part eight

18 2 0
                                    

*💔SO DA SHAQUWA*💔

*its for sale*

Mrs bb
Mom muhseen.

Free page
       *eight*

Washe gari tun da yafito office kasa tsinana wata tsiya yayi,ga ayyukan jibge saman table d'insa file's sunfi guda goma suna bukatar ya dubasu amman ya kasa,baida kuzari ko kadan.tun dai day samu ya ajiye yakumbo asibiti ya wuto nan,shiko shiga duba jikin nata baiba yasan bata farka ba sai yamma,shiyasa ya bari sai lokacin sannan yaje
Ga rashin bacci da bai samu yayi ba,saboda tunanin halin da Anam din take ciki,yasha mamakin rashin fad'an da Ammi batai masa ba daya koma gida don tana zaune falo har saida taga shigowarsa,amman ko kallonsa batai ba alamun dai ranta b'ace yake dashi.saidai Adda safara,u ce keta kokarin ganin ta sashi walwala,wanda baibata damar ba ya wuce d'akinsa don bata san yadda ya tsaneta bane da ko inda yake bazata kalla ba balle har tayi masa magana.

Ko break baiba yafito yabiya wajen yakumbo ya sameta kitchen ta buga ta gumi alamun ta lula duniyar tunani,babu abunda yake mata yawo akai illa kalaman mahaifin zeena yana haf da rasuwa.
_"mairo kiyi mun alkawarin kulawa da zeenatu,kingani ita kadai Allah yabamu bayan ita bamuda kowa,don Allah kiyi iyakar iyawarki wajen bata tarbiyya da kulawa,domin itama mukadai gareta gashi ni inajin ajikina daker xan tashi,balle na zamar mata bango majingina,don Allah mairo kirik'e wannan alkawarin duk da ban bar maku komi ba nasan zakiyi komi don farin cikinta,kirike ta dakyau mairo kirike zeenatu da kyau........._

Kuka ta fashe dashi tana dora kanta saman sink din wanke wanke na cikin kicin din,sosai take rera abunta bata san yashigo ba.
Dagota yayi ya rungume yanajin idonsa yana cika da kwalla,amma ya daure baiyyi kukan ba yace cikin sanyin murya mai ratsa xuciya.

"Yakumbo sai yaishe zaki bar wannan kukan?karki jama kanki wani damuwar bacin wadda kike ciki,kiyi hkr komi yaxo karshe nai maki alkawarin Anam bazata koma prison ba insha Allah."

Dagowa tayi tana zamewa daga garesa tana tsane kwallarta tace "nagode *yarona* hakika ina kuka ne badan komi ba sai dan sab'a alkawarin danayiwa marigayi malam mud'allib,har Allah ya anshi ransa nanata mani yake na rike masa zeenatu da amana,nakula da ita kar nabari tayi kuka.saigashi saboda wani son raina da tsoro yasa na jefata cikin halin k'ak'anikaye,nazeer idan zeenat tabar gidan can ka gama mani komi arayuwata........"ta fada tana share hawaye.
Ajiyar zuciya yasauke yace "insha Allah zan tabbatar maki da hakan,kishirya na saukeki asibitin idan kin gama ina wajen get ina jiranki."
Ya juya yafita sauran ayyukanta tayi saurin gamawa shaf shaf,sanna ta wuce wajen hajiya babba Ammi kenan ta sameta daining ita da Addah suna hira suna break
Cikin girmamawa yakumbo ta durk'usa har kasa saman guiwarta tace "hajiya ayimun uxiri na gama duk ayyukan safe,shine nace zanje asibiti na duba jikin xeena shekaran jiya aka kawota daga can gidan yarin babu lfy."

Shek'ek'e take kallonta fuska daure babu faraa taja tsaki tace "idan kinje don Allah kiyi zamanki har lokacin aikin rana ya wuce zaki sani"
Tatashi nata sake cewa uffam ba ta wuce tabarsu tana jin Adda nacewa.
"Dama mutuwa tayi kowa yahuta,wanan yarinya Allah yasani bani kaunarta duk da tafita cikin family din nan hankalina ya kasa natsuwa,jinake kamar naje nakasheta dakaina............saurin ficewa yakumbo tayi tana rik'e kukanta dole ne ma tazo tabar garin nan,zamanta da anam cikin wadannan mugayem hadarine,gara sukoma kauyensu yafiye masu kwanciyar hankali.

Bakin get din asibitin ya tsaya ta sauka tace "ba zaka shiga ba kaganta"
Girgiza kai yayi yace "ina saurine,zan dawo anjima ai amma ke kibari inkika koma dadare saina sake kawoki,saboda ayyukanki ko"

Tace"haka ne yanxu ma bazan dade ba zan koma hajiya taja mun kunne"

Ya laluba aljihunsa ya fiddo five thousand yace "kihau napep inzaki koma"

Ganin idan tace aa zubar mata dasu zai yawuce yasa ta ansa cikin kulawa tace "nagode Allah yayi albarka"
Yace ameen sannan ya wuce.

******

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now