part three

30 0 0
                                    

💕💕💕💕💕💕💕💕

*💔SO DA SHAK'UWA*💔

By
Mrs BB
Mom muhseen.

*It's for sale*

Acc no:3150952555
Bank: first bank
Name: Aisha Abubakar
300 naira only.

Ga masu turo katin waya kuma zasu turo ta wannan layin 09034722970. Don Allah vanda kira only chat

*yan niger kuma 400fcfa saman stock na airtel ko Mkoudi. Ko kuma a turo orange money. Sai a tuntuɓi wannan lambar domin ƙarin bayani 84506476*

*sadaukarwa*
Gareki masoyiya abokiyar kwarai *fauxiyya s madaki* tare da duk sauran masoyana na fili dana boye na sadaukar da wannan littafi domin ku.Allah ya jaddada kauna tsakaninmu Ameen.

               Free page
                *Three*

Ajiyar xuciya take ta saukewa ahankali bayan uban kukan da tasha kamar bazata daina ba,idon nan mai kyau yayi jajawur sai sauke numfashi takeyi.
Beeba na zaune har lokacin tana shafa kanta tunaninta ma ko tayi bacci amma data lek'a fuskarta taga idonta biyu,shirun sukai suduka yayin da mutanen dakin duk sunyi bacci sun barsu,saboda tashin asuba da ake masu sutai wajen aikin wahalarsu.

Ahankali beeba tace "mamana"

Kamar bazata ansa ba xuwa can taja wani numfashi tace mata "na'am"

Cigaba da magana beeba tayi da cewa"daman kina da aure kike zaune agidan nan tsawon shekara uku?meyasa baki nemi sakinki ba kafin azaunar dake anan,shi wane irin azzalumine da zai barki da igiyar aure akanki har wannan shekarun."

Lumshe idonta tayi tana jin kanta yana sarawa bakinta da labbanta suka motsa tace "shid'in ya kasance mai adalci acikin rayuwata,shid'in mutum ne dabazan iya mancewa dashi ba,duk da kalar abubuwan da suka faru bana jin haushinsa ko kad'an,domin ya kasance  mutumin kirki wanda bai maida d'an adam kamar bawa ba,ya daukan da kima mutunci da girmamawa duk da ya auran bazan iya sanin cewar yana so ko bayaso ba,abunda nasani shine yanemi amuncewata nikuma na bashi yardata dari bisa d'ari,wanda nima bazan iya gane cikin *so da shak'uwa* wanne nake masa ba.na samu xuciyata da amuncewa,ba tare da duba k'alubalen dake zagaye damu ba."

Taja numfashi tayi shiru yayin da beeba take k'agare da sonji cikekken bayani daga gareta,jin tayi shiri yasa ta sake mata magana.

"Mamana tun bayan dawowarmu daga wajen wannan matar da naji kin kira da momy xuciyata ta kwad'autu da sonjin labarinki,don Allah inba damuwa mezai hana kibani naji"

Gyara kwanciyarta tayi takawata fuskarta da wani irin murmushi mai kyau,galala tayi tana kalonta don tsabar mamaki.

Cikin murmushin tace mata "nabaki mamaki ko,nima bansan nayi ba kawai dai duk sadda wasu side of my life suka fad'o mani bana sanin inayinsa,zanso kiji labarin *zeenat Anam* amman bazan iya bakishi ahalin yanxu ba kiyi hkr,zan so ke kifara bani naki saboda labarina yana da tsawo beebah."

Jinjina kai tayi tana cewa "shikenan mamana insha Allah zanbaki labarin habeebatu hasan,yanxu dai mu kwanta dare nayi kuma kinsan munada ayyukan yi da safe."

Sukai addua kowa yaje ya kwanta bisa gadonsa cike da tarin tunanika kala daban daban.

💕💕💕💕💕💕💕

            *2days later*

"What's wrong with you my boy?"

Komawa yayi cikin kujerarsa da yake kai ya kwantar da bayansa yana sake narkar da fuskarsa kamar zai fashe da kuka,yayin da wanda yayi masa tambayar yake kallonsa ta cikin computer ma'ana dai suna video call ne.

SO DA SHAQUWAWhere stories live. Discover now