Two

239 18 1
                                    

   Page 2

  Mariya Abaya baƙi ta saka wanda ba shi da wani kwalliya, sai farin hijab ƙarami da ya rufe mata kirji, takalminta baƙi mai tsini da handbag ɗinta ƙarami fari, ta yi kyau sosai duk da ba wani kwalliya ta yi a fuskarta ba, sai ɗaddaďan ƙamshin turare take mai saukar da nutsuwa a ruhi da gangar jiki.
  Tana gaishe da Umma ta fita a gida, bata tsaya gaishe da Abba ba. Napep ta tara sai court. Tana isa office ta wuce, ta samu maza ukun sun zo da mace ɗaya ita ma cikin Abaya kamar yadda take, alamu dai ita ma ba ta son suit ko ba ta saya ba.
  Da sallama ta shiga musu suka amsa, daga haka ta nufi table ɗinta ta zauna. File ɗin jiya ta ɗauka ta fara dubawa, yana nan tsaf yanda ta bari, abu kaɗan ya rage ta gama haɗa tambayoyi da za a gabatar a court, amma kafin nan sai ta yiwa wanda suka kawo ƙarar tambayoyi.
  Dafe kanta ta yi don dole sai taje, kuma dole ta sanar da wanda ya bata duba shari'ar cewa za taje. Ƙaramin tsaki tayi ƙasa ƙasa sannan ta miƙe, ta ɗauki file ɗin tare da handbag ɗinta ta fita.
  Zagaye wajen ta fara tare da duba office-office ko za ta samo office ɗinsa, sai dai kaf gurin irinta ne ƙananan ma'aikata. Har ta haƙura sai kuma tayi tunanin duba saman bene, hakan yasa ta nufi can.
  Tun daga harabar wajen yake da kyau da tsari, sosai gurin ya haɗu,  ga office a jere reras. A hankali take tafiya tana duba kowane office da taga sunan mai shi a rubuce a sama cikin style na calligraphy, cak ta tsaya ganin sunan da ba tayi tsammanin gani ba, ta kurawa jikin ƙofar ido tamkar wacce za ta hango shi tsaye, abubuwa dayawa suka fara kai kawo a zuciyarta da ƙwaƙwalwarta da ya haddasa mata bugun zuciya.
  Takun mutane da taji ya dumfarota yasa ta yi azamar ɗauke idonta, ta cije lips ɗinta jin yadda zuciyarta ta juya. Kafafuwanta taja tabar gurin cikin wani irin yanayi da ta tsinci kanta.
  Office ɗaya ta tsallake sannan ta samu wanda take nema, bakin ƙofa ta ƙarasa ta ƙwanƙwasa da ƙyar saboda tsoron da taji ya maye gurbin abin da taji yanzu. Tsawon mintuna ba'a amsa ba, hakan yasa ta sake ƙwanƙwasa. Da ƙyar ta iya jiyo muryar na ciki ya bata umarni ta shiga.
  Tura ƙofar ta yi a hankali tana shiga, bakinta ɗauke da sallama yayinda bugun zuciyarta ta ƙara ƙarfi. Tsaye ta yi ƙyam bayan ta daidaita nutsuwarta, ta ɗago a hankali ta kalli wajen da yake zaune, kansa a ƙasa yana danna computer tamkar bai san da shigowarta ba.
  Tsawon daƙiƙa ita ta kasa magana shi bai ɗago ba ya tambayeta dalilin zuwanta ba, sai shakar ƙamshin turaren juna suke kowanne a zuci yana mitar na juna ya dame sa.
Mariya har cikin ranta jira take ya nemi dalilin zuwanta a matsayinsa na oganta, ya bata dama ta faɗi abin da take tafe da shi. Shi kuma mamakin rainin hankalinta yake da tazo ta sa shi a gaba ta kasa faɗin komai.
  Fuska ya sake tamkewa ya ɗago ya mata kallo ɗaya ya mayar kansa kan abin da yake, tamkar ba zai furta komai ba da ƙyar ya buɗe baki ya ce.
"Idan ba ki da abin faɗa ki bar kaina."

  Jin muryarsa yasa Mariya ɗagowa ta kalle shi, taga tamkar ba shi ya yi maganar ba. Matsawa ta yi ta ajiye file ɗin hannunta a saman table ɗinsa.
"Da ma nace zan je na musu wasu tambayoyi ne."

"Wani case ne?"
Ya tambaya yana barin abin da yake ya ɗago ya kalleta.
Kanta ta ƙara rissinarwa ta ce.
"Na yarinya da tsoho da suke gidan haya tare."

  Kafin ta gama bayanin ya jawo ya buɗe, ya fara karanta abin da ta rubuta ganin yadda take fitar da harafi ɗaiɗaiya cikin sanyin murya. Bayan ya gama ya rufe ya ce.
"Babu buƙatar wannan, amma idan ta kama za kiyi hakan. Tambayoyin da kika tanada su kaɗai zasu yi aiki a court, don haka kin gama naki."

  Mariya jin abin da ya faɗa yasa ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya miƙe. Numfashi ta sauƙe a hankali, sannan ta ce.
"Ok sir."
Ta juya ta fara ƙoƙarin barin office ɗin, har ta kama handle taji ya ce."Na sallameki?"

  Dakatawa ta yi ta dawo baya ta tsaya, kanta a ƙasa tana mamakin wannan isa da mulki, sai wani muzurai yake mata.
  Barrister Waliy ajiye file ɗin da ya dauko ya yi saman table ya tura gabanta.
"Ki je ki duba wannan. Sabbin case ne ba kamar wanda kika gama ba, duk da shi ma sai na zauna na duba."

GOBE DA NISA Where stories live. Discover now