*💔SO DA SHAK'UWA*💔
*its for sale*
By
Mrs BB
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461 or
Humaira7531The last free page
*Twenty*Sassanyar ajiyar zuciya na sauke ina murmushi nace masa "Ayya kayi hkr ban zaji ai zaka neman ba wall...a...hi...."
Na karashe wallahin aduburce,saboda wannan k'amshin dake ratsa mun dukkanin xuciya da rahina,har da gangar jikina.
Rutse idona nai saboda jin anshigo,kenan yusra bude tabar kofar data shigo.
Durk'ushinsa naji gefena kamar zai fado kan bayana,yazare hannuna daga saman dutsin kamar sakarai saina bisa da kallo,gyara durk'ushinsa yayi yaci gaba da goge rigar da nake gogewar.
Matsawa nai najigina da katakon gadona,ina sauraren yayan da yayi shiru yana jiran na gama abunda nake."Mekikeyi ne?"
Saida na runtse idona sanan nace masa "guga nake,"
"Oky inkin gama ki kirani da wayarki,Allah yasa baki baccin wuri."
Nace "aa yaya yau bazanyi ba zan kira kan."
Yamun sallama na sauke wayar cikin wata irin kasalar jiki.Tattare kafafuna nai na rungume na kwantar da kaina bisa guiyawuna,duka idanuna na tsura masa gugar yake cikin natsuwa da bi asannu,sai lallab'a kayan yake kamar yana jin tausayinsu,haka nazeer yake komi yakeyi cikin sand'o da natsuwa yakeyinsa,har saika gaji ina sauri kake ka anshe abunka.
Mamakin ramarsa nakeyi don yayi wata irin rama sosai wadda kallo d'aya zakai masa ka gano hakan.
Ba tare daya kallan ba ya ce "pls bani d'an ruwa na yayyafa akai."
Wayyo Allahna ai jinai kamar yana busamun sarewa acikin kunnuwana,jikina amace na tashi ko kusa ban ankare da shigar dake jikina ba,toilet din na shiga Cup d'in da nake wanka dashi wani lokacin aciki na d'ebo ruwan.
Na fito naga ya dakata da gugar ya tankwashe kafarsa guda ya zauna akai,dago fuskarsa yayi wadda tayi fayau ya kara haske,sai sajensa da gemunsa da yake bala'in fiddo masa kyansa,har nakan rasa wanne yafi wani kyau cikin shida yah aysar.
Tsaye nai gabansa muna kallon juna ido cikin ido,har ban san ruwan dana d'ebo yana xuba kasa ba saboda shagala.
Dauke idonsa yayi yana kallon wani wajen,kafin yace "ki kalli gabanki malama baki ga abunda kike ba"Zaro idona nai ganin duk na jik'e wajen,sai kyafce kyafcen ido nake na juya don sake d'ebo wani..............tafiya nai luuuuuuu zan ci k'asa saboda sulb'in tayils din jina nai kawai ajikinsa har kaina yana bugar karfen gadona,kara nasa badan zafin da naji yakai nayi ihun ba,tsananin shock d'in da naji yasa na saki wannan yar karar,jikina banda tsuma babu abunda yake shikuma jin nayi wannan karar yayi saurin rufe mun bakina da hannunsa,ya ta dani zaune saurin matsawa ai daga jikinsa nasaka kaina cikin guiwata na saka kuka.......
Fuskarsa ya shafa har xuwa cikin gashin kansa,tsikar jikinsa babu abunda take sai tashi,har yanxu jiyake kamar anjona shi ga shocking.
Lumshe idonsa yayi inama kukan zaizo masa shima.Amman duk da haka saiya narke murya yace "kibar wannan kukan tunda dai ba abunda ya sameki,nine zanyi ba keba ai."
Idona share share na d'ago na dalla masa harara,ya d'age girarsa kurin yana sauke numfashi.
Jingina yayi da gadon ya rufe idonsa,tashi nai naje wajen madubi naga kona ji ciwo duk da bana jin hakan,rigar jikina dana ankare yasa na saki kara wadda ta sashi saurin nufo inda nake,ya rik'o kafad'ata cikin disshiyar murya yace "what happen,are u ok"Ture sa nai na bude wadrop na dauki jallabiya na ruga bayi na saka,ina ajiyar zuciya amman ni shashasha ce wlh.
Koda nafito ya goge wajen da towel din bakin kewayena,yana zaune yana danna wayarsa.
Bance masa komi ba na sake d'ebo wani ruwan,na dawo na ajiye zan cigaba da gugar.
YOU ARE READING
SO DA SHAQUWA
Randomlabarine akan tsantsar soyayya sadaukarwa jajircewa,da darasin rayuwa labarin yana koyar da zamantakewar duniya da yadda zaka zauna da mutane,karki bari ya wuceki tabbas so da shaquwa yana dauke da salo salo na musamman sai wanda ya bisa zaifahimci...