*💔SO DA SHAQUWA*💔
Mrs bb
Mom muhseen.Free page
*eleven*"Na tare gidan salmanu kamar gaske zamuyi zaman lafiya nidashi, adaren da aka kaini ban tsira wajen salmanu ba d'an naman da ake kaima amarya bai kawo ba,kamar yayi shaye shaye haka ya fad'o dakin da aka saukeni afirgice na mik'e ina kallonsa,idonsa jajawur yana kallona.
Muryarsa kakkausa ta daki kunnena yake cewa.
"Badai kisa anrabani da wadda nakeso ba,kenan har kin kai nasoki to bari kiji ni kyan ki da ake xuxutawa agari kwata kwata baya damuna,don haka yadda kika bakanta man kema saina bakanta maki keda iyayenki,sannan wlh bazan zauna dake ba amman kafin nan bari na wanki sadakina...........ayam ta fad'o mani to dayake nima d'in Allah yayini banda hakuri,kuma masifafface tagaske ba'a gaya mun ba siga nayi shiru.
Hankad'asa nai da iyakar karfina,kasancewar cikin maye yake yatafi yafad'i kasa.gabana yana fad'uwa don sai yanxu tsoron lamarin ya kamani,jikina yafara tsuma ina kermar baki nace
"Wallahi baka isa ba,kaidin banza da wofi har ka isa ka wulakantani angaya maka ni duk kauyen nan akwai wanda nakesone,to ni hadi yafiye mun kai (wani babban kazamine acikin gari kowa yasan kalar kazantarsa gashi kamar wani mahaukaci haka yake)
A haukace ya sake yowa kaina na fasa kara,bai hana ya sake tausheni ba muka hau kokowa cikin d'akin yaringa makani ga bango,yaringa dukana ina ramawa ina cixonsa da yakushinsa yadda yayi mun raunika haka naimasa,duk wannan danben bai hana salmanu ya rabani da budurcina ba,kuma ba karamin illa yayi mun ba don ko yatsana bana iya dagawa.
Yayi mun kaca kaca sannan yafice ya barni nan yashe kamar wata marar galihu.
Naci kuka har nagodema Allah bana iya taimakon kaina,sunan baffa dana yakumbo kawai nake kira dayake cikin gidansu aka katange wani waje muke zaune.
Wajen azahar naji alamin shihowar innarsu dakin,muryata bata fita sosai nace "inna kitaimaka mun karna mutu,kikaini wajen yakumbona wallahi salmanu kashe ni zai"
Sallalami taitayi ganin ta'asar da yayi mun kuma yafice babu wanda ya sake ganin gilminsa,ita tasaka ruwan zafi tayi mun wanka ihu nake da kuka har ta gama,ta samun kaya tafita taje ta sanar da kawun.
Ranar asibitin cikin gamawa na kwana,dinki uku akaimun ga gabana naci wuya har bansan ya zan kwatan ta ba,nayiwa salmanu Allah ya isa tafi cikin buhu,ana sallamata nace wlh bazan koma gidanmu zan tafi,rigima akasha dani sosai dole inna ta hakura natafi gida wajen yakumbona............"kiyi hkr zeenatu shi aure ya gaji haka,hkr akeyi komi zai daidaita."Wata kara na fasa ina fashewa dakuka daidai sadda naji shihowar baffa.
"Wallahi bazan koma ba,cewa fa yayi nasaka anraba shi da wadda yakeso!baya sona kuma saiya bakanta mun nidaku kamar yadda aka bakanta masa.............."daina kuka yar gidan baffanta ai tafaru takare share hawayenki salmanu bashine ya dace da rayuwarki ba,don gashi ya aiko abani takardar sakinki shi bazai zauna da wadda baya so ba"
Ihun murna na fashe dashi ina fadawa jikin yakumbo,wadda ita takama hawaye take tana cewa "me mukaima salmanu haka?daga abun arxiki saiya koma na tsiya,wallahi banji dadi ba duka nawa xeenatu take dazai maidata bajawara da kananun shekarunta...........katseta baffa yayi yace"babu komi haka Allah yaso,don haka bazan sake mata wani aure ba mairo karatu zata koma,ki shirya gobe litinin zamu shiga cikin birni komi ya kamata ayimata sai ayi.tafara makarantarta muga abunda Allah zai"
"Amman ka manta sai tayi iddah,kabari ta gama iddarta sannan saika sata makarantar"
Jinjina kai yayi yace "ohh wlh namanta,To kikula da ita don Allah duk abunda ya dace ki nuna mata,kiringa mata nasiha don xeenatu tana da rawar kai"
Acikin wata uku nayi iddata cikin kulawar yakumbo,bana fita ko ina bana kwalliya duk daman haka Allah yayini bata daman ba,duk wasu k'a idoji da mai idda zatabi ina binsu har Allah yasa na kammala iddata cikin kwanciyar hankali,nanfa samarin garin da jawara suka kunno mun kai amman na rufe idona nida baffa mukace bamusan wannan ba.
Yakumbo kau kamar ta daura mun duk wanda yazo saboda bata burin daya wuce nayi aure................
YOU ARE READING
SO DA SHAQUWA
Randomlabarine akan tsantsar soyayya sadaukarwa jajircewa,da darasin rayuwa labarin yana koyar da zamantakewar duniya da yadda zaka zauna da mutane,karki bari ya wuceki tabbas so da shaquwa yana dauke da salo salo na musamman sai wanda ya bisa zaifahimci...