part eighteen

15 1 0
                                    

*💔SO DA SHAK'UWA*💔

*its for sale*

By

Mrs BB
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461 or
Humaira7531

Free page
   *Eighteen*

Tunda na farka na tashi na gyara falon nashare nai mopping na saka turaren wuta cikin burner,sannan naje na gyara gadon na fesa freshener mai kamshin strawberry na hada da tsintsiyar kamshi,sanan na shiga wanka ina ta kokowa da xuciyata akan tunanin nazeer yatai kobai tai ba.
Idan nayi tunanin yatafin sai naji hankalina yana tashi,sharewa kawai nake.............kofar ya tura yashiga daddaden kamshin  dake tashi acikin dakin ya daki hancinsa,lumshe idonsa yayi yana jin xuciyarsa har ta fara
Mahaukaciyar kewarta tun yanxu,jin ana watsa ruwa a bayin yasan wanka take,kayan data fiddo ya kalla under wears dinta ne sama bra da pant,saurin kauda kai yayi yana sakejin xuciyarsa tana halbawa.
Jingina bayansa yayi da kofar yana rungume da hannunsa,daidai na na fito da d'an towel dinta iya cinya...........xuciyarsa jiyayi ta tsaya da bugawa,tunda yake baitab'a ganin surarta haka ba kirjinsa ya doka,...........huking nai atsayen da nake ganinsa cikin dakin baccin mu,wanda hakan bata tab'a faruwa ba.
Kallon cikin idon juna muke kamar wasu wawaye,yana yin bugun xuciyata ya sauya yaringa yi da sauri da sauri.
Saurin dauke kai nai ina jan karamin tsaki,na nufi wajen kayana na dauka zan koma bayin na saka...........naji yace mun cikin wata murya wadda ban sansa da ita ba yace.

"Zan tafi Anam"

Ban waigo ba saboda bana fatan sake kallon cikin idonsa dakata wa nai da shiga toilet d'in nace "to"

Raunin muryarsa ta bayyana yace "shikenan Abunda zakice."

Runtse idona nai bance komi ba,kuma ni ban shiga toilet d'in ba.
Takunsa najiyo daga bayana dan danan nafara kokarin barin wajen,bakin gado naje na ajiye kayan na fara neman inda zanga hijab d'ina na saka............caraf ya rik'emun hannu nai saurin jiyowa ina kallonsa idonsa ya canza kala kuka ne kawai bai rushe ba,shima d'in da alamun ba wuya yayisa.
Fixge hannuna nai cikin fushi nace "karka sake rik'emun hannu,ka mance hannun bazawara ne.ko kamance bazawara kake tsaye gabanta?"

Wannan ya tabbatar masa taji abunda yake gaya ma yah aysar.
Wani abu daya tokare masa makoshi ya hadiye amman yaki wucewa,bakinsa yabude zai magana na wuce na daukko abayata na saka nace.

"Zan shirya kaxo ka sani agaba,lokaci dai baya jiran kowa."

Na samu gefen gadon na zauna ina daukko jikkar kayan shafata na bude ya fiddo abunda zanyi anfani dashi,hannuna sai rawa yake inason bude robar man na kasa.sai kerma hannun yake dama jikina baki daya,ganin nazeer ya sake dawo mun da maganganunsa na jiya.bakin cikin su yana ninkuwa cikin raina,..............abun mamaki jinai kwalla ta cika idona.nai saurin saka gefen abaya na goge afakaice.
saidai ganinsa nai gabana ya durk'usa bisa guiwarsa,ansar man yayi daga hannuna ya bude mani.
Ya ajiye gefena dauka nai ina kokowar lakutowa amman rawar da hannuna keyi da jikina yasa na kasa,hawayen suka samu damar fara layi bisa kumatuna.
Kamo hannuna yayi ya bude tafin ta lakuto man ya samun cikin tafin hannun,daidai sadda kwallata ta d'igo aciki.

Saurin d'ago hab'a ta yayi idonsa jawuri muryarsa ta shak'e yace "menai maki Anam?don Allah menai maki,kuka kike? saboda me?inhar akan maganar dakikaji ne kiyi hkr banda wani zab'i saina fadin hakan,yazanyi yaya yatirkeni shiyasa nace masa haka.sokike nayi karyar abunda ba gaskiya ba."

Dago idona cike da hawaye dake xuba nai ina kallonsa nace "katashi kaban waje,ina ruwana da duk abunda zakace,wulakancine ai mun gamu dashi tunda muka nace agidanku,ba bazawara ba kakirani ma da duk sunan da kake ganin shine daidai,bai daman ba."

Nafara kokarin anashe hannuna wajensa matsowa yayi kamar zai shige jikina,nai saurin naja baya.

"Anam kinsan tambayar da yaya yayi mani kau?cewa fa yayi wai ko sonki nake!taya kike zaton bazan fadi duk abunda zaisaka na kare kaina ba."

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now