part ten

16 2 0
                                    

*💔SO DA SHAQUWA*💔

Mrs bb
Mom muhseen.

Free page
       *ten*

Suna gab da shiga kofar falon suka jiyo har gagin fadan Ammi tana cewa........."wallahi ba a halicci yar da zata mallakemun d'ana ba,ko takai kaska naci billahil axim sai tarabur mun da d'ana,watau duk abubuwan dasuka faru bai saka taji ta tsanesaba?saima kusanci da hakan ya k'ara masu kwantar da hankalin juu kibar xubar da hawayenki abanxa awofi,indai nice mahaifiyar aduniya bada wata mata saike...........fad'an ta bai hanasu karasa wa ba jibril da wani sajan suna biye dasu abaya da jakunkunansa.

Sallama yayi cikin mazan taka da daurewar fuska babu alamar burbushin dariya ko fara'a akan fuskar tashi,tai saurin mik'ewa tana washe hakoranta wadasuka sha adon hakurin xinari na makka guda bigu..........."ga yarona ga yarona oyoyo!sannu aysar d'ina yau dai gani ga babban yarona d'an albarka,mai sharemun kukana yarona maijin maganata masoyina."
Rungume juna sukai yana sassauta daurewar fuskarsa,don daman yayi tunanin haka daya shigo zata yi shiru kamar ba itace mai maganar ba.

Gefe nazeer ya tsaya ya rungume hannu yana kallonsu,ba tun yau yasan cewar Ammi tafi son yayansa ba,ba tun yau take fadar shine mai faranta mata ba,kullin wajenta shine masoyinta meyasa?meyasa shi bata daukarsa d'anta?kullin kyara da fad'a ne tsakaninsu,babu jituwa babu soyayyar da da uwarsa.........ako dayaushe wannan abun yana karya masa xuciya,duk da daman shi mai saurin kukane amman wannan yafi kowane abu saka shi cikin damuwa matsananciya.
Ya hanga ya duba baiga inda ya kuskure mata ba tunda Allah yasa yayi yau da hankali,tabbas shekara uku baya akan zeenat yayita sab'a mata har baisan iyaka ba,kuma zaice ashekarunne kawai yayimata abunda ba daidai ba,kafin xuwan su yakumbo kamar zai lashi kafarta don biyayya komi yaga zai sa tayi masa dariya kokariyake yayi mata,amman bata nuna jin dadi.yayansa ko kashi yanuna yana so daga ranar Ammi shine abun sonta,bai taba ganin abunda yaya yake so Ammi bata soshi ba sai zeenat anam................"to ki sakeni haka nagaji fah wlh"

Ta sakesa yana idasa shigowa cikin babban falon daya gaji da had'uwa,hada ido sukai da juu tai saurin mik'ewa "Adda,Ammi ni zan shiga na d'an watsa ruwa na huta zuwa 3:00pm zan saukko."

Adda safara'u cikin kaunar yar tata tace "to yar lele ahuta lafiya"

Ta wuce tana satar kallonsa hakika tasan yagama ganota taxo tayi kararsa.

Nazeer cikin sanyin murya yace "Ammi yau dai ga yaya ya dawo,duk ta damuwa da bacin rai ya kare ko?"
Ya fada yana mata murmushi,ta fakaici idon aysar d'in ta maka masa harara,ta maida hankalinta wajen aysar d'in tana ta masa murmushi,jakunkunan da aka shigo dasu ya nuna mata yace "ga tsara ba nan Amm,nazeer daukar mun bag dina kaimun sama"

Yayi hanzarin tashi yazo ya d'auki jakar ya nufi part d'insa dake nan k'asa don shi baisan upstairs.

Binsa da kallo aysar d'in yayi sannan yaja ajiyar xuciya ya maido idonsa akan ammin.
yace "mamana in banda ni da nazeer aduniya yanxu wakike dasu dasuka kaimu awajenki?"

B'ata rai tayi watau zai fara mata masihar tashi kenan.
"Ban son shirme fah,wagareni to da yakaikun"

Yacigaba da cewa "har yau alakarki da yaron can bata sauya ba,haba mama haba Amminah meyasa zaki yi haka,Adda kina kallon ta kina ganin duk abubuwan da take yiwa yaronta ke bazaki iya nusar da ita ba,itafa ta haifesa itafa ta kawosa duniya,kinsan baki sonsa kika yar da kika haifai,wlh bakida abunda zakiyi ya kona xuciyata sama da nuna kin d'an uwana dakike,kuma inhar bata sauya zane ba zakisha mamakina Ammi.kekuma ga duniyar nan Allah ya bamu sa'a"
Yace ma Adda safara'u.
Yamik'e yabi bayan kanensa don ya taushesa,mawuyacine inba yana can yana kuka ba.

💕💕💕💕💕💕💕💕

Kwance nake cikin wani madaidaicin falo mai kyau acikin gidan momyn,zamuyi awa guda da dawowa daga asibitin,nai wanka momy ta kwaso mun sabbin kayan hafixa da ba sawa take ba wajen kala takwas,tace na fara anfani dasu kafin na idasa warwarewa naje nayo siyayya dakaina.
Allah sarki momy hakika banda kalaman gode mata,saboda ta soni lokacin da banda kowa,lokacin da kowa nawa ya gujeni mezance da wannan matar banda na dawwama ina mata adduar gamawa da duniya lafiya.

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now