part six

27 2 0
                                    

💕💕💕💕💕💕💕💕

*💔SO DA SHAK'UWA*💔

By
Mrs BB
Mom muhseen.

*It's for sale*

Acc no:3150952555
Bank: first bank
Name: Aisha Abubakar
300 naira only.

Ga masu turo katin waya kuma zasu turo ta wannan layin 09034722970. Don Allah vanda kira only chat

*yan niger kuma 400fcfa saman stock na airtel ko Mkoudi. Ko kuma a turo orange money. Sai a tuntuɓi wannan lambar domin ƙarin bayani 84506476*

*sadaukarwa*
Gareki masoyiya abokiyar kwarai *fauxiyya s madaki* tare da duk sauran masoyana na fili dana boye na sadaukar da wannan littafi domin ku.Allah ya jaddada kauna tsakaninmu Ameen.

               Free page
                  *Six*

Aiki mukai tayi yau d'in kamar wasu jakkuna,babu abunda yake saurin wahalar dani irin fasa duwatsu,shine yake samun ciwon kirji dan danan,kafin in ankare na kwanta ciwo shiyasa bana murna juma'a taxo aztagfirullah saboda wahalar da ake bamu ta aikin marece,mune kwasar wasu bololi fashin duwatsu,ranar mune zamuyi girkin dare abun babu sauki sai wajen lillahi.muna aikin ina tunanin labarin beebah,tabbas akwai tausayi da makirci saidai ko kusa bai kamo kafar nata labarin ba,ba mamaki idan taji nawa taita rusa kuka.

Bamune muka gama ayyukan ba sai ana kiran sallar magriba,iyakar wahaltuwa yau mun jigata,nidai alfarma na roka naje na watsa ruwa don samun sauk'in ciwon da jikina hake,ga kirjina da xuciyata sunyi mun nauyi kamar an dora mun bulo samansu.
Wankan nayo naxo cikin yan komatsaina na lalubo wata robar virselin na fara kalatowa don ya kare babu komi aciki,sauran yan dakin daga mai salla sai masu hira,beeba kuma laximi take ta gama salar magriba.da yake itama taje ta watsa ruwan,daker na samu shafa ma kafata da hanuna don daman ni bamai sama fuska virselin bace tunda naxo gidan,shiyasa duk fatar jikina ta lalace banda ta fuskar,ita tasha banban dasu balaifi duk da ina bak'a bakina kalar ruwan k'asa its means dai brown color niba fara ba bakuma baka ba,to naci sa'a fuskata color dinta ya nanan amman banda sauran jikina,inhar kasanni shekarun baya inka yanxu dole kasha mamakin yadda nakoma.............cikin kayana kala hudu da muke anfani dasu na dauko daya dana yi sati ban saka ba doguwar rigace purple,plan yard ne baida wani abu ajikinsa.na saka kayata banda matsakar inears don momy tana kawo mani time to time,so su indasu balaifi.salla nayi saboda ganin lokacinta yana wucewa,bayan na gama na fiddo qur ani na ina karantawa cikin natsuwa,dakin yayi shiru sai sautin muryata  kakeji tana tashi cikin daddad'en sauti,duk sadda na fara karatu irin haka tofa zanji sunyi shiru kamar ba kowa,har nake mamaki daman sun san in ana karatun qur ani ba'a son hayaniya,saida wata xulai tace mun wlh zeenah dadin muryarki ne ma yakesawa muna saurarawa,kina bamu sha'awane sosai.

Yanxun ma nasan dadin muryata da karatun yasa sukai shiru suna saurarena,beeba ta tusani gana tana kallona kamar ta samu tv,murmushi nake mata idan na d'ago muka had'a ido da ita,ahaka nai ta karatuna har nayi hixub biyu cikakke............jinai duk sunyi mun kabbara.
Dariya nai ina rufe qu'anin nace "Alhamdulillah to muyi addua mana Domin duk sadda ka gama karatun qu'ani anaso kayi addua kuma babu makawa tatafi direct xuwa ga ubangiji,mufara."

*"Allahumma inna a'uxubika min axabil k'abar,wamin axabi jahannam,wamin fitinatil mahya walmamat,wamin fitinatil masihiddajjal.*

*Allahuma k'hini azabaka yauma taba asu ibadak,*

*yahayyu yaqayyum birahmatika astagisu,aslihli sha'ani kulluhu wala tak'ilni ila nafsi d'arfata ain.*

*Allahumma inna auxubika min jahadil bala'i watark'ishsha k'ak'i,washima datul ahk'abi*

*Allahumma afeeni fi badani,Allahumma afeeni fi sam'i Allahumma afeeni fi basari la'ilaha illa anta,Allahumma inni auxubika minal kufri walfak'ari,wa'auxu bika min axabil kabar la'ilaha illa anta*

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now