Page 5
Mariya ɗauke manyan idanuwanta ta yi a cikin na Barrister Waliy da ya kallota. Zuwanta court yau Litinin ta samu labarin za ayi zaman shari'a, hakan yasa ta nufi inda ake yi.
Turus ta tsaya a bakin ƙofa ganin Barrister Waliy cikin kayan barristers, saman coat ɗin jikinsa ruwan toka. Kayan sun mishi kyau sosai, yana zauna shi ɗaya gabansa computer da alamu har da shi za a fafata a shari'ar da za a gudanar.
Ƙoƙarin neman wajen zama ta fara a gefe. Ta ji an dafata, ta ɗago da sauri ta ga wata budurwa ce da kayan gida.
Fuskar budurwar ɗauke da murmushi ta ce. "Brother yana miki magana."Mariya hannun budurwar tabi da kallo inda take nuna mata, karaf suka haɗa ido da Barrister Waliy, ta yi azamar ɗauke idonta ta kalla budurwar, idan idanuwanta basu yi ƙarya ba kamanni ta ga suna yi da shi.
Kasa magana tayi ta juya ta nufi wajensa jiki a sanyaye da bata san na menene ne ba, budurwa ta bita da kallo tana murmushi cikin ranta tana faɗin. 'Allah yasa halin ba ɗaya ba, don na hango ita ma miskilar kanta ce."
Wani murmushin tayi mai kama da na mugunta tana cije lips ɗinta, idan da hakan zai kasance tasan ahlinsu zasu fi kowa murna, ko don cikar burinsu da suka daɗe suna neman yi.
...Mariya tsayawa tayi gefe da shi kaɗan bayan isarta wajensa, murya ƙasa tace. "Ina kwana sir."
Kujeran gefen sa ya nuna mata bai ɗago ba daga abin da yake yi.
"Zauna." Ya ba ta umarni.
Babu musu ta zauna inda hakan ƙara musu kusanci ya yi, kujerun don daf da juna da suke, hakan yasa taji ta takura sosai, ga ƙamshin turarensa ya danne nata sosai.
Barrister Waliy ma hakan ya ji, sai dai ya fuske ko ba komai akwai idon jama'a musamman na ƙanwarsa Nabeela da idan dai zai yi zaman shari'a sai ta halarta, don ita ma burinta kenan ta zama Barrister.
Kuma dole Mariya ta kasance tana kusa dashi don ita ce ta ƙarasa binciken shari'ar, hakan yasa da yaga shigowarta da kallon da ta mishi ta wuce don neman gurin zama ya ƙira Nabeela ta turota.
Barin abin da yake yi ya yi ya ce.
"Miƙo min file ɗin can."Mariya wacce tasan da ita yake ta gyara ta ɗauka ta ajiye mishi a gabansa, ya buɗe ya sake bi ya tura gabanta.
"Ki sake dubawa domin yanzu za ayi zaman shari'ar."Babu musu Mariya ta buɗe ta fara dubawa, yadda ta ba shi har yanzu yana haka, hakan yasa taji daɗi ya ratsata ganin bai canza komai ba.
Shigowar alkali yasa kowa ya nutsu aka miƙe aka ce. "Court."
Bayan alkali ya zauna sannan suka zauna, alkali ya nemi sanin me ake tafe dashi yau na shari'a. Regista ya miƙe ya gabatar, alkali ya nemi mai ƙara da mai laifi, tsoho ɗan shekatu saba'in ya fito ya shiga cikin doc, sannan yarinyar da take ƙarar tsoho ta fito da cikinta da har ya fito sosai.
Lauyan mai kare mai laifi ya miƙe ya gabatar da kansa tare da mataimakinsa, haka Barrister Waliy ma ya gabatar da kansa a matsayinsa na lauyan mai ƙara, bayan ya zauna Mariya ta miƙe cikin faɗuwar gaba ta gabatar da kanta a matsayinta na mai taimakawa Barrister Waliy sannan ta zauna. Gaba ɗaya a tsorace take wai yau ita ce gaban court, abin da ta jima da mafarkin gani.
Barrister Waliy ne ya fara miƙewa ya fara gabatar da shari'ar da duk abin da ya shafe shi, sannan ya fara watsa musu tambayoyin da Mariya ta rubuta dukkan su tsoho da yarinyar.
Bawan Allah duk ya rikice da tambayoyin Barrister Waliy, hakan yasa yayi ta sakin zance har magana ta tabbata cewa aikinsa kenan a unguwa, neman ƙananan yara musamman zawarawa, bayan haka ga shaidu da Barrister Waliy ya gabatar na ƴan unguwa da suka jima da zargin hakan.
Lauyan mai kare tsoho sai ya tashi zai yi magana sai alkali ya hana don magana ta riga ta tabbata, tsoho ya karɓi laifinsa da cikinsa. Hakan yasa take alkali yanke mishi hukucin riƙeta da ciyar da ita na tsawon har ta haihu, kuma ya ci gaba da ciyar da abin da ta haifa, idan yayi wayo ya karɓi abinsa.
Sannan ita ma da laifinta da ta biye mishi ga abin kunyar da ta samu, sannan ba shi da hukuncin fyaɗe don da yardarta ya nemeta har ta samu cikin.
Haka aka watse tsoho kunya kamar ya nutse ƙasa ganin yau dai Allah ya toni asirinsa, iyayen yarinya da yarinya sun ji taƙaici da kunya saboda akwai laifin ƴarsu, amma ko ba komai sun ji daɗin hukuncin da aka yanke mishi, kuma sun tona asirinsa ko ire-irensa tsofin banza zasu hankaltu.
Bayan gama shari'ar aka watse kaf a gurin amma Barrister Waliy ba shi da niyar tashi, hakan yasa Mariya ƙoƙarin tashi amma ya dakatar da ita ta hanyar mata tambaya.
"Na gama dake?"
YOU ARE READING
GOBE DA NISA
Romance"GOBE TA MATA NISA!" Tana ganin yadda rana kan yi tsayi a idanuwanta, tana ganin yadda duhun dare kan ƙara baƙanta duhun da ke zuciyarta. Rayuwa na tafiya da tafiyar mataki na daƙiƙa zuwa sa'a, sai dai a gareta sai ta zame mata shuru. Shuru irin na...