi a zukatan jama'a ya fara nasa jawabin.
 Mariya duk yadda taso jurewa karta kalle shi kasawa tayi, a hankali ta ɗago kanta tana kai idanuwanta gare shi.
  Tamkar walkiya haka ya hango fararen idanuwanta suna kallon sa, kallonta ya yi suka haɗa ido. Mariya da sauri ta ɗauke idonta ta sunkuyar ƙasa jin yadda zuciyarta ta buga.
Barrister Waliy ma janye nashi ya yi yaci gaba da bayaninsa.
Awanni uku aka ɗauka ana abu ɗaya wanda duk su Mariya ake ƙarawa sani a fannin aikinsu a matsayinsu na sabbi. A wajen aka raba musu abin ci da abin sha aka ajiyewa kowa a gabansa, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara ɗauka yana sha.
  Mariya kasawa tayi ganin uban jama'ar nan ta ɗauki abu tasha, ji take ai zata kware.
Haka aka gama taron wajen ƙarfe sha biyu saura sannan aka sallame su, kowa ya miƙe ɗauke da abin da bai ci ya fita. Mariya kasa ɗauka tayi, tana miƙewa ta juya ta fice.
Duk abin da tayi idanuwan Barrister Waliy akanta, daga jiya zuwa yau ya karanceta tsaf, babu abin da yake hangowa tare da ita sai miskilanci zalla.
Miƙewa ya yi daga inda yake ya nufi inda ta zauna, hannu yasa ya ɗauki abubuwan da babu abin da ta taɓa ya fice a compress room ɗin. Office ɗinsa ya wuce kai tsaye, bayan ya shiga ya ajiye snack ɗin hannunsa saman tables sannan ya zauna. Landline na office ɗinsa ya jawo ya yi ƙira.
...

  Ƙara ne ya cika office ɗinsu na landline, dukkansu sun tsorata don ba a taɓa ƙiransu ba. Kafin ya yanke ɗaya namiji ya miƙe ya ɗauka da sauri yana kafawa a kunne, sallama ya yi a hankali kamar mai tsoro.
  Daga can ɓangaren Barrister Waliy jin muryar namiji ya amsa sallamar ya ba shi umarni.
"Ka turo min waccan mai white hijab, Barrister Waliy ne."

"Ok sir."
Ya faɗa yana zare wayar jin ya kashe. Wajen zamansa saurayin ya koma, ya dubi matan ciki yaga banda Mariya babu mai baby hijab fari, sauran gyale ne sun yi rolling, hakan yasa ya gane ita yake nufi.
"Barrister Waliy yana ƙiranki mai hijab."

GOBE DA NISA Where stories live. Discover now