💕💕💕💕💕💕💕💕
*💔SO DA SHAK'UWA*💔
By
Mrs BB
Mom muhseen.*It's for sale*
Inkika karanta batare da kin biyaba nabarki da fitowar rana da faduwarta,kuma Allah yana kallonki.Acc no:3150952555
Bank: first bank
Name: Aisha Abubakar
300 naira only.Ga masu turo katin waya kuma zasu turo ta wannan layin 09034722970. Don Allah vanda kira only chat
*yan niger kuma 400fcfa saman stock na airtel ko Mkoudi. Ko kuma a turo orange money. Sai a tuntuɓi wannan lambar domin ƙarin bayani 84506476*
*sadaukarwa*
Gareki masoyiya abokiyar kwarai *fauxiyya s madaki* tare da duk sauran masoyana na fili dana boye na sadaukar da wannan littafi domin ku.Allah ya jaddada kauna tsakaninmu Ameen.Free page
*one*_KATSINA PRISON_
"Baiwar Allah don Allah ya sunanki,kullum na kanso na tambayeki saidai tsoro da fargaba ya hanani"
Wadda aka tambaya sunan nata ta saki wani lallausan murmushi wanda ya bayyanar da kyakkyawan beauty point d'inta guda biyu watau dumful,ta lumshe dara daran idanunta masu matuk'ar girma da haske,kafin muryarta siririya mai fitar da wani irin sauti kamar tana rera wak'a,cikin natsuwa tace."Meyasa kike son jin sunana?meyasa kikejin tsorona?sannan meyasa kike fargaba?"
Tai mata tambayoyi uku cikin lokaci guda,tana jinginar da kanta jikin bangon d'akin da suke wanda ba uwar kowa ciki sai dab'en siminti da gadajen karfe wanda banda tabarma da wane shegen tsumman bargo babu komi samansa.
Cikin natsuwa wacce tayi tambayar dafarko ta gyara zamanta tana maida dukkan hankalinta akanta tasake cewa.
"Tambayarki ta farko itace abunda yasa nake son sanin sunanki shine,tunda Allah ya had'amu d'aki guda dake tsawon watana uku kenan da nazo na sameki bantab'a ganin kinyi wani abu ba banda bautar Allah,baki magana da kowa baki sakarma kowa fuska,in aka nemi rainaki zaki takama ma mutun burki.hud'd'arki kike ke kedaya ba tare da wata damuwa ba,sai naji sha'awar son sanin sunanki"
"Tambayarki ta biyu data ukku da kikace meyasa nakejin tsoronki da fargabar yi maki mgn,shine inajin tsoronki ne ta dalilin yadda kowa na d'akin nan yake shakkarki,shiyasa nima na cika da wannan tsoron,sannan ina fargabar nayi maki magana ki harxuk'a karshe muyi fad'a kinji dalilina."
Idonta arufe yake ruf tana girgiza k'afarta guda data dora daya bisa d'aya,ta d'an daga kanta sama kadan saika rantse batajin me wannan baiwar Allah take fad'a,kusan almost ten minutes da yin maganar sannan ahankali ta fara maganarta batare da ta bude idonta ba.
"Kibar tsorona,sannan kibar fargabar tambayata abunda ya shige maki duhu,inhar na sani to zan sanar dake.suma sauran dake tsorona bai rasa nasaba da wata danayi ma dukan mutuwa saida ta suma,karshe aka raba mana d'aki da ita shima itace ta jani da badan haka ba babu ruwana da kowa,saboda ba zaman wani nake ba kamar yadda suma ba zamana suke ba that's why"
Ajiyar xuciya matar ta sauke ta sake gyara zama tace "to baki fad'a mun sunan ki ba"
Murmushi tayi tace "sunana *zeenatu Abdulmud'alib* Amman ana kirana da *Anam* "
Jinjina kai tayi tace "suna mai daraja agareni da rayuwata,domin kuwa sunan mahaifiyatane,"
Murmushin xeenat tayi wanda naga alamar dai d'abiar tace yin hakan,ahankali ta furta "Allah sarki"
Matar tace "duk da baki bukaci jin nawa ba tsawon wannan lokacin to ni sunana *habibatu hasan* amman ana kirana *beebah* don Allah inba damuwa zanso na ringa kiranki da mamana,domin girmama sunan agareni."
YOU ARE READING
SO DA SHAQUWA
Randomlabarine akan tsantsar soyayya sadaukarwa jajircewa,da darasin rayuwa labarin yana koyar da zamantakewar duniya da yadda zaka zauna da mutane,karki bari ya wuceki tabbas so da shaquwa yana dauke da salo salo na musamman sai wanda ya bisa zaifahimci...