Page 6
Da sallama ya shigo babban falon gidansu cikin shirin fita aiki kamar kullum, da mahaifiyarsa da ƙannensa mata da suke zaune ya fara cin karo, suna ganinsa suka gimtse dariyar da suke, musamman Nabeela da ita ce kan gaba na dalilin dariyar nasu da yake cike da farin ciki.
Ciki ya ƙarasa sai lokacin suka lura da wacce take bin bayansa, ita ma cikin shirin fita nata aikin take. Take fara'ar fuskarsu ta ɗauke banda na Ammi.
Kujera Waliy ya samu ya zauna, wacce suka shigo tare ta zauna a hannun kujeran da yake. Kamar kullum shi ya fara gaishe da Ammi sannan ita, duk da abin yana sosa ran Ammi haka ta amsa don karta nunawa Waliy ɓacin ranta akan Rumana. Sannan su Nabeela suka gaida su.
Rumana ce ta fara miƙewa, ta kalli Waliy tana gyara siririn gyalen kanta tace. "B zan yi latti fa, mu tafi."Miƙewa ya yi, ya kalli Ammi da ta ɗauke idonta ya ce. "Ammi zamu wuce."
"Allah ya kiyaye ya yi jagora." Ta faɗa musu tana dawo da dubanta kansu.
Murmushi Waliy yayi da ya ƙara fitar da kamilalliyar fuskarsa mai tsorata mutum, ya juya ya fice yabi bayan Rumana da tuni ta fice.
A harabar gidan ya sameta jingine a jikin motarta, wajenta ya ƙarasa ya tsaya a gabanta. Fuskarsa a haɗe kamar ba yanzu ya gama murmushi ba. Wani kallo ya aika mata sannan ya buɗe baki ya ce.
"Wai yaushe za kiyi hankali Ruman? Zamu ɓata ina faɗa miki idan ba za ki ɗauki mahaifiyata da daraja ba.""Me nayi B? Naga dai gaisuwa ce na gaisheta." Ta faɗa da Hausarta da ba ya fita tana kallonsa. Don ita gaskiyarta ba ta ga wani abin da tayi ba, amma shi kullum faɗarsa bata ba wa mahaifiyarsa daraja. Kuma duk safiya tana shiga ta gaisheta sai kuma washegarin da safe, ita ma yanayin aikinta baya barinta wuni a gidan sai yamma take dawowa, ta dawo kuma fta gaji.
Tsakin Waliy da barinsa wajenta yasa ta kallonsa taga ya wuce wajen motarsa. Kwafa tayi ta buɗe nata ta shiga, tana zaune zai zo ya bata haƙuri don tasan baya iya dogon fushi da ita saboda ƙaunarta da yake tun tushe.
Haka Waliy ya fice a gidan cikin jin haushin Rumana, abin nata ya fara ba shi haushi, duk da yana mata uzurin yanayin tashinta kenan babu kwaba da kuma al'adun inda ta taso.
Yasan ba don son da take mishi tun bata san kanta ba da babu abin da zai sakata baro ƴan uwanta, iyayenta ta biyo shi don aurensa da burin zama dashi.Shi da ita ɗin yaran Yaya da ƙani ne Abubakar da Talba, wanda iyayensu su kaɗai suka haifesu. Tare suka taso su biyu, Abubakar ya riga Talba aure hakan yasa Waliy ya zamto shine babba a gidan kuma ɗa namiji kaɗai.
Haka rayuwa ta tafi har Mami ta haifi nata yaran Mimi, Ihsan da Rahma sai Rumana auta, sannan lokacin Ammi ta sake haihuwar mata ita ma Sadiya da Shukrah, Radiyya, Farah da Nabeela auta, yaran kusan sa'annu suke.
Mimi da Sadiya kansu ɗaya, Ihsan da Shukrah, Rahma da Radiyya, Farah da Rumana, sai Nabeela ita ɗaya.
A gabansa aka haifi Rumana duk da lokacin shekarunsa bakwai. Tun ranar da ya kyalla ido ya ganta ta gansa ƙaunar junansu ya shiga ransu, gida ɗaya suka taso hakan yasa suka shaku. Shekararta goma ta gama primary shi kuma secondary a lokacin mahaifin Rumana ya samu aiki a ƙasar Canada.
