part five

22 2 0
                                    

💕💕💕💕💕💕💕💕

*💔SO DA SHAK'UWA*💔

By
Mrs BB
Mom muhseen.

*It's for sale*

Acc no:3150952555
Bank: first bank
Name: Aisha Abubakar
300 naira only.

Ga masu turo katin waya kuma zasu turo ta wannan layin mtn  09034722970. Don Allah vanda kira only chat

*Yan niger kuma 400fcfa saman stock na airtel ko Mkoudi. Ko kuma a turo orange money. Sai a tuntuɓi wannan lambar domin ƙarin bayani 84506476*

*sadaukarwa*
Gareki masoyiya abokiyar kwarai *fauxiyya s madaki* tare da duk sauran masoyana na fili dana boye na sadaukar da wannan littafi domin ku.Allah ya jaddada kauna tsakaninmu Ameen.

               Free page
                 *five*

Muryarsa mai dan karen sanyi da dad'i yace ma momyn.

"Abunda yafaru yariga yafaru bazan iya dawo dashi na goge abunda nai ba,amman zan yi iyakar kokarina wajen ganin nayi abunda ya dace"

Ta tab'e baki tace "uhm daga baya kenan,Allah ya taimaka yabada sa'a kuskure kam ai kunyi saidai addua,katashi kaje inda zakaje kadawo mutafi."

Shashshab'ewa yayi yana narkewa yace "momy wlh nagaji da aikin nan nikadai,Allah yasani ina wahaltuwa kota nan wajen nayi kewarta ina cikinyi ma wlh."

Harara ta maka masa tana tashi tace "ni nayi nan inka gama sabbatun saika wuce"

Tatashi tabarsa yana tunane tunanen da suka zamar masa jiki,daker ya lallashi xuciyarsa ya iyatashi yabar gidan.

💕💕💕💕💕💕💕💕

Abinci suke ci wanda suka anso na rana,don daman duk juma'a sai bayan sallar ake raba masu abincin,shinkaface da wake julof amman saikace ba'a saka komi aciki ba,gata nan fara fat ko man kirki babu sai iyayen fato faton tattasai busasshe da aka yi sanwar dashi,abincin dai cinsa sai dole dolenma dole.
Kallon abincin take yayin da tunaninta yatafi duniyarta ta baya,ko k'adan bata cin abincin da babu nama ko kifi ko kwai,dole acikin uku nan asamu guda rayuwarta mai tsadace awancen lokacin,wanda ita d'in ba yar kowa bace amman ta dauki rayuwarta da zafi,kome tanema samu take duk tsadarsa kuwa.sai abunda ranta yakeso zataci ko kadan inhar abinci baiyi mata bata hadiye lomar data saka acikin bakinta,sai gashi yau anwayi gari duk wannan karyar babu ita,duk wannan daukar kan da zafi babu shi duniya ta koya mata hankali,ta koya mata darasi wanda bazata tab'a manta wa dashi ba................"mamana lafiya dai"

Beeba ta fad'a tana tsura mata ido ganin tana ta kallon abincin takasa saka koda loma d'ayace abakinta.

Kwalla ta d'igo kasa daga idonta tai saurin sharewa tana yak'e tace "aa beeba bakomi na tuna bayane,kici abincin nan bana jin zan iyaci ni"

"Haba mamana,karki bari damuwa ta haifar maki da ciwon da bazaki warke cikin sauki ba,kiyi hkr don Allah kixo muci"

Girgiza kai tayi tana cewa "ciwo kuma beeba saidai ace Allah ya sawake,don babban ciwon da damuwa ke haifarwa ni tariga ta haifarmun dashi,ba ciwon xuciya bane da hawan jini ake gudarmaka inaka cikin damuwa?toni duk inadasu duk da cewar anhaifeni da ciwon xuciya amman daga baya na warke,xuwa nan gidan komi ya zama sabo."

Beeba tausayinta ya kamata taji hawaye suna xubo mata tace "kiyi hkr mamana haka kaddararmu take Allah yayi mana magani,amma ki daure kici abincin nan inkuma bazakici ba na hada maki gari kici."

Lumshe idona nai inajin yadda kirjina yake suya yana rad'ad'i kamar ana yankarsa,nace "ko ruwa bazan iya had'iya ba beeba kiyi hkr.kedai kici kigama kidora mun daga inda kika tsaya."

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now