part fifteen

15 1 0
                                    

*💔SO DA SHAK'UWA*💔
*It's for sale*

By

Mrs BB
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461

Free page
*fifteen*

Zan iya cewa tun daga ranar nida nazeer wata matsananciyar *shak'uwa* tashiga tsakaninmu.shi da kansa yake kaini makaranta,da dafarko dady hanawa yayi yace bai kware wajen tuki ba,saida ya samashi rigima sannan yace to yakula banda gudu,kuma yasaka natsuwa sosai,mafarin kullin zai kaini kuma ya d'aukkoni.
Idan na dawo da marece zanje islamiyya dake wajen unguwarmu,bana dawowa sai karfe shidda kuma tare zamu dawo ak'afa,muna tafiya muna fira da dariya,dadaddare kuma mutafi can bayan part d'in momy nayi shimfid'a muyi karatu,sai gashi physics din da nake kuka dashi yanxu sonsa nake sosai,don nazeer ya bada babbar gudunmawarsa wajen ganar dani harda sauran subject.
Don ta dalilin nazeer turanci ya zauna bakina,ko kadan baya mun mgn da hausa idan yana mun lesson,tun ina jurewa saboda ba fahimta nake sosai ba har nayi masa magana.
Nace nifa ba fahimta nake sosai ba,yace shiyasa bazan gane ba acikin aji,saboda skul din pravete ce kuma ta masu hali so teachers din basa hausa gaskiya.
Ahankali ya ringa yimun yadda zan gane kuma na koya, banyi aune ba ban ankare ba naji na ba nazeer damar karantata tare da karantar duk wani action dina,nima kuma na karancesa.
Nasan mode dinsa na farin ciki,nasan na bakin ciki nasan mode dinsa idan yana cikin damuwa,haka zan iya gane damuwarsa idan ya bani damar hakan.atakaice mun zama kamar abokan juna duk da kuwa yagirman saidai girman da yayi mani bazai wuce shekara uku tsakani ba.

Wannan kusancin ya kara rura wutar kiyayyata a wajen juwairat da su Ammi,don karara suke nuna mun tsana.
Batasu nake ba muddin basu shiga harkata ba ni babu abunda ya shafan dasu,tunda ba su suka ajiyeni ba,abunda nake yawan gayama yakumbo kenan.
Muna gaf da samun hutu nazeer ya samu admission a jamiar *UDUS* da murnar sa yashigo dakin mu lokacin yakumbo bata nan tana can b'angaren masu aiki,saudaya wa idan kadaici ya isheta da zama waje d'aya saita tafi can tunda har yanxu ba wani sabawa sukai da momy sosai ba.
Ina falo na baje jikkar islamiyya ina duba tajwidin da mukaiyi jiya don yau za,a anshi hadda.
Kasancewar juma'a ce yau jin anshigo yasa nai saurin kallonsa,hannunsa sanye cikin aljihu kamar yadda yake d'abiar sace,yau manyan kaya yasaka saboda masallaci,sunyi masifar masa kyau kaini zan iya cewa ko tsumma nazeer ya yafa kyau yake masa.
Coffee brown shadda ce shampoo,an masa rigar half janfer mai hannun links ga agogonsa itama kalar shaddarsa,babu hula kansa don daman da wuya kagansa da hula k'ube,ko masallacin yasa yaje daya dawo zaicire.
Fuskarsa dauke da murmushi ga dumful d'insa nan guda d'aya yafito,lumshe idona nai nima nai masa murmushin ina tattare littatafaina gefe.
Najawo gyalen dana daukko zan daura saman riga da siket d'in dake jikina na less pink and marron color,anyimun irin wuyan nan open shoulder,anyi kwalliya da bakin less din tunda nasa kayan ni kaina nasan sun gama ansata,ba kamar dana duba madubi saida nayi murmushi ganin dirina yana sake bayyana,amman d'an jikina nanan saidai kara mulmulewa dayayi.yakumbo kanta saida taita yaba kayan,don cikin sabbin dinkunan mune da ban gama sawa ba har yau.
To saboda nauyin d'ankwalin less din yasa ban daura saba,na dauko karamin gyale maroon don na daura,iskar danaji tamun dadi yasa na ajiye ina karatuna.

Yafashi nai bisa kaina ina cewa.
"Ji yadda ka toge bazaka shigo ba ne"

Shigowar yayi bayan ya cire cover dinsa bakake da bakar safa sanye cikin kafafunsa,gyara zamana nayi cikin kujera yana isowa ya zauna saman hannun kujerar da nake yana wani yimun kallon dayasan bana so.
Ga wannan matsiyacin kamshin nasa maijefa ka cikin wani yanayi mai dadi.

Had'e rai nayi nace "daina kallona haka bana so,kuma katashi akaina da wannan turaren mai hawan kai"

Dariya yayi yace "bazan tashi ba,keda zaki tambayeni farin cikin menake amman kin fara hantara ta"
Ya fada da muryar shagwab'a kamar zai fashe da kuka,dalalo idona nayi nace.

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now