Nan fa aka so rabasu don Talba yace zai tafi da yaransa gaba ɗaya huɗu mata har da Rumana da ita ce ƙaramar su. Tashin hankali da Rumana da Waliy suka shiga yasa mahaifinsa Abubakar cewa a tafi da Waliy ya yi karatunsa a can, kowa yayi na'am da haka.
Haka suka tafi inda ƙarfin shaƙuwa da soyayya ta ci gaba da wanzuwa tsakanin Ruman da Waliy, har takai ya kammala karatunsa na lauyanci ya dawo ƙasarsa bautar ƙasa, anan ya tarar jinyar mahaifinsa, ga ƙannensa mata bayan Sadiya da Shukrah guda uku sun taso, Radiyya, Farah da Nabeela.
Hakan yasa ko da ya kammala bai koma ba. Jinyar ajali yasa Allah ya karɓi abunsa inda ahlin sun ji mutuwarsa, dole Talba ya zo suka yi sati biyu suka koma harda yara.
Rumana da kuka ta koma don tana son zama tare da masoyinta, shi yayi ta lallashinta don makaranta da take ya kusa karewa, sai dai ya kula ta sake shagwaɓewa da sangarta ko don har yanzu ita ce auta, kuma yanayin al'adar can ba wa yaro damar yin yadda ya so.
Bayan komawar su kullum suna cikin waya da juna, a haka ya samu aiki ya fara a court, acan kuma Rumana ta kusa kammala karatun likitanci da take. Haka Waliy ya ɗauki dawainiyar kannensa da mahaifiyarsa duk da Baba Talba yana aiko musu da kuɗaɗe da wasu abubuwan buƙata.
A haka aka aurer manya biyu Sadiya da Shukrah har da yayun Rumana da Mimi, Ihsan, saura Radiyya, Farah da Nabeela da ita ce auta, sai Rahma sa'ar Farah.
Shekara ɗaya da aurensu Sadiya suka haihu, a lokacin Rumana ta kammala karatunta ta zama likita, duk yadda iyayenta suka so tayi aiki a Canada ƙi tayi, ta birkice musu ita Nigeria zata dawo wajen Waliy don yadda ta gansa a bikinsu Sadiya tsawon shekara ta kasa mance siffarsa da kyawunsa, wanda ya ƙara mata sonsa.
Ganin haka Baba Talba yayi wa Waliy maganar aurensu, tuni ya amince don burinsu kenan. Haka aka sha biki aka kawota gidansu a part nasa wanda ita da mahaifiyarta basu so ba, amma son da take mishi ya danne.
Haka suka fara rayuwa tare da juna cikin so da ƙaunar juna, duk da Waliy yana haƙuri da wasu halayyarta na sangarci da rashin girmama na gaba da ita, don sai abin da taga dama take yi. Ya sha mata magana sai tace ita fa bata ga laifin abin da tayi ba ba.
A cikin haka ya nema mata aiki ta fara fita inda lalaci yaci gaba, don aikin gida da girki mai aiki ce take komai, babu abin da take yi sai tayi wanka ta fita aiki, ta dawo ta ci tasha, hatta wajen shimfiɗa watarana sai Waliy ya nuna mata ɓacin ransa take yarda, wai tsoron ta lalacewa take, ƙasan ranta kuma tsoron samun ciki take duk da a matsayinta na likita ta yiwa kanta garkuwar hana ɗaukar ba yanzu ba.
Ammi tana lura da duk irin zaman da suke, sai dai bata taɓa nunawa Waliy ko a fuska ba, haka ta kwaɓi yaran yiwa Rumana rashin kunya don bata ba ta girma, balle shi da babu zancen raini tsakaninsa dasu. Sai dai Ammi da yaran su haɗu su yi ta tattaunawa.
Har yau da Nabeela tana basu labarin diramar Waliy da Mariya na jiya suna dariya, sai ga Waliy da Rumana sun shigo suka katse musu.
***
A haka Waliy ya ƙarasa office da takaicin Rumana, yana shiga bai nemi kowa ba yau yaci gaba da aikinsa.
Da ƙyar ya kawar da abin da Rumana ta mishi kafin ya samu sukuni, duk da hakan yasa a ransa dole zai mata magana kuma yaci gaba da kwaɓarta don hakan ba al'adar hausa ba ce rashin girmama na gaba musamman iyaye.
...
YOU ARE READING
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...