Seven

159 9 0
                                    

Page 7

   Manyan idanuwanta ta ɗago ta kalle shi da sauri, ta ga shi ma ita yake kallo da murmushi ɗauke saman fuskarsa, babu shiri ta kawar idanuwanta don yadda ya haddasa mata ci gaba da bugun zuciya bayan wanda take ciki.
Mariya jiki na mugun rawa ta miƙe, ta ɗauki plate ɗaya ta buɗe flask ta zubawa Abba ta ajiye a gabansa. Haka ta jawo wani ta zubawa Umma ta ajiye mata, ta ɗauki wani za ta zubawa Yaya Haydar ta ji muryarsa yana faɗin.
"Haɗa min tea."

  Bari ta yi ta ɗauki cup ta hau haɗa mishi daidai yadda yake so, bayan ta gama ta ajiye mishi a gabansa. Ita ma black tea ta zuba ta zauna, ta ɗauki teaspoon tana juyawa don ba ta da ƙarfi ko nutsuwar cin abinci a gaban mutane biyun. Haka sauran yaranma da ƙyar suka zuba suka hau tsakura.
Abba ya kalleta yana murmushi ya ce. "Na fa kula ba kya son cin abinci yarinyar nan."

  "Faɗa mata dai."
Umma ta faɗa ita ma. Kowa dai ya yi gum da bakinsa ganin dodon nasu yana nan.
  Mariya ganin suna shirin kafa chapter nata yasa ta miƙe, ta ɗauki handbag ɗinta tana faɗin.
"Sai anjimanku."

"Tsaya ku tafi da Yayanku, shi ma wajen aikinsa zai fara fita yau."
Abba ya faɗa yana mayar kallonsa kan Yaya Haydar da ya ƙara haɗa fuska sosai.
  Girgiza kai Mariya ta yi cikin tsoro, haɗa tafiya da Yaya Haydar gani take zai sumar da ita ko ya jefarta a motar. Da ƙyar ta buɗe baki za tayi magana taji maganarsa ya ce.
"Abba sai anjima."

  Daga haka ya bar wajen, cikin sanyin jiki Mariya tabi bayansa. A waje ta hangosa cikin motarsa an buɗe mishi get, tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da shi ta ga yaja motarsa ya fice. Ko kaɗan ba taji haushi ba sai ma farin ciki da taji na ganin ya tafi ya barta.
  Haka ta fito ta tari napep ta nufi office, bayan ta isa ba ta iya shiga office ba sai da ta shiga wajen sayar da snack ta saya da drinks, sannan ta wuce office ta zauna taci kafin ta fara aikinta.
  Sallama suka ji daga bakin ƙofar, gaba ɗayan su suka ɗago har Mariya jin tasan muryar. Da Nabeela suka haɗa ido, tana mata murmushi ta ƙaraso table ɗinta taja kujera ta zauna. "Sannunki da aiki."

  Babu yabo ba fallasa Mariya ta amsa mata, hakan ya ƙara burge Nabeela tana jinjinawa ajin yarinyar.
Cikin murmushi ta sake faɗin.
"Kin san menene? Tun da muka rabu nake tunaninki, haka kawai kike burge ni."

  Sai lokacin Mariya ta saki murmushi mai sanyi, ta kalli Nabeela da ta kura mata idonta irin na Barrister Waliy sosai.

"Na gode sosai." Ta faɗa tana sunkuyar kanta ta ci gaba da abin da take yi.
Nabeela wayarta ta ciro, ta ajiye a gaban Mariya tana faɗin.
"Saka min lambarki muna waya, na zo jin wata shari'a ce na samu an ɗaga shi ne nace bari na ƙaraso mu gaisa."

'Naga ta kaina.' Faɗin Mariya a zuciyarta, a fili ta murmusa ta ɗauki wayar Nabeela ta saka mata lambarta ta miƙa mata wayar.
  Karɓa Nabeela tayi ta ce. "Sunan kawar tawa. Ni sunana Nabeela Abubakar ƙanwa ga Barrister Waliy Abubakar. "

"Mariya Harun."
  Faɗin Mariya domin ta gano ƙanwarsa ce duba da ranar da kuma kammanin su.
  Miƙewa Nabeela ta yi tana faɗin.
"Sai mun yi waya, bara na tafi kar Yaya ya ƙira gida ya ji ban isa ba nayi laifi."

  Murmushin ƙarfin hali Mariya ta yi tana faɗin. "Allah ya tsare."

   Nabeela ta amsa da amin ta fice cikin farin ciki ganin plan nasu ya fara tafiya cikin shiri.
  Bayan fitar su Mariya ta ci gaba da yin aikinta, ba ta damu da ƴan wajen da suka fara maganganun ƙasa ƙasa ba.
  Ita damuwar da take ciki ya linka shekarunta, gaba ɗaya ta rasa mafita a abin da take son cimmawa kafin lokaci ya ƙure mata, dole ta aiwatar da komai cikin sauri kuma tana neman taimako.
Sai dai na waye? Wa zai taimaka mata? Tsawon shekaru ta rasa wa zata tunkara shi yasa ta ka sa cika burinta.
Barin abin da take yi ta yi ta dafe kanta, a hankali ta furta. "Allah ka cika min burina."
...

GOBE DA NISA Where stories live. Discover now