Page 12
Last Free PageShuru da Barrister Waliy ya yi ya fara takurawa Mariya, ga ƙamshin turarensa duk ya cikata tamkar babu nata a gurin, gare shi ma hakan ne ba ta sani ba amma ya basar.
Yana sunkuye yana ta rubuce-rubuce a file sabo, wanda bayan shigarsu office ɗinsa ya ɗauko ya fara yi.
Tsawon mintuna goma ya gama ya ɗago, ya kalla Mariya da take zaune a ɗaya daga cikin kujerun office ɗin, kanta a ƙasa tana wasa da zoben yatsarta.
Sunanta ya ƙira a hankali sannan ya ci gaba da faɗin. "Akan case naki ne, yau da safe na samu ƙira daga court ta bamu ranar zama sati biyu mai zuwa. Don haka zamu fara haɗa dukkan shaidu, so ina buƙatar waɗanda kike dasu domin tattara bayanai da ɓullowa shari'ar."Kai Mariya ta jinjina cike da farin ciki, cikin sanyin muryarta ta ce.
"To Allah ya kaimu. Sai dai babban shaidata yana gidanmu kuma mun bar gidan jiya sun koremu, tashin hankali da muke ciki yasa na manta dashi.""What? Kuna ina? Ke da wa?" Barrister Waliy ya jera mata tambayoyi cikin sauri, cike da mamakin ta ya iyaye zasu kori yaransu a gida, don kawai an kama su da wani laifin daban bai kamata su aikata musu hakan ba.
Mariya cikin raunin murya na neman yin kuka ta ce. "Ni da ƴar uwata my twins sister, muna gidan Auntinmu ƙanwar mahaifiyarmu."
Dafe kai Barrister Waliy ya yi, mamaki yake wannan wani irin iyaye ne suka samu. Ya jima a haka ya ɗago ya kalla Mariya wacce ta gama share hawayenta.
Cikin kwantar murya ya fara ce mata. "Kin ga ki daina zubar da hawayenki, Allah zai kawo muku mafita balle ma in sha Allah ina tare daku. Maganar shaida kuma dole ki ɗauko, amma ta ya? Kina ganin ba zasu koraki ba idan kika koma?"Shuru Mariya tayi don ba ta da masaniya, duk gidan babu wanda ta yarda dashi shi yasa tsawon shekaru ta ɓoye inda babu mai gani ko da Haneefa ce.
"Magana nake miki?" Barrister Waliy ya faɗa ganin ta faɗa tunani.Kallon shi tayi sau ɗaya ta sunkuyar kanta ganin shi ma ita yake kallo, a hankali ta ce. "Gaskiya sai dai da sassafe kamar ƙarfe shida, lokacin duk suna baccin safe."
"Gobe kina da free?" Ya tambayeta yana miƙa mata wayarsa ya ci gaba da faɗin. "Saka min contact naki."
Babu musu ta karɓi hadaddiyar wayarsa ta saka mishi lambarta, tasan babu abin da zai yi da shi sai don taimaka mata.
Bayan ta saka ta miƙa masa, ya karɓa yana saving ya ce. "Shike nan ki koma bakin aikinki, sai mun yi magana.""Na gode sosai."
Mariya ta faɗa tana tashi, daga haka ta juya ta fita.
Tana fita office ɗinsu ta wuce ta shiga ta zauna bayan ta musu sallama. Ƙoƙarin kunna computer na gabanta ta fara ta ji ƴar gefenta ta ce. "Barrister Aliyu Haydar yana nemanki."A mutuƙar razane Mariya ta kalleta, ita kuwa ta ɗauke kanta cike da jin haushin Mariya da ya fara kamata, ba ita kaɗai ba hatta ƴan gurin ganin baristoci biyun masu ji da miskilancin da kwazo tana neman shige musu, musamman na yau da Barrister Aliyu Haydar ya ƙira a turo mishi Mariya, mutumin da baya ɗaukar raini ga shegen girman kai, wani lokaci har gwara Barrister Waliy akansa.
Mariya wacce tana cikin tunanin me ƙiran Yaya Haydar yake nufi a gareta sam ba ta san suna yi ba, tasan ƙiran Yaya Haydar gareta mugunta ce ko neman tarwatsa mata shirinta, ko ya tsoratata ta janye niyarta.
Tuna haka yasa ta ji idan dai haka ne ba zata je ba, tana da Barrister Waliy zai tsaya mata ya taimaka mata ba zata sake haɗa ko hanya da Yaya Haydar ba, har ya samu damar mata wani muguntar.
Haka ta zauna ta fara aikinta duk da ta ka sa cire tunanin kar Yaya Haydar kar ya zo ya sameta, amma har azahar ta yi suka fita zuwa masallaci shuru.
A nan ta ga babu motarsa ma alama ya fita, hakan yasa taji nutsuwa. Bayan sun yi sallah suka nufi cafeteria suka ci abinci, sannan suka koma office.
Har ƙarfe huɗu ta yi suka tashi ba ta sake ganin alamar Yaya Haydar ba, haka ta fita ta wuce gida.
Bayan isarta ta samu Zakiyyah ta dawo ban da Haneefa. Ta gaishe da Aunti Babie ta wuce ɗaki, wanka ta yi ta gabatar sallar la'asar ta fito.
Dining ta nufa ta zuba abinci taci cikin nutsuwa, bayan ta kammala anan ta zauna ganin yara a falo da Zakiyyah suna kallon wani film mai daɗi da ya ɗauki hankalin su, ita ma kallon ta fara.
Ƙiran sallar magriba ne ya miƙar dasu ba a gama ba, suka gabatar suka dawo suka ci gaba. Har ƙarfe bakwai da rabi sannan aka kammala, sai lokacin kowa ya nemi abincin dare banda Mariya da ta ɗauki fresh milk tasha mai sanyi, daga nan ta wuce ɗaki ta kwanta.
Tana kwance tana sakawa da warwarewa har aka ƙira isha'i ta miƙe tayi ta sake komawa ta kwanta, a haka bacci ya ɗauketa ba ta san lokacin da Zakiyyah ta shigo ba.
Ƙarfe biyun dare da minti goma Mariya ta farka a mutuƙar gigice, tare da faɗin. "Bana so don Allah ka bari."
CITEȘTI
GOBE DA NISA
Dragoste"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...