Page 4
A facing ɗinta ya zauna, yana jifanta da murmushin nan nasa mai tsinka zuciyarta ya amsa gaisuwarta, tare da tambayarta ya aiki.
Mariya kanta kawai ta girgiza alamar lafiya ta ka sa yin magana. Gaba ɗaya a takure take da zaman, hakan yasa ta miƙe tana cewa.
"Sai da safenku."Umma ta amsa ta bita da kallo, ta juyo ta kalli Abba da ya bita Mariya da kallo ta ce.
"Wannan shegen miskilancin yarinyar nan naka ya ishe ni, ace mutum magana yana ba shi wahala."Abba da yabi Mariya da kallo harta shige ɗaki ya juyo ya kalli Umma jin abin da ta faɗa, fuskarsa da murmushi ya ce. "Abin gado ne."
Umma baki ta taɓe ta miƙewa.
"Sai dai a wajenka." Tana faɗa tabar wajensa ta nufi fridge ta ɗauko mishi ruwa, sauran yaranma ɗaya bayan ɗaya suka miƙe suka shige ɗaki. Shigowarsa dama yasa gaba ɗaya suka nutsu, sallamarsa ne ta katse musu surutun su.
Ummi Aisha da ta shiga ɗakinsu ta zauna kusa da Mariya da take kwance saman gado idanuwanta rufe, kallonta tayi tana faɗin.
"Kinji kin ƙara taɓa Umma. Wai don Allah bakinki ba ya tsami?"Mariya idanuwanta ta buɗe tana kallon Ummi Aisha, tamkar ba za ta tanka ba, tayi murmushi da ya bayyana dimples ɗinta sannan tace.
"Ina yi mana, kawai dai bana saka kaina hiran da bai shafe ni ba, sai kuma wanda bai game ni ba nake ƙin tankawa.""A wajen aikinma haka kike musu?"
Ummi Aisha ta tambayeta ganin yau ta buɗe baki ta mata magana mai tsayi.
Girgiza kai Mariya tayi ta rufe idanuwanta, tasan idan ta biyewa Ummi Aisha sai su kwana surutu.
Fitowar Haneefa a bathroom yasa Ummi Aisha miƙewa ta shige bathroom don yin wanka. Haneefa bayan ta saka kayan baccinta ta zauna kusa da Mariya, buɗe ido Mariya ta yi ta kalleta ba tace komai ba.
Haneefa ta mata murmushi ta ce.
"Me ya faru naga kamar kina da damuwa."Girgiza kai Mariya tayi sannan tace.
"Babu komai, gajiya ce."Jin abin da ta faɗa yasa Haneefa hawa gadon sosai, ta kwanta gefen Mariya bata kara cewa komai ba.
Ita ma Mariya kwanciyarta ta gyara tana matsawa tsakiyar gado ta barwa Ummi Aisha ƙarshe don dama koyaushe ita ce a tsakiya sai idan Haneefa bata nan.
Dalilin yawan mafarkan da take masu firgitata ta farka yasa Haneefa take sakata tsakiyarsu, don da zaran ta farka itama sai taji wani lokaci, watarana kuma bata jinta har ta yi ta koma, shi yasa idan take da night duty kullum tunaninta yar uwartan ta kwana.
Haka Ummi Aisha ta fito ta gama shirin baccinta ta kashe wuta ta haye saman gado ta kwanta. Addu'a suka yi kafin dukkansu su kwanta.
Cikin ikon Allah yau har gari ya waye Mariya ba tayi mafarki ba balle ta farka, hakan ya musu daɗi dukkansu duk da dama takan jera kwanaki uku zuwa huɗu ba tayi ba.
Bayan sun gabatar da sallah kamar kullum suka tattare ɗakin suka shirya suka fito, Umma suka gaishe suka yi breakfast kafin su fita. Ɓangaren Abba suka nufa suka gaishe dashi wanda da farko Mariya kamar kar taje, amma ganin Haneefa yasa ta binta.
Bayan ya musu fatan alheri kafin su fito suka bar gida kowacce ta kama gabanta zuwa wajen aikinta.
Mariya yau ma akan case na Isah Hamza ta wuni, har aka tashi ta musu sallama ta dawo gida.Haka kwanakin suka tafi a rayuwar ahlin kamar baya.
Mariya ta dage da zuwa aiki da take jajircewa akai don cikar nata burin, basu kara haɗuwa da Barrister Waliy ba.
Bai nemeta ba akan aikin da ya bata, hakan yasa ta kwantar da hankalinta take bin komai daki-daki wanda har ta kusa kammala na zargin Isah Hamza da ake yana sata a unguwar su, saura ɗayan.
A haka har aka shiga weekend, mai maimakon su huta amma Ummi Aisha ta kwakulo musu tafiya gidan ƙanwar Abba yini. Mariya haushinta taji sosai don ita kam burinta ta huta a weekend ɗin nan, kuma idan ta zauna ita ɗaya za a bari domin har su khadeeja da suke yara zasu je.
Dole yasa ta shirya cikin riga da skirt na lace blue da ash, ta yi amfani da ash mayafinta, sai ƙaramin handbags ɗinta kalar takalminta. Tayi kyau sosai domin Mariya akwai kyau da tsarin halitta mai burgewa, wanda da dama shi yake fisgar jama'a.
Haka Haneefa irin lace nata ta saka sai banbancin color, na Haneefa brown da mint green maimakon color irin na Mariya, sai kamminsu ya sake fitowa.
Bayan sun gama shiryawa Abba ya bada mota driver ya kaisu har gidan Aunti Yahanasu, tayi murnan ganin yaran yayan nata sosai, suka haɗu da yaran gidan sai suka cika gidan sosai da hayaniya, kowa ya kama abokinsa suna kuskus abinsu.
Mariya, Haneefa da Ummi Aisha su ma gefe ɗaya suka haɗe da ƴan biyun Aunti Yahanasu suka kafa cafta. Hira suke sosai, da ƙyar Mariya tayi ƙoƙarin sakewa take saka baki gudun su kafa nata chapter na rashin son magana.
Hakan ko ya musu daɗi har Hassana sai da ta tanka ta ce.
"Yau za ayi ruwa da kankara."
YOU ARE READING
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...