BismillahilRahmaninRaheem
Page 1
Ahlin gaba ɗaya farin ciki suke da murna domin samun wannan karuwar abin da basu zata ba, wanda suke ganin abu ne mai wuya samun shi, duk da ya kasance murnar wasu a ciki suke hakan bai sa sun bayyana a fuskarsu ba suka bari a zuci. Ƙaramar walima aka haɗa a gidan, aka ci aka sha kowa na taya wacce abin farin cikin ya sameta murna.
Idan ka dubeta kuwa yadda kyakkyawar fuskarta take annuri zai ba ka tabbacin tana farin ciki da wannan rana, burinta ya cika saura mafarkinta da kaso sittin shi ne abin da ya taimakawa rayuwarta tsawon rai. Jama'a da dama suna ganin hakan ba mai yiwuwa bane saboda kankantarta kuma mace ce.
Sunanta ta ji an ƙira, ta juya tana amsawa wacce ta ƙirata cikin sanyin muryarta na marar son hayaniya. Kanwar mahaifiyarta ce Aunti Babie, cikin murmushi ta ce.
"Zamu wuce gida Mariya, Allah ya taimaka yasa a shiga a sa'a."Mariyatul Kibdiyya cikin muryarta mai daɗin sauraro ta ce.
"Amin Aunti na gode. Sai na zo muku.""Babu komai, ai ke yanzu babu zama."
Aunti Babie ta faɗa tana saka yaranta a gaba suka fita a falon, Zakiyyah tabi bayan mahaifiyarta tana yiwa sauran ƴan matan sallama sai bayan kwana biyu.
Suna fita Mariyatu, Haneefa da Ummi Aisha suka gyara falon ganin yadda aka mayar a hargitse.
A haka kowa ya watse wanda suka zo tayata murna aka bar ƴan gidan. Suna gamawa ɗakinsu suka wuce, kai tsaye bathroom suka yi rige rigen shiga ganin magriba ta yi, alwala suka yi suka gabatar da sallah, kasancewar cikinsu a cike yake basu bi takan abincin dare ba kowace ta nemi guri ta zauna tana ɗaukar wayarta.
Haka suka zauna suna chat suna hira jifa jifa wanda duk Haneefa da Ummi Aisha ne, Mariya daga umm sai a'a nata, haka har dare ya yi suka gabatar da sallar isha'i. Bayan sun idar suka fita suka yi wa Umma sai da safe suka dawo ɗaki suka kwanta.Washegarin ƙarfe bakwai da rabi cib Mariya da Haneefa suka gama shirinsu na tafiya aiki. Mariya yau ne ranar farkonta, wanda dalilin samuwar aikin yasa ahlin haɗa mata walima jiya a gida suka zo yi mata murna.
Haneefa cikin uniform din nurses fari, ta yi kyau abinta.
Mariya kuwa cikin bakin doguwar riga baki, sai baby hijab fari da ya rufe kirjinta, ya haska farin fatarta ya fito mata da tsantsan kyawunta, duk da bai kamata ba hakan baya hana mutum hango zubin halittarta. Fuskarta fiyau babu wani kwalliya sai hoda da man baki da ta sanya don girmama dokokin aikinta.
Bayan sun gaishe da Umma a gurguje suka hau yin breakfast da mai aiki ta gabatar jera a dining.
Haneefa ce ta fara gamawa ta miƙe, ta kalli Umma da take zaune ta ce.
"Umma wai Abba bai farka ba.""Yana falonsa."
Umma ta faɗa daga inda take zaune tana duba wasu kayyaki da aka kawo mata.
Haneefa ta juya kalli Mariya ta ce.
"Ki gama muje gaishesa sai mu wuce."Miƙewa Mariya ta yi don ta kammala kenan, ta ɗauki handbag ɗinta tabar gurin. Ganin haka Haneefa yin gaba Mariya tabi bayanta zuwa falon Abba, a hanya suka haɗu suka ƙarasa.
Da sallama suka shiga gaba d'ayan su, Abba ya amsa musu yana zaune saman kujera hannunsa ɗauke da remote yana kallon labaran safe, yayinda yake sanye da jallabiya. Guri suka samu suka zauna, cikin ladabi suka gaishe dashi. Da fara'a a fuskarsa ya amsa musu tamkar koyaushe. Suka miƙe Haneefa tana cewa.
"Abba zamu wuce aiki.""A dawo lafiya."
Ya faɗa yana binsu da kallo suka fita, musamman Mariya da yaga kwalliyarta ya karɓeta.
Bayan fitar su adaidaita suka shiga kowacce ta wuce wajen aikinta.
Mariya tunda ta hau mashin har ya sauƙeta bakinta da addu'o'i, yau ne ranar farkonta aiki bayan interview da suka sha aka tantance aka zaɓa masu ƙoƙarinm aka basu aikin, hakan yasa duk a tsorace take.
Da bismillah ta saka ƙafarta cikin ma'aikatar, tana shiga ta fara bin harabar wajen da kallo. Ba wani ma'aikata bane babba amma tsarin gini ya fita mai kyau, ginin zamani ne hawa ɗaya bene. Kallon wajen ta ci gaba da yi idanuwanta suka hango mata waɗannan suka yi interview tare.
Cikin sauri ta ƙarasa wajen su, ta musu sallama suka amsa mata daga nan ta ci gaba da tsayawa. Mintuna biyar da tsayuwarta taga kowa yana gyara tsayuwar sa, ita ma nata ta gyara tana kai kallonta kan mutanen da suka dumfaro su.
Mutumin da ya musu interview ne tare da wasu biyu, wanda ɗayan lokacin da ake mata interview yana office din amma bai ko kalli inda take ba balle ya tofa, sai ɗayan da bata san shi ba.
Tsit gurin ya ɗauka bayan isowar su, baƙon fuskar cikin su ya musu sallama tare da fara gabatar da kanshi gare su da sauran cikin harshen turanci.
"Ni sunana Barrister Hamza, wannan Barrister Waliy Abubakar sai wannan oga kwata kwata Judge Nuhu. Barkanku da zuwa wannan kotun, da fatan za ku yi aiki tukuru kamar yadda ya kawoku, wanda muke sa ran kuma nan da shekara ɗaya kun zama baristocin kanku, ku fito gaban court a dama daku a fafata."
ESTÁS LEYENDO
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